YIN
RIKO DA ALKUR’ANI DA SUNNAH
KO
ALKUR’ANI
DA AHLUL BAITI?
Godiya ta tabbata
ga Allah Madaukaki Ubangijin halittu kuma mai gudanar da lammuran su. Tsira da
amincin Sa su kara tabbata ga Annabin rahama Muhammadu dan Abdullahi da iyalan
gidansa tsarkaka wadanda Allah Ya sanya bin su shine lamuni daga bata, da kuma
sahabban sa managarta, da waanda suka I shiyar sa har zuwa ranar sakamako.
Soyayya da
tausayawar da Allah Madaukakin Sarki Ya ke yi wa bayi domin su sami kamalar da
zata sadar da su zuwa ga ingantaccen rayuwa a nan gidan duniya da kuma wacce ta
fi ta muhimmanci shine rayuwar din-din-din bayan na wannan duniya, ya sanya Shi
aiko Annabawa da Manzonni domin su shiryar da mutane zuwa ga wannan tafarki.
Wadannan Manzonni sun sami turjiya daga al'umunsu sakamakon taurin kai da kin
karban gaskiya da ganganci bayan an bijirar musu da dukkan hujjoji. A karshe
sai ya zamo mutane 'yan kadan ne suke yin imani da su.
To saidai wani abin takaici shine bayan wadannan Manzonni su shude sai kuma a sami wasu daga cikin mabiya wadannan manzonni sun dauki matakin jirkita karantarwar tasu don karantarwar ba ta dace da son ransu ba. Sannan hatta litattafan shiriya da aka saukar wa wadannan Annabawa sai sun jirkita su ta wajen kari da ragi da canza wasu kalmomi da wasu na dabam na abinda suka ga dama, kamar yanda ya zo a cikin Kur'ani;
مِّنَ الَّذِينَ هَادُوا يُحَرِّفُونَ الْكَلِمَ عَن مَّوَاضِعِهِ وَيَقُولُونَ سَمِعْنَا وَعَصَيْنَا
"Daga waɗanda suka yahudance (yahudawa), akwai wasu sunã karkatar da magana daga wurãrenta suna cẽwa: "Mun ji kuma mun saba ....."
(Nisa’i, aya ta 46)
Da haka kuwa sai a wayi gari gaba daya an kauce akan karantarwar wadannan Annabawa, ana aikata wani abu dabam sabanin abinda suka karantar
amma da sunan
wannan addini.
Shima Annabin karshe Muhammadu dan Abdullahi (s) wanda ba za a sake aiko wani Annabi ba har zuwa ranar tashin kiyama. Saboda haka ya zamo sakon da ya fi bukatuwa a tsare shi daga jirkicewa. Kuma lallai Allah Ta'ala Ya yi tanadi na musamman domin kariya ga wannan sako na karshe.
Saidai yanayin al'uma tun Manzon (s) yana nan a cikinsu ya nuna cewa lallai wasu daga cikin al'umarsa za su bi sahun sauran al'umu wajen jirkita wannan sako da dasa son ransu a ciki. kamar yanda ya zo a ruwaya daga Manzon Allah;
: ﻋَﻦْ ﺃَﺑِﻲ
ﺳَﻌِﻴﺪٍ ﺍﻟْﺨُﺪْﺭِﻱِّ ﻋَﻦْ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲِّ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ
ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻗَﺎﻝَ
ﻟَﺘَﺘْﺒَﻌُﻦَّ ﺳَﻨَﻦَ ﻣَﻦْ ﻛَﺎﻥَ ﻗَﺒْﻠَﻜُﻢْ ﺷِﺒْﺮًﺍ ﺷِﺒْﺮًﺍ
ﻭَﺫِﺭَﺍﻋًﺎ ﺑِﺬِﺭَﺍﻉٍ ﺣَﺘَّﻰ ﻟَﻮْ ﺩَﺧَﻠُﻮﺍ ﺟُﺤْﺮَ ﺿَﺐٍّ
ﺗَﺒِﻌْﺘُﻤُﻮﻫُﻢْ ﻗُﻠْﻨَﺎ ﻳَﺎ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟْﻴَﻬُﻮﺩُ
ﻭَﺍﻟﻨَّﺼَﺎﺭَﻯ ﻗَﺎﻝَ ﻓَﻤَﻦْ
Daga Abi Sa’idil
Khudri, daga Annabi (s) ya ce; sai kun bibiyi hanyoyin wadanda suka gabace ku
taki bayan taki kuma taku da taku, har ko da sun shiga ramin damo ne zaku bi
su. (sai mai rawaito hadisin yace) sai muka ce ya Manzon Allah (kana nufin za
mu bi gurbin) yahudu da nasara? Sai ya ce; to da su waye (nake nufi)?
(Sahihul Bukhari
hadisi na 6928)
Abinda yake
tabbatar da hakan kuwa shine yanda wasu daga mabiyansa suke kirkiran karya su
jingina ta zuwa gare shi da gangan, har sai da abin ya yi yawa watarana ya fito
ya nuna bacin ransa game da irin wannan hali na wasu daga cikin sahabbansa;
قد كثرت على الكذابة، ألا من كذب علي متعمدا فليتبوأ مقعده من النار
“Lallai masu mini karya sun yawaita, to duk
wanda ya ganganta yi mini karya to ya tanadi mazaunin sa a wuta (ranar kiyama)”
Domin kiyaye wannan addini daga gurbata sai Allah Madaukaki ya lamunce yin kariya ga Alkur'ani ta yanda ba zai yiyu wani ya canza wani abu daga cikin mataninsa ya yi tasiri ba kamar yanda yake cewa;
إِنَّا نَحْنُ
نَزَّلْنَا
الذِّكْرَ
وَإِنَّا
لَهُ
لَحَافِظُونَ
Lallai Mũ ne, Muka
saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lallai Mu, Mãsu kiyayẽwa ne gare shi.
(Sura Al-Hijr, aya ta 9)
(Sura Al-Hijr, aya ta 9)
Sannan sai Allah Ta'ala Ya sanya kuma Ya umurci Manzo (s) da ya bayyana wa al'uma hanyar tsira daga gurbacewan addini har zuwa ranar tashin kiyama.
Sakamakon sanin cewa akwai wadanda za su yi sa'ayi wajen ganin sun gurbata wannan addini da jirkita ma'anonin sakon da ke rubuce tamkar yanda Yahudu da Nasara suka aikata, kuma tun Manzon yana raye wasu sun fara wannan aiki.
Dukda cewa Allah
Ta'ala Ya yi alkawarin kare wannan littafi na Alkur'ani daga jirkitan kalmomi (matani),
to duk da haka bai tsira daga jirkitar tafsiri, tawili ko fassara ba. Sannan a
gefe guda ga karantarwar Manzo (s) wanda yake bayani ne game da
hukunce-hukuncen da yake dauke a cikin Alkur'anin shima yana fuskantar
jirkicewa daga miyagu.
Sakamakon haka tun daren farko sai Allah Ta'ala Ya fitar da hanyar da al'uma zasu tsira daga wannan rami na halaka. Saboda haka Ya yi tanadi na musamman ga al'uma kuma Ya umurci Manzo (s) da ya bayyana musu. Saboda haka sai Manzon Rahama Muhammad (s) ya yi ta bayyana wanan kariya a matsayin wasici ga al'umarsa, a inda yake cewa;
Sakamakon haka tun daren farko sai Allah Ta'ala Ya fitar da hanyar da al'uma zasu tsira daga wannan rami na halaka. Saboda haka Ya yi tanadi na musamman ga al'uma kuma Ya umurci Manzo (s) da ya bayyana musu. Saboda haka sai Manzon Rahama Muhammad (s) ya yi ta bayyana wanan kariya a matsayin wasici ga al'umarsa, a inda yake cewa;
إني تارك فيكم الثقلين ما إن تمسكتم به لن تضلوا بعدي كتاب الله وعترتي اهل بيتي
“Lallai ni mai bari
ne a cikin ku nauyayan abubuwa guda biyu, matukar kuka yi riko da su a baya na
ba za ku taba bacewa ba, sune littafin Allah (Alkur'ani) da tsatso na (zuriya ta)
iyalan gida na (Ahlul baiti)”
Amma sakamakon wasu al'uma basa kaunar wadannan tsatso na Manzon Allah (s) kuma suka sami damar salladuwa a kan al'umar musulmi da sunan sune shuwagabanni (Banu Umayya) saboda haka suka dinga la’anta da yakar wannan tsatso (zuriya) na Manzo (s) suka karkashe su, sannan suka sauya wannan wasici na Allah da Manzon Sa, suka ce wai Manzo ya bar wasicin riko da
كتاب الله وسنتي
Alkur'ani ne da
sunnarsa ce.
Saboda haka suka
sanya aka kirkiro musu hadisai na karya a matsayin sune sunnar Annabin suka
dora al'uma akan haka. Suka caccanza abinda suka ga dama a guraben sahihiyar sunna
ta Manzo (s)
Saidai abinda ya shafi wannan jirkitawan da suka yi game da wasicin
Manzo (s) ya ci karo da matsaloli ta yanda aka kasa samun sahihin sanadin da ya
taho da shi a irin ma’aunin malaman Ahlus sunnah. Hatta manyan malaman salafawa
Ibn Taimiyya, Imam Zahabi da Sheikh Nasiruddin Albani sun raunata hadisan ta
dukkan fuskokin da suka taho. A lokaci guda kuma suka inganta ruwayoyin da ta
zo da umurni da yin riko da Alkur’ani da Ahalul baiti, musamman shi Albani.
RUWAYOYIN YIN UMURNI GAME DA RIKO DA ALKUR'ANI DA AHLUL BAITI DAGA RUWAYOYIN AHLUS SUNNAH
Kasancewar Allah Ta'ala ba zai bar al'uma cikin duhun bata ba sai Ya nuna ikonSa ta yanda gaskiya ta bullo daga mabubbugan da makiyanta suka yarda da ita. Saboda haka sai ga tarin irin wadannan ruwayoyi na wasicin yin riko da Kur'ani da Ahlul baiti birjik a cikin ruwayoyin Ahlus Sunna tare da lafuzza mabanbanta.
Ga kadan daga
cikinsu;
1-
:
عن
زيد
بن
أرقم
إني تارك فيكم ما إن تمسكتم به لن تضلوا بعدي أحدهما أعظم من الآخر كتاب الله حبل ممدود من السماء إلى الأرض وعترتي أهل بيتي ولن يتفرقا حتى يردا علي الحوض
إني تارك فيكم ما إن تمسكتم به لن تضلوا بعدي أحدهما أعظم من الآخر كتاب الله حبل ممدود من السماء إلى الأرض وعترتي أهل بيتي ولن يتفرقا حتى يردا علي الحوض
Daga Zaidu dan
Arkam: Manzon Allah (s) ya ce; Lallai ni mai bari ne a cikin ku abinda idan
kuka yi riko da shi a baya na ba za ku taba bacewa ba. Dayan su ya fi
dan'uwansa girma. Sune littafin Allah (Alkur'ani), igiya mikakkiya daga sama
zuwa kasa, da tsatso na (zuriya ta) iyalan gida na (Ahlul baiti), kuma ba za su
taba rabuwa da juna ba (Alkur'ani da Ahlul baiti) har sai sun riske ni a tafki
(alkausara a ranar kiyama) .....
(Sunanu Tirmizi,
hadisi 3788. Sannan Sheikh Nasiruddin Albani ya inganta hadisin a cikin
"Silsilatu ahadisis sahiha)
2-
عن جابر بن عبدالله قال
رأيت رسول الله صلى الله عليه وسلم في حجته يوم عرفة وهو على ناقته القصواء يخطب فسمعته يقول يا أيها الناس إني تركت فيكم ما إن أخذتم به لن تضلوا كتاب الله وعترتي أهل بيتي
Daga Jabir dan Abdullah ya ce; Na ga Manzon Allah (s) a hajjinsa ranar Arafah ya haye a kan taguwarsa mai daraja yana huduba. Sai na ji shi yana cewa; ya ku mutane lallai ni na bar muku abinda idan kuka rike a baya na ba zaku taba bacewa ba, (sune) littafin Allah da tsatso na iyalan gida na.
(Sunanu Tirmizi,
hadisi na 3786. Sheikh Nasiruddin Albani ya inganta shi)
3-
عن زيد بن ثابت
إني تارك فيكم خليفتين : كتاب الله حبل ممدود ما بين السماء والأرض ، وعترتي أهل بيتي ، و إنهما لن يتفرقا حتى يردا علي الحوض
Daga Zaid bin
Thabit : Manzon Allah (s) ya ce; Lallai ni na bar muku masu mayewa (khalifofi)
guda biyu, su ne littafin Allah (Alkur'ani) wacce itace igiya mikakkiya
tsakanin sama da kasa, da tsatso na iyalan gida na (Ahlul baiti). Kuma lallai
su biyun nan (Alkur'ani da Ahlulbbaiti) ba za su taba rabuwa da juna ba har sai
sun tarar da ni a tabki (Alkausara ranar kiyama)
(Sahihul Jami'i na
Sheikh Nasiruddin Albani, hadisi 2457. Sannan ya ce hadisin ingantacce ne)
4-
عن أبي سعيد الخدري
يا أيها الناس ! إني
تركت
فيكم
ما
إن
أخذتم
به
لن
تضلوا
كتاب
الله
،
وعترتي
،
أهل
بيتي
Daga Abi Sa'idil
Khudri ya ce, Manzon Allah (s) ya ce; Ya ku mutane, lallai ni hakika na bar
muku abinda in kuka rike a baya na ba za ku taba bacewa ba, (sune) littafin
Allah (Alkur'ani) da tsatso na iyalan gida na (Ahlul baiti)
(Albani ya fitar da wannan hadisi a cikin Sahihul jami'i, hadisi na 7877. Sannan ya inganta isnadinsa
(Albani ya fitar da wannan hadisi a cikin Sahihul jami'i, hadisi na 7877. Sannan ya inganta isnadinsa
5-
Ibn Arabi ya fitar a cikin littafinsa mai suna "Aridhatul Ahwazi" Juzu'i na bakwai shafi na 159, sannan ya inganta isnadin sa. Hadisin na cewa;
Ibn Arabi ya fitar a cikin littafinsa mai suna "Aridhatul Ahwazi" Juzu'i na bakwai shafi na 159, sannan ya inganta isnadin sa. Hadisin na cewa;
وقد تركت فيكم ما إن تمسكتم به لم تضلوا كتاب الله وعترتي أهل بيتي لن يتفرقا حتى يردا على الحوض
"Kuma hakika na bari a cikin ku abinda idan kuka rika ba za ku bace ba. (Sune) littafin Allah (Alkur'ani) da tsatso na iyalan gida na (Ahlul baiti). Ba zasu taba rabuwa da juna ba (Alkur'ani da Ahlul baiti) har sai sun tarar da ni a tabki (Alkausara a ranar kiyama).
6-
Al-Dahawi ya fitar a cikin littafinsa
"Mushkilul Athar" juzu'i na 5 shafi na 18. Kuma da ingantaccen sanadi
cewa;
لما
رجع
رسول
الله
صلى
الله
عليه
وسلم
عن
حجة
الوداع
ونزل
بغدير
خم
أمر
بدوحات
فقممن
ثم
قال
كأني
قد
دعيت
فأجبت
إني
قد
تركت
فيكم
الثقلين
أحدهما
أكبر
من
الآخر
كتاب
الله
عز
وجل
وعترتي
أهل
بيتي
فانظروا
كيف
تخلفوني
فيهما
فإنهما
لن
يتفرقا
حتى
يردا
علي
الحوض
ثم
قال
إن
الله
عز
وجل
مولاي
وأنا
ولي
كل
مؤمن
ثم
أخذ
بيد
علي
فقال
من
كنت
وليه
فهذا
وليه
اللهم
وال
من
والاه
وعاد
من
عاداه
فقلت
لزيد
سمعته
من
رسول
الله
صلى
الله
عليه
وسلم
قال
ما
كان
في
الدوحات
أحد
إلا
رآه
بعينيه
وسمع
بأذنيه
Yayin da Manzon
Allah (s) daga hajjin bankwana kuma ya sauka (yayi masauki) a tabkin khum
(Ghadir khum) sai ya yi umurni da tsayawa a karkashin wata biya. Sannan sai ya
ce; Kamar an kira ni kuma na amsa (zan bar duniya in koma ga Allah). Lallai ni
na bari a cikinku nauyayan abubuwa guda biyu. Dayan ya fi dayansa girma, (sune)
littafin Allah (Alkur'ani) mai girma da daukaka, da tsatso na iyalan gida na.
Ku kula da yanda zaku maye ni a cikinsu. Kuma lallai su (Alkur'ani da Ahlul
baiti) ba za su taba rabuwa ba har sai sun tarar da ni a tabki (alkausara a
ranar kiyama). Sannan sai ya ce; lallai Allah mai girma da daukaka shine
majibinci na kuma nine majibincin dukkan mumini. Sannan sai ya rike hannun
(Sayyidina) Ali, sai ya ce; duk wanda na kasance majibicinsa to wannan (Ali
a.s) majibincinsa ne. (Sai Manzon Allah (s)ya yi addu'a) ya Allah jibinci wanda
ya jibinci shi (Ali a.s) kuma ka yi gaba da wanda ya yi gaba da shi. (Sai mai
ruwayar ya ce) sai na ce wa zaidu, shin ka ji shi (wannan zancen) daga (bakin)
Manzon Allah (s)? Sai ya ce babu wani mutum guda da yake cikin wannan bishiyar
face ya ganshi da idanuwansa kuma ya ji da kunnuwansa.
7-
Ya zo a cikin
“Sunanul Kubra” na Imam Al-Nisa’i, juzu’i n 5 shafi na 130.
زيد بن أرقم (( إني قد تركت فيكم الثقلين أحدهما أكبر من الآخر كتاب الله وعترتي أهل بيتي فانظروا كيف تخلفوني )) السنن الكبرى للنسائي - (ج 5 / ص 130)
Daga Zaidu da Arkam
yace, Manzon Allah (s) ya fada cewa;
Lallai ni mai bari
ne a cikin ku abinda in kuka yi riko da shi ba za ku taba bacewa ba a baya na.
Dayansu ya fi dayansa girma, (sune) littafin Allah (Alkur'ani), da tsatso na
iyalan gida na . (Saboda haka) ku lura da yanda zaku maye mini a cikin su.
8-
Ya zo a cikin Sahihu Muslim juzu'i na 7 shafi 123 (bugun "darul fikr, Bairut.)
Ya zo a cikin Sahihu Muslim juzu'i na 7 shafi 123 (bugun "darul fikr, Bairut.)
انطلقت أنا
وحصين
بن
سبرة
بن
مسلم
إلى
زيد
بن
أرقم فلما جلسنا
إليه
قال
له
حصين
: لقد
لقيت
،
يا
زيد
! خيرا
كثيرا
. رأيت
رسول
الله
صلى
الله
عليه
وسلم
. وسمعت
حديثه
. وغزوت
معه
. وصليت
خلفه
. لقد
لقيت
،
يا
زيد
خيرا
كثيرا
. حدثنا
،
يا
زيد
! ما
سمعت
من
رسول
الله
صلى
الله
عليه
وسلم
. قال
: يا
ابن
أخي
! والله
! لقد
كبرت
سني
. وقدم
عهدي
. ونسيت
بعض
الذي
كنت
أعي
من
رسول
الله
صلى
الله
عليه
وسلم
. فما
حدثتكم
فاقبلوا
. وما
لا
،
فلا
تكلفونيه
. ثم
قال
: قام
رسول
الله
صلى
الله
عليه
وسلم
يوما
فينا
خطيبا
. بماء
يدعى
خما
. بين
مكة
والمدينة
. فحمد
الله
وأثنى
عليه
. ووعظ
وذكر
. ثم
قال
" أما بعد
. ألا
أيها
الناس
! فإنما
أنا
بشر
يوشك
أن
يأتي
رسول
ربي
فأجيب
. وأنا
تارك
فيكم
ثقلين
: أولهما
كتاب
الله
فيه
الهدى
والنور
فخذوا
بكتاب
الله
. واستمسكوا
به
" فحث على
كتاب
الله
ورغب
فيه
. ثم
قال
" وأهل بيتي
. أذكركم
الله
في
أهل
بيتي
. أذكركم
الله
في
أهل
بيتي
. أذكركم
الله
في
أهل
بيتي
Daga Yazid bin
Hayyan ya ce; Na tafi ni da Hassin bin Sabra bin Muslim zuwa ga Zaidu dan
Arkam, yayin da muka zauna sai Hassin ya ce masa, hakika ya kai Zaidu ka sadu
da alheri mai yawa, kaga Manzon Allah (s) kuma ka saurari hadisin (hadisan sa
masu yawa). Kuma ka yi yaki tare da shi kuma ka yi sallah a bayan sa. Lallai
hakika ya kai Zaidu ka sadu da alheri mai yawa, ka mana hadisi ya Zaidu na
abinda ka ji daga Manzon Allah (s).
Sai (Zaidu bin Arkam) ya ce; ya kai dan dan'uwa na, wallahi shekaruna sun yawaita kuma zamani na ya gabata, (saboda haka) na mance wasu sashen abinda na kiyaye daga Manzon Allah (s), (saboda haka) abinda na hadasto muku ku karba, abinda kuma na kasa tunowa to kada ku kallafa mini shi (dole sai na fada). Sannan sai ya ce "watarana Manzon Allah (s) ya mike yana mai huduba a cikin mu (sahabbai) a wurin wani ruwa (tabki) wanda ake kiran sa "Khumman" (ghadir khum) a tsakanin Makka da Madina. Sai (Annabi s.) ya yi godiya ga Allah kuma ya yi yabo gare shi, sannan ya yi wa'azi ya tunatar. Sannan sai ya ce; Bayan haka ku saurara ya ku mutane, lallai ni mutum ne, ya yi kusa Manzon Ubangijina ya zo (Mala'ikan mutuwa domin karban rai na in koma ga Allah) kuma in amsa kiran, to ni mai bari ne a cikin ku nauyayan al'amura guda biyu. Na farkonsu shine littafin Allah (Alkur'ani), ku yi riko da shi, sai ya yi horo akan littafin Allah kuma ya kwadaitar a cikin (al'amarin) sa. Sannan sai ya ce (abu na biyu) da iyalan gida na, (ya ci gaba da fadin cewa) ina tunatarwa (gargadi) gare ku game da iyalan gidana! ina tunatarwa (gargadi) gare ku game da iyalan gidana!! ina tunatarwa (gargadi) gare ku game da iyalan gidana!!!”
Sai (Zaidu bin Arkam) ya ce; ya kai dan dan'uwa na, wallahi shekaruna sun yawaita kuma zamani na ya gabata, (saboda haka) na mance wasu sashen abinda na kiyaye daga Manzon Allah (s), (saboda haka) abinda na hadasto muku ku karba, abinda kuma na kasa tunowa to kada ku kallafa mini shi (dole sai na fada). Sannan sai ya ce "watarana Manzon Allah (s) ya mike yana mai huduba a cikin mu (sahabbai) a wurin wani ruwa (tabki) wanda ake kiran sa "Khumman" (ghadir khum) a tsakanin Makka da Madina. Sai (Annabi s.) ya yi godiya ga Allah kuma ya yi yabo gare shi, sannan ya yi wa'azi ya tunatar. Sannan sai ya ce; Bayan haka ku saurara ya ku mutane, lallai ni mutum ne, ya yi kusa Manzon Ubangijina ya zo (Mala'ikan mutuwa domin karban rai na in koma ga Allah) kuma in amsa kiran, to ni mai bari ne a cikin ku nauyayan al'amura guda biyu. Na farkonsu shine littafin Allah (Alkur'ani), ku yi riko da shi, sai ya yi horo akan littafin Allah kuma ya kwadaitar a cikin (al'amarin) sa. Sannan sai ya ce (abu na biyu) da iyalan gida na, (ya ci gaba da fadin cewa) ina tunatarwa (gargadi) gare ku game da iyalan gidana! ina tunatarwa (gargadi) gare ku game da iyalan gidana!! ina tunatarwa (gargadi) gare ku game da iyalan gidana!!!”
Saboda haka matukar
mutum musulmi yana so ya yi addinin musulunci ingantacce to dole ya yi addini
irin yanda Ahlul baiti suka aikata ba irin yanda makiyan su Banu Umayya suka
sanya aka rubuta da sunan wai shine sunnar Annabi (s) ba.
Wani abin lura
shine ba zai dace da hankali ba ace an bar abubuwa guda biyu dukansu kundaye ba
tare da masu bayani ba. Kamar yanda Allah bai saukar da litattafai ga al’uma ba
face ya sanya Annabawa ne wadanda ya danka musu su kuma sune masu bayani abunda
ke kunshe a cikin litattafan.
Kenan wasici da
Alkur’ani da kuma masu fassara manufar abinda ke dauke a ciki (Ahlul baiti) shine
ya dace da hankali. Wadannan Ahlul baiti sune wadanda Allah Ya zaba ya tsarkake
su domin yin ingantaccen fassara ga Alkur’anin da kuma hakaito ingantattun
sunnoni na Annabi (s) tare da ingantattun fassarorinsu ba tare da kuskure ko
taki ba, ta yanda zai zamo musulmai sun zama amintattu kuma tsararru daga
fadawa tarkon masu jirkita koyarwan addini.
Wa
sallallaahu alaa Muhammad wa alaa aalihit taahiriin.
Murtala Isah Dass
(1st
RABI’US THANI, 1439 / 20 DECEMBER, 2017)
Domin neman Karin bayani/ Gyara ko
Kalu-bale, a tuntubeni ta daya daga cikin wadannan lambobi;
08133289306, 08058636125
& 07083030309.
Haka ma za a iya saduwa da ni ta
Whatsapp a wannan lambar; 08058636125
Ko a sadu da ni ta daya daga cikin
wadannan Adireshin Email:
Sannan ana iya samun wannan kasida da
wasu makamantan sa a wannan website na internet:
Comments
Post a Comment