SHAIKH AN-NAWAWI DA MAULUDIN MANZO (S)
WAHABIYAWA: KARFIN HALI - BARAWO DA SALLAMA
Shahararre kuma babban Malami masanin hadisai a duniyar Sunnah "Shaikh Abu Zakariyya Yahya bin Sharaf an-Nawawiy" wanda aka fi sanin sa da "Imam An-Nawawi.
Wannan Malami shine wanda ya tattara hadisai guda arba'in a lilltafi guda wanda ake kiran sa "Arba'una Hadith" . Wannan littafi ya shahara ta yanda ake koyar da shi a makarantun addini a duniyar sunna.
Anan Nigeria kuwa bayan karantar da shi da akeyi a makarantun addinin musulunci an sanya wannan littafi a manhajar karantar da dalibai darasin Addinin Musulunci tun daga makarantar karamar sakandare (JSS level) har zuwa babban sakandare (SS level).
A cikin littafin ne a hadisi na biyar ya rawito hadisin da ya tuke da Ummul Muminina A'isha, Wanda take cewa Manzon Allah s.a.w.a yace;
"Man Ahdatha fi Amrina Haza Malaisa Minhu Fahuwa Raddun"
Ma'ana Duk wanda ya fari wani abu daga cikin wannan al'amari namu (Addinin mu na Musulunci) wanda baya cikin sa, to an mayar masa.
A wani kaulin kuma "Man Amila Amalan Laisa Alaihi Amruna Haza Fahuwa Raddun.
Ma'ana Duk wanda ya aikata wani aiki wanda bubu shi a wannan al'amari namu, to an mayar masa.
Shi Imam An-Nawawi ya ciro wadannan hadisai ne a cikin Buhari da Muslim.
Wannan babban Shehin yayi sharhi wa Litattafan Sahihan nan na Ahlus Sunna wato Sahihul Bukhariy da Sahihu Muslim. Ya wallafa litattafai da dama wanda suka hada da littafin hadisin nan "Riyadhus Salihin"
To wannan hadisi da na kawo a sama shine Wahabiyawan wannan zamani suke nuna jahilcin su a kan sa wajen cika baki suna nuna cewa shine babban Makamin su wanda yake tabbatar da Bidi'ancin Mauludin Manzon Allah s.a.w.a.
To Amma abin ban sha'awa shine sai ga wannan Malami Imam An-Nawawi yana bada fatawar halaccin yin mauludi, kai bama halacci ba da irin muhimmancin da yake tattare da yin wannan ibada ta Mauludin Manzo s.a.w.a.
Ga abinda yake cewa;
" ﻭﻣﻦ ﺃﺣﺴﻦ ﻣﺎ ﺍﺑﺘﺪﻉ ﻓﻲ ﺯﻣﺎﻧﻨﺎ ﻣﺎ ﻳُﻔﻌﻞ
ﻛﻞ ﻋﺎﻡ ﻓﻲ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻟﻤﻮﺍﻓﻖ ﻟﻤﻮﻟﺪﻩ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﺪﻗﺎﺕ، ﻭﺍﻟﻤﻌﺮﻭﻑ،
ﻭﺇﻇﻬﺎﺭ ﺍﻟﺰﻳﻨﺔ ﻭﺍﻟﺴﺮﻭﺭ، ﻓﺈﻥ ﺫﻟﻚ ﻣﺸﻌﺮٌ
ﺑﻤﺤﺒﺘﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﻪ
ﻓﻲ ﻗﻠﺐ ﻓﺎﻋﻞ ﺫﻟﻚ ﻭﺷﻜﺮﺍً ﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻋﻠﻰ
ﻣﺎ ﻣﻦّ ﺑﻪ ﻣﻦ ﺇﻳﺠﺎﺩ ﺭﺳﻮﻟﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﺃﺭﺳﻠﻪ
ﺭﺣﻤﺔ ﻟﻠﻌﺎﻟﻤﻴﻦ
"Daga cikin mafi kyawun abinda aka farar a wannan zamani namu shine abinda ake yi ko wani shekara a ranar da ta dace da ranar haihuwar sa s.a.w.a daga sadakiki da kyautatawa da bayyana ado da farin ciki. Lallai wannan abu ne wanda yake ingizar da soyayyar sa (Manzon Allah) s.a.w.a, da kuma girmama shi (Manzon Allah din) a cikin zuciyar mai yin hakan, da kuma godiya ga Allah Madaukaki game da baiwar da yayi na samar da Manzon Sa wanda ya aiko shi Rahma ga Talikai".
Za'a sami wannan zance a littafi;
(Baa'isu Alaa Inkaaril Bid'i walhawaadisi: wallafar Shaikh Abu Shamah. Shafi na 13)
To yaya yanzu watsu tsirarun jahilai za su zo suna wasu babatu da haushi wai Mauludi Bidi'a ne?
Sannan ga abubuwa gagara kirge da suka kirkira suna aikatawa a matsayin addini, wasu abubuwan ko shekara dari basu yi ba. Wasu ko shekara hamsin, kai wasu abubuwan su na yanzu su suka kirkira kuma suna kan kirkirowa.
Ya kamata wahabiyawa susan cewa yanzu zamanin karatu ne, jahilci da 419 bazai ciyu ba.
Da can baya Malaman darika sun yi shiru sun kyale ku kuna ta yi wa jahilai Kalkalar karatu a makogoro.
To mutum ya sani ko amai zai yi don tsabar kalkala to haka zai kade rigar sa ba tare da samun nasarar yaudaran wani ba. 'Ya'yan ku ma yanzu suna yin karatu suna fahimtar wannan shiriritar suna watsi da shi.
Ba wanda yace bukin Mauludi wajibi ne a musulunci dole ka zo ka yi.
Kowa ya rike fahimtar sa ba tare da sukan juna da munanan suna ba.

Comments
Post a Comment