MENENE GASKIYAN
LAMARIN?
TAMBAYOYI ZUWA GA AHLUS
SUNNA.
Murtala Isah Dass.
(SHIFTA DAGA FACEBOOK)
Ta tabbata a tarihi
kamar yanda ya taho a cikin ingantattun hadisan Ahlus sunnah cewa bayan nada
Khalifa Abubakar a Saqifa, ya tattaro sahabbai sai ya fada musu cewa "Kun
kasance kuma hakaito hadisi daga Manzon Allah (s) wadanda kuke sabani a cikinsa,
kuma al'umar da zasu taho a bayanku zasu kasance mafiya tsananin sabani,
(saboda haka) kada ku sake hakaito wani abu na hadisan Manzo (s). Duk wanda ya
tambayeku (wani abu game da addini), kuce; a tsakaninmu akwai littafin Allah.
Ku halallat halalinsa ku haramta haraminsa. (Tazkiratul Huffaz, na Imam
Zahabiy, juzu'i na 1, shafi na 3)
Ga mataninsa na
larabci;
: ﺇﻥ ﺍﻟﺼﺪﻳﻖ ﺟﻤﻊ
ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﻌﺪ ﻭﻓﺎﺓ
ﻧﺒي ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺁﻟﻪ ) ﻓﻘﺎﻝ
: ﺇﻧﻜﻢ ﺗﺤﺪﺛﻮﻥ ﻋﻦ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ
( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ) ﺃﺣﺎﺩﻳﺚ
ﺗﺨﺘﻠﻔﻮﻥ
ﻓﻴﻬﺎ ، ﻭﺍﻟﻨﺎﺱ
ﺑﻌﺪﻛﻢ ﺃﺷﺪ ﺍﺧﺘﻼﻓﺎ ، ﻓﻼ
ﺗﺤﺪﺛﻮﺍ ﻋﻦ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺁﻟﻪ ) ﺷﻴﺌﺎ
، ﻓﻤﻦ ﺳﺄﻟﻜﻢ ﻓﻘﻮﻟﻮﺍ : ﺑﻴﻨﻨﺎ
ﻭﺑﻴﻨﻜﻢ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ
، ﻓﺎﺳﺘﺤﻠﻮﺍ ﺣﻼﻟﻪ
ﻭﺣﺮﻣﻮﺍ ﺣﺮﺍﻣﻪ
ﺗﺬﻛﺮﺓ ﺍﻟﺤﻔﺎﻅ
ﻟﻠﺬﻫﺒﻲ 1 : 3
Ba wannan matakine
kawai Khalifa Abubakar ya dauka ba a'a ya ma sanya sahabban suka tattaro
hadisan da suka rubuta, sai ya banka musu wuta ya kona. Kuma abu mafi al'ajabi
shine mutum zai yi tunanin ko abin ya shafi wasu ne da ake ganin raunin su ta
yanda zasu iya sanya son ran su ko wani abu makamancin ha. Amma sai gashi hatta
hadisan da 'yarsa Ummul muminina A'isha ta rubuta ya karba ya kona su. Kamar
yanda yazo a cikin Tazkiratul huffaz din a kuma wancan juzu'i da shafi na sama,
kamar haka;
ﻗﺎﻟﺖ ﻋﺎﺋﺸﺔ: ﺟﻤﻊ
ﺃﺑﻲ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﻋﻦ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ (
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ) ﻭﻛﺎﻧﺖ
ﺧﻤﺴﻤﺎﺋﺔ ﺣﺪﻳﺚ
ﻓﺒﺎﺕ ﻟﻴﻠﺔ ﻳﺘﻘﻠﺐ ﻛﺜﻴﺮﺍ .
ﻗﺎﻟﺖ : ﻓﻐﻤﻨﻲ
ﻓﻘﻠﺖ : ﺃﺗﺘﻘﻠﺐ ﻟﺸﻜﻮﻯ ﺃﻭ
ﻟﺸﺊ ﺑﻠﻐﻚ ؟ ﻓﻠﻤﺎ
ﺃﺻﺒﺢ ﻗﺎﻝ : ﺃﻱ ﺑﻨﻴﺔ !
ﻫﻠﻤﻲ ﺑﺎﻷﺣﺎﺩﻳﺚ
ﺍﻟﺘﻲ ﻋﻨﺪﻙ ، ﻓﺠﺌﺘﻪ ﺑﻬﺎ ،
ﻓﺪﻋﺎ ﺑﻨﺎﺭ ﻓﺤﺮﻗﻬﺎ .....
Da alama dai da wuya a iya dogaro da gundarin
Alqur'ani wajen gudanar da rayuwa a musulunci ba tare da jingina zuwa ga
shiryarwan Manzo (s) ba kamar yanda Khalifa ya bukata. Saboda haka sai tarihi
da ya nuna cewa al'umar musulmi basu iya dabbaka wannan doka ba sunci gaba da
naqalto hadisan Manzo har ma da ci gaba da rubuta shi.
Saboda haka bayan
shudewan Abubakar yayin da khalifa Umar bin Khattab ya hau kan karagar
Khalifanci shima sai ya dauki wannan mataki, ya sake sanya sahabbai suka
kakkawo hadisan da suka rubuta ya kona su. Kamar yanda yazo a cikin littafin
Tabaqaat, Na Ibn Sa'ad, juzu'i na 5, shafi na 140.
Ga matanin sa na
larabci;
: ﺍﻥ ﺍﻻﺣﺎﺩﻳﺚ ﻛﺜﺮﺕ
ﻋﻠﻰ ﻋﻬﺪ ﻋﻤﺮ ﺑﻦ
ﺍﻟﺨﻄﺎﺏ ﻓﺎﻧﺸﺪ
ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺍﻥ ﻳﺄﺗﻮﻩ
ﺑﻬﺎ ﻓﻠﻤﺎ ﺍﺗﻮﻩ ﺑﻬﺎ ﺃﻣﺮ
ﺑﺘﺤﺮﻳﻘﻬﺎ .
( ﺍﻟﻄﺒﻘﺎﺕ 5 : 140) .
Tambayoyi anan sune;
#Ashe zai iya yuwuwa
ayi watsi da hadisai a rike Alqur'ani kadai sakamakon sabanin da za'a iya samu?
To idan haka ne meye ma'anar riko da dubban dubunnan hadisan da yanzu ake
amfani da su wadanda wasu ne suka naqalto su a bayan sahabbai?
#Yaya akayi sahabban
ma da kansu an kasa nitsuwa da ruwayoyin su kai tsaye amma kuma aka yi riko da
naqaltowan wadanda suka taho a bayan su?
#Shin yaya akayi
sahabban da ake gani su suka yi zamani da Manzon Allah (s) suka ji daga gare
shi amma aKhalifofi suka kasa nitsuwa da su? Shin ba na baya bane sukafi
cancantar suyi watsi da hadisai sakamakon qarin nisan zamani wanda zai haifar
da qarin sabani kamar yanda Khalifa Abubakar ya bayyana ba?
#Shin khalifofin nan
suna ganin akwai wadanda suka rawaito qarya kenan shi yasa ake samun sabani, ko
kuma wasun su basa iya fahimtar hadisan ne sai su rawaito wani abu daban
sabanin yanda Manzon ya fada? Idan wasu sahabbai zasu yi qarya wa Manzo to yaya
batun adalar dukkan sahabbai kenan?
#Idan Manyan
Khalifofi biyu Abubakar da Umar zasu yi umurnin yin watsi da hadisai to menene
hujjar yanzu azo ana wajabta yin riko da hadisai har ana takama da sunan
"Ahlus sunna"?
#Shin shin Khalifofin
da suka hana suna kan bata kenan amma na
yanzu sune akan shiriya? Koko Sahabbai ba amintattu bane, ko basa da ilimin
gano sahihan hadisai sai wadanda suka taho a abayan su sune amintattu kuma masu
iya fahintar haqiqanin sunna?
#Shin ba zurfin
sabanin da wadannan khalifofi suka gani a cikin hadisan da sahabbai suke
naqaltowa daga Manzo (s) ne ya sanya suka ma kasa zama su tantance sahihai daga
gurbatattu ba, amma sai daga baya wasu suke ganin sun fisu kenan har suka yi
hakan?
Shin wai yaya abin
yake ne, ko kuma akwai wani lauje cikin nadi ne?
Muna jiran amsoshin
wadannan tamayoyi (Musamman Shehunan mu na Ahlus Sunna da social media, kafin
mu amsa su a tamu nazariyyar a rubutu na gaba da yardar Allah.
HANA RAWAITO DA RUBUTA HADISI A LOKACIN KHALIFOFI BIYU NA
FARKO(ABUBAKAR DA UMAR) SHAHARARREN AL'AMARI NE DA BABU KOKWANTO A CIKINSA.
Na kuduri yin wannan rubutu ne domin kara fayyacewa game da rubutun da nayi a
kwanakin nan wanda na masa Maudhu'i "Menene gaskiyan lamari? Tambayoyi
zuwa ga Ahlus sunna"
Sakamakon haka ne wasu daga cikin wahabiyawa/ salafawa suka bayyana da kurarin zasu amsa wadannan tambayoyi da nayi a wannan rubutu, amma maimakon hakan sai suka 6uge da hauragiyan musanta faruwan hakan da hujjar da'awar cewa wai ruwayoyin basu inganta ba.

Lamarin hana ruwayar hadisan
Annabi shaharan sa ya wuce wannan cashi-fadin nasu. Shi ya sa ma kafin in taho
fagen amsa wadancan tambayoyi naga cewa ya kamata in qara fayyacewa ta yanda
al'uma zasu kara ganin abin a sarari.
Hana rawaito hadisai yana daya daga cikin manyan matakan da Khalifa Umar ya dauka kuma ya zafafa a kan sa sosai a lokacin khalifancin sa fiye da Khalifa Abubakar.
Khalifa ya dauki kakkausan mataki akan sahabban da suka nace da yada hadisan Manzon Allah (s) a cikin al'umar musulmi a lokacin khalifancin sa, ta yanda takai ga yayi daurin talala ga wasu shahararrun sahabbai, kamar Abdullahi bin Huzaifa, Abu Darda'i, Abu Zarril Ghifariy, Ibn Mas'ud da Uqba bin Amir. Wadannan sahabbai suna zaune ne a garuruwa daban-daban suna ilmantar da al'uma addini ta wajen fassara musu ayoyin Qur'ani da kuma Hadisan da suka ji daga bakin Manzon tsira (s). Amma sai Khalifa Umar ya sa aka kirayosu, ya tuhume su akan me yasa suke karanta wa mutane hadisan Annabi? Sannan daga qarshe sai sanya musu takunkumin fita daga Madina zuwa wani waje ya musu daurin talala, domin kada in ya barsu suka koma suyi watsi da wannan umurni nasa suci gaba da yada ruwayoyi (domin shi kansa yasan hakan ne zai faru). Kuma bai sake su daga wannan daurin talala da yayi musu ba har rasuwar sa. Saidai ance an rangwata musu zuwa aikin hajji a Makka, amma a hakan ma akwai 'yansandan ciki masu lura da su.
Wannan ya zo a cikin Kanzul ummal, juzu'i na 5 shafi na 239, hadisi mai lamba na 4865.
Ga mataninsa na larabci;
وعن عبد الرحمن بن عوف قال: ما مات عمر بن الخطاب حتى بعث إلى
أصحاب رسول الله فجمعهم من الآفاق عبد الله بن حذيفة وأبا الدرداء وأبا ذر وعقبة
بن عامر، فقال: ما هذه الأحاديث التي أفشيتم عن رسول الله في الآفاق؟
قالوا: تنهانا؟
قال: لا، أقيموا عندي، لا والله لا تفارقوني ما عشت، فنحن أعلم نأخذ
منكم ونرد عليكم فما فارقوه حتى مات
Imam Hakim ma ya fidda wannan hadisi a cikin Mustadrak nashi a juzu'i na farko, shafi na 110. Haka ma yazo a cikin Tazkiratul Huffaz, juzu'i na 1 shafi na 7.

عن سعد بن إبراهيم عن أبيه ان عمر بن الخطاب قال لابن
مسعود ولأبي الدرداء ولأبي ذر ما هذا الحديث عن رسول الله صلى الله عليه وآله واحسبه حبسهم بالمدينة حتى أصيب
هذا حديث صحيح على شرط الشيخين وانكار عمر أمير المؤمنين على الصحابة كثرة الرواية عن رسول الله صلى الله عليه وآله فيه سنة ولم يخرج

Dukda wannan daurin talala da
akayi wa wadannan sahabbai tarihi ya bayyana cewa Abu Zarril Ghifariy bai daina
rawaito hadsai ba. Saboda hakane ma a wani shekara da ya tafi Makka a majalisin
sa al'uma suka taru suna masa fatawoyi yana basu amsa ta wajen karanto musu
hadisan Manzo (s) sai wani dansandan ciki (S.S.S.) na khalifa ya taho ya tsaya
a kansa yake ce masa; shin ashe ba'a hana ka bada fatawa ba? Sai Abu Zarri ya
daga kansa ya kalle shi yace masa; shin kai mai tsaro ne akai na? To bari in
shaida maka kaji da kyau, koda zaku sanya takobi akan wuya na ne don ku hana ni
fadar wani kalma da na jishi daga Manzon Allah to sai na fada koda kuwa in nayi
hakan zaku sare shi ne.
Kamar yanda wannan bayani yazo a cikin Sunanu Daramiy, juzu'i na 1 shafi na 132. Tabaqaat na Ibn Sa'ad, juzu'i na 2 shafi na 354.
Ga matanin sa na larabci;
Kamar yanda wannan bayani yazo a cikin Sunanu Daramiy, juzu'i na 1 shafi na 132. Tabaqaat na Ibn Sa'ad, juzu'i na 2 shafi na 354.
Ga matanin sa na larabci;
ما رواه الدارمي وغيره: ان أبا ذر كان
جالسا عند الجمرة الوسطى وقد اجتمع الناس يستفتونه، فأتاه رجل فوقف عليه، ثم قال: ألم تنه عن الفتيا؟ فرفع رأسه إليه، فقال: أرقيب أنت على؟! لو وضعتم الصمصامة على هذه وأشار إلى قفاه ثم ظننت اني أنفذ كلمة سمعت من رسول الله (ص) قبل ان تجيزوا
علي لأنفذته

Shiririta ne kawai da nuna
tsagwaran jahilci mutum yace zai musanta wannan waqi'i da kundin tarihi na
wannan addini ya taskace. Wannan irin musa haqiqa salo ne na Ibn Taimiyya, kuma
wannan shi ya bayyana tsirarar tabewar sa da kuma jahilcin sa wanda yau ya zama
abin zance a tsakanin ma'abuta ilimin musulunci, sunnansu da shi'ansu.
Khalifa Umar bin Khattab ya
kasance koda rundunar yaki zai tura sai ya musu kashedin cewa kada su rika
karanta wa mutane hadisai. Kamar yanda a wani lokaci ma hankalin sa ya kasa kwanciya
bayan ya tura runduna sai ya biyo su domin ya tabbatar basu watsa hadisai ba
kamar lokacin da ya tura runduna zuwa Iraqi, yake shaida musu cewa ya biyo su
ne domin ya musu gargadin cewa mutanen Iraqi masu himma ne wajen karatun
Alqur'ani, saboda haka kada su gurbata su ta wajen karanto musu ruwayoyi.
Saboda haka ne ma yasa a lokacin da Quraiza bin Ka'ab ya tafi can, jama'a suka
taru suna masu marmarin su ji hadisan Manzo (s) daga gare shi, sai yace musu
Umar ya hana mu (rawaito hadisai).
Kamar yanda yazo a cikin Tazkiratul Huffaz, juzu'i na 1 Shafi na 7;
وقد روى شعبة وغيره عن بيان الشعبي عن قرظة بن
كعب قال لما سيرنا عمر إلى العراق مشى معنا عمر وقال أتدرون لم
شيعتكم؟ قالوا نعم تكرمة لنا قال ومع ذلك انكم تأتون أهل قرية لهم
دوي بالقرآن كدوي النحل فلا تصدوهم بالأحاديث فتشغلوهم جردوا
القرآن وأقلوا الرواية عن رسول الله وانا شريككم. فلما قدم قرظة بن
كعب قالوا حدثنا فقال نهانا عمر رضي الله عنه.

Sahabin da Ahlus sunna suka fi
cika litattafan su da ruwayoyin sa shine Abu Huraira, to shima ya bada bahasi
ya shaida wa al'uma wannan shaharren lamari na sanya dokan hakaito hadisai da
tsanantawa a daga Khalifa Umar.
Bayan rasuwar Khalifa Umar a lokacin Mulkin Sarki Mu'awiya 'dan Abu Sufyan, Abi Salama yayin da yaji Abu Huraira yana zazzago hadisai babu kama hannun yaro. Sai yaje ya same shi yace masa wai shin haka ka kasance kana zazzago wadannan hadisan a lokacin Umar kamar yanda kake yi yanzu? Sai Abu Huraira yace masa; da na kasance ina rawaito hadisai a zamanin Umar kamar yanda nake rawaito muku yanzu da nasha jibga.
Wannan yazo a cikin Tazkiratul Huffaz, juzu'i na 1 shafi na 7.
Ga mataninsa da larabci;
الدراوردي عن محمد بن عمرو عن أبي سلمة عن أبي هريرة وقلت
له أكنت تحدث في زمان عمر هكذا فقال لو كنت أحدث في زمان
عمر مثل ما أحدثكم لضربني بمخفقته.

Saboda haka kokarin wani a yanzu
da zai taho ya kawo wata mugalada don rufe wannan haqiqa yana bata wa kansa
lokaci ne kawai.
Da'awar cewa wai su malaman da suka rubuta wadannan hadisai suna so su nuna munanan aqidun khawarijawa ne na kin hadisai, shirme ne kawai. Domin shi Imamu Zahabiy bayan ya kawo wancan hadisin da na kawo a wancan rubutuna na farko inda aka rawaito cewa Khalifa Abubakar ya tara sahabbai ya gargade su da kada su rawaito hadisai, cewa abinda Khalifa yake nufi shine a tabbatar da cewa ana bukatan hadisin ya tabbata daga siqqa ne cikin sahabbai kafin a a karbe shi da tantancewa, har ya kawo misalin cewa ai shi kansa Khalifa Abubakar din yakan nemi hadisai yayi aiki da su wadanda amintattu suka rawaito.
Ga matanin abinda ya fada da larabci;
فهذا... يدلك ان مراد الصديق التثبت في الاخبار والتحري
لا سد باب الرواي
ألا تراه لما نزل به أمر الجدة ولم يجده في الكتاب
كيف سأل عنه في السنة فلما أخبره الثقة ما اكتفى حتى استظهر بثقة آخر
To a nan ne ma muke jaddada tambayar mu akan cewa ashe dama sahabbai zasu iya rawaito qarya? Ashe a cikin sahabbai akwai wadanda ba amintattu ba, kamar yanda Zahabiy ya kawo a cikin dalilan khalifofi na hana rawaito hadisai? To yaya batun babatun adalan dukkan sahabbai?
Ashe abinda Khalifa Umar yayi na hana nmanyan sahabbai irin su Abu Zarri rashin yarda da gaskiyar su ne, ta yanda zasu iya rawaito qarya da sunan Manzo (s)? Ashe su ba amintattu bane?
Ashe irin su Abu Huraira duk ba yardaddu bane a wajen Khalifofi amma sai gashi daga baya sun zama yardaddu a wajen na baya, aka cika duniya da ruwayoyin su?
Bayan haka Imam Zahabiy ya kawo wani bayani domin qara nuna manufan Khalifa Abubakar cewa ba irin ra'ayin Khawarijawa yake nufi na cewa "littafin Allah ya ishemu" ba;
ولم يقل حسبنا كتاب الله كما تقوله الخوارج.
Ashe fadar cewa "Hasbuna kitabullahi" kwarijanci ne? ashe fadar hakan bata ne? To zamu ga waya assasa wannan mazhaba na "Hasbuna kitabullah" a yayin da zamu bada amsan wadancan tambayoyi inshaAllahu.

A biyo ni nan gaba domin jin
amsar wadannan tabayoyi.
Zan jinkirta amsa su zuwa munasaba ta Idil Ghadeer mai albarka wanda zai zo bayan babban salla, domin neman tabarruki da wannan Idi mai Albarka idin Wilaya. Sannan shi kansa amsan wadannan tamboyoyi yana da alaqa ne kai tsaye da wannan Munasaba Idin Wilaya.
Wasallallahu Ala Muhammad wa Alihit Tahirin.
Zan jinkirta amsa su zuwa munasaba ta Idil Ghadeer mai albarka wanda zai zo bayan babban salla, domin neman tabarruki da wannan Idi mai Albarka idin Wilaya. Sannan shi kansa amsan wadannan tamboyoyi yana da alaqa ne kai tsaye da wannan Munasaba Idin Wilaya.
Comments
Post a Comment