Skip to main content

Posts

MENENE TAMBAYOYIN DA ‘YANMATA SUKE YI??? NA 1

MENENE TAMBAYOYIN DA ‘YANMATA SUKE YI??? ماذا تسأ ل الفتيات؟ NA   - 1 DAGA “CIBIYAR NUUN” MASU WALLAFA DA TARJAMA FASSARA: MURTALA ISAH DASS MUKADDIMA A kwai tambayoyi (masu yawa) da suke kekkewayawa a cikin rai (kwakwalwar) ko wace budurwa, wadanda take bukatar amsar su, wani lokaci takan koma wajen uwarta ko 'yar'uwarta ko kawarta ko kuma wajen malamarta ta makaranta. Saidai wani lokaci bata gamsuwa da amsar da suke bata. Saboda haka sai kaga son sanin wadannan abubuwan na tunkudata zuwa ga tambayoyi masu dinbin yawa (alhali ta rasa mai bata gamsassun amsoshi) Yawancin uwaye kunya na lullubesu (suna jin kunya) game da amsa wasu sashen tambayoyi masu tsarkakiya. (Sannan wani bangare kuma ita kanta budurwar ce take jin kunyar yin tambayar alhali abin na damunta tana so ta sami bayani a kan su) Wannan littafi da ke gaba gareki ya ke 'yar'uwata abar girmamawa, tattararrun tambayoyi ne daga cikin tambayoyi wadanda ake jin kunyar ...
Recent posts

SHAFAN KAFAFUWA A ALWALA KO WANKEWA?

SHAFAN KAFAFUWA A ALWALA KO WANKEWA? Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin duniyoyi. Tsira da amincin Sa su kara tabbata bisa Manzon Sa Muhammadu da iyalan gidan sa masu tsarki da sahabban sa managarta, tare da sauran Annabawa da Manzannni, da wadanda suka bi hanyarsu har zuwa ranar sakamako. A ddinin Musulunci addini ne na mika wuya ga Allah Madaukakin sarki. Shi Allah Ya halicci ‘dan adam da aljani ne domin su bauta masa, bai yarda da bautan wanin saba in ba shi kadai ba. Wannan bauta kuma bai yarda mutum ya yi shi yanda yaga dama ba, sai ya aiko Manzannin Sa Ya saukar ga kowannen su da littafi mai dauke da yanda yake so su gudanar da bautar. Saboda haka aiki zai zamo kar6a66e ne a waje Allah kawai idan ya dace da yanda yayi umurni a yi. Manzo na qarshe da Allah ya aiko shine Annabi Muhammadu (s) tare da littafi Alkur’ani mai girma, ta yanda Ya umurci wannan al’uma da aikin ibadu nau’i dabam-dabam ciki kuwa har da Sallah, kuma ya zamo ma shine mafi girman a cikin su. Kuma shi ...