Skip to main content

Posts

YIN RIKO DA ALKUR’ANI DA SUNNAH KO ALKUR’ANI DA AHLUL BAITI?

YIN RIKO DA ALKUR’ANI DA SUNNAH KO ALKUR’ANI DA AHLUL BAITI? Godiya ta tabbata ga Allah Madaukaki Ubangijin halittu kuma mai gudanar da lammuran su. Tsira da amincin Sa su kara tabbata ga Annabin rahama Muhammadu dan Abdullahi da iyalan gidansa tsarkaka wadanda Allah Ya sanya bin su shine lamuni daga bata, da kuma sahabban sa managarta, da waanda suka I shiyar sa har zuwa ranar sakamako. S oyayya da tausayawar da Allah Madaukakin Sarki Ya ke yi wa bayi domin su sami kamalar da zata sadar da su zuwa ga ingantaccen rayuwa a nan gidan duniya da kuma wacce ta fi ta muhimmanci shine rayuwar din-din-din bayan na wannan duniya, ya sanya Shi aiko Annabawa da Manzonni domin su shiryar da mutane zuwa ga wannan tafarki. Wadannan Manzonni sun sami turjiya daga al'umunsu sakamakon taurin kai da kin karban gaskiya da ganganci bayan an bijirar musu da dukkan hujjoji. A karshe sai ya zamo mutane 'yan kadan ne suke yin imani da su. To saidai wani abin takaici shine bayan wadanna...