Skip to main content

Posts

Showing posts from June, 2017

HANA RUBUTA HADISAI DA KONA WADANDA AKA RUBUTA DAGA KHALIFA ABUBAKAR DA UMAR

MENENE GASKIYAN LAMARIN? TAMBAYOYI ZUWA GA AHLUS SUNNA. Murtala Isah Dass. (SHIFTA DAGA FACEBOOK) Ta tabbata a tarihi kamar yanda ya taho a cikin ingantattun hadisan Ahlus sunnah cewa bayan nada Khalifa Abubakar a Saqifa, ya tattaro sahabbai sai ya fada musu cewa "Kun kasance kuma hakaito hadisi daga Manzon Allah (s) wadanda kuke sabani a cikinsa, kuma al'umar da zasu taho a bayanku zasu kasance mafiya tsananin sabani, (saboda haka) kada ku sake hakaito wani abu na hadisan Manzo (s). Duk wanda ya tambayeku (wani abu game da addini), kuce; a tsakaninmu akwai littafin Allah. Ku halallat halalinsa ku haramta haraminsa. (Tazkiratul Huffaz, na Imam Zahabiy, juzu'i na 1, shafi na 3) Ga mataninsa na larabci; : ﺇﻥ ﺍﻟﺼﺪﻳﻖ ﺟﻤﻊ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﻌﺪ ﻭﻓﺎﺓ ﻧﺒي ‏( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ‏) ﻓﻘﺎﻝ : ﺇﻧﻜﻢ ﺗﺤﺪﺛﻮﻥ ﻋﻦ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ‏( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ‏) ﺃﺣﺎﺩﻳﺚ ﺗﺨﺘﻠﻔﻮﻥ ﻓﻴﻬﺎ ، ﻭﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﻌﺪﻛﻢ ﺃﺷﺪ ﺍﺧﺘﻼﻓﺎ ، ﻓﻼ ﺗﺤﺪﺛﻮﺍ ﻋﻦ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ‏( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ‏) ﺷﻴﺌﺎ ، ﻓﻤﻦ ﺳﺄﻟﻜﻢ ﻓﻘﻮﻟﻮﺍ : ﺑﻴﻨﻨﺎ ...