Skip to main content

Posts

Showing posts from May, 2017

SHAIKH AN-NAWAWI DA MAULUDIN MANZO (S)

SHAIKH AN-NAWAWI DA MAULUDIN MANZO (S) WAHABIYAWA: KARFIN HALI - BARAWO DA SALLAMA Shahararre kuma babban Malami masanin hadisai a duniyar Sunnah "Shaikh Abu Zakariyya Yahya bin Sharaf an-Nawawiy" wanda aka fi sanin sa da "Imam An-Nawawi. Wannan Malami shine wanda ya tattara hadisai guda arba'in a lilltafi guda wanda ake kiran sa "Arba'una Hadith" . Wannan littafi ya shahara ta yanda ake koyar da shi a makarantun addini a duniyar sunna. Anan Nigeria kuwa bayan karantar da shi da akeyi a makarantun addinin musulunci an sanya wannan littafi a manhajar karantar da dalibai darasin Addinin Musulunci tun daga makarantar karamar sakandare (JSS level) har zuwa babban sakandare (SS level). A cikin littafin ne a hadisi na biyar ya rawito hadisin da ya tuke da Ummul Muminina A'isha, Wanda take cewa Manzon Allah s.a.w.a yace; "Man Ahdatha fi Amrina Haza Malaisa Minhu Fahuwa Raddun" Ma'ana Duk wanda ya fari wani abu daga cikin wannan al'...