Skip to main content

SHAFAN KAFAFUWA A ALWALA KO WANKEWA?


SHAFAN KAFAFUWA A ALWALA KO WANKEWA?

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin duniyoyi. Tsira da amincin Sa su kara tabbata bisa Manzon Sa Muhammadu da iyalan gidan sa masu tsarki da sahabban sa managarta, tare da sauran Annabawa da Manzannni, da wadanda suka bi hanyarsu har zuwa ranar sakamako.
Addinin Musulunci addini ne na mika wuya ga Allah Madaukakin sarki. Shi Allah Ya halicci ‘dan adam da aljani ne domin su bauta masa, bai yarda da bautan wanin saba in ba shi kadai ba. Wannan bauta kuma bai yarda mutum ya yi shi yanda yaga dama ba, sai ya aiko Manzannin Sa Ya saukar ga kowannen su da littafi mai dauke da yanda yake so su gudanar da bautar. Saboda haka aiki zai zamo kar6a66e ne a waje Allah kawai idan ya dace da yanda yayi umurni a yi.
Manzo na qarshe da Allah ya aiko shine Annabi Muhammadu (s) tare da littafi Alkur’ani mai girma, ta yanda Ya umurci wannan al’uma da aikin ibadu nau’i dabam-dabam ciki kuwa har da Sallah, kuma ya zamo ma shine mafi girman a cikin su. Kuma shi Manzon ya koyar da wadannan ibadu a aikace a fili kuma filla-filla.
To saidai wannan addini na Musulunci ya gamu da ibtila’i a inda bayan rasuwar Manzon (s) aka sami sa6ani dangane da alamura masu yawa, sakamakon jarrabar addinin da akayi da wasu gur6atattun masu da’awar musulunci a baka amma baikai zuci ba, wadanda suka yi ta kawo cikas. Hatta abubuwan da basu dace ace an sami sa6ani akansu ba kamar wannan ibada na sallah wanda a daukacin rayuwar Ma’aiki (s) tun bayan aiko shi da sakon Annabta yake yi tare da jama’a sau biyar a kowani yini, amma sai gashi an sami al’umar musulmi sun yi sa6ani akan sa sakamakon kokarin irin wadannan gurbatattu na ganin sun jirkita addinin koma su kawo karshen sa. 
Babban abin takaici shine tun ba’a je ko ina ba sai ga tarihi na nuna cewa Sahabin Annabi kuma hadimin sa “Anas bin Malik” kamar yanda Bukhari ya fitar a Sahihin sa;
Bayan rasuwar Ma’aiki (s) da yayi tafiya zuwa Sham, yaje masallaci akayi salla dashi, da ya komo masaukin sa sai aka ga yana kuka, sai aka tambaye shi me ya sa yake kuka? Sai ya ce babu wani abu na addini wanda jama’a basu jirkita shi ba daga yanda Manzon Allah (s) ya aikata ko ya koyar, sai wannan sallah da mukeyi, to amma sai ya ga ita sallar ma an jirkita ta.
عن الزهري أنه قال : دخلت على أنس بن مالك بدمشق وهو يبكي ، فقلت : ما يبكيك ؟ فقال : لا أعرف شيئا مما أدركت إلا هذه الصلاة ، وهذه الصلاة قد ضيعت
Daga Zuhriy yace; Na shiga wajen Anas bin Malik a Dimashk yana kuka, sai na tamaye shi, me ya sanyaka kuka? Sai ya ce “bansan wani abu cikin abinda na riska (a wannan zamani da ake aikatawa daidai da yanda yake a shara’ance ba) face wannan sallah, to ita ma wannan sallar an walakantata (an jirkitata)”
(Sahihul Bukhari, Juzu’i na 1, shafi na 134)

Kamar yanda Imam Ahmad bin Hanbal shima ya rawaito irin wannan hadisi inda yake cewa da aka tambayi Anas bin Malik cewa me yasanyaka kuka?
عن أنس قال : ما أعرف فيكم اليوم شيئا كنت أعهده على عهد رسول الله صلى الله عليه وسلم غير قولكم : لا إله إلا الله
 Sai ya amsa da cewa; bansan wani abu na addini da ake yi a lokacin Manzon Allah (s) wanda yau ba a jirkita shi ba, face fadar “la’ilaha illallahu” da kuke yi.
(Musnad Ahmad bin Hanbali, juzuI na 3 shafi na 270)

Wannan babban abin takaici ne dake nuna zurfin irin hatsarin da wannan addini ya shiga ciki tun bai wuce karnin farko ba, tun sahabban Annabin basu gama barin duniya ba amma an canza al’amuran addinin. Sannan wannan canji bai tsaya ga wasu ayyuka masu wuyan sha’ani kawai ba, a’a har ma ayyukan da Manzon Allah (s) yake yi tare da jama’a ko wane rana akalla sau biyar wato sallolin farilla na kowace yini.

Ita ma mukaddimar da ake gabartarwa kafin shi wannan sallah wato Alwala kenan bai tsira daga wannan jirkita ba. Manzon Allah (s) ya kasance yana yin alwala a gaban iyalan sa, hakama a gaban sahabban sa na kimanin shekaru ashirin da uku amma ace wai an sami sabani game da yanda ake yin sa.
A matakin farko Ayan Alkur’ani ya karantar da yanda ake alwala a yayin da yake cewa;
يا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذا قُمْتُمْ إِلَى الصَّلاةِ فَاغْسِلُوا وُجُوهَكُمْ وَأَيْدِيَكُمْ إِلَى الْمَرافِقِ وَامْسَحُوا بِرُؤُسِكُمْ وَأَرْجُلَكُمْ إِلَى الْكَعْبَيْنِ
“Ya ku wadanda sukayi imani idan kun tashi zuwa ga salla ku wanke fuskokin ku da hannayen ku zuwa gwiwoyi, kuma ku shafi kayukan ku da kafafuwan ku zuwa dugadugi. (Ma’ida, aya ta 6).
Kuma abinda akayi ittifaki shine babu yanda za a yi Manzon Allah (s) ya sabawa karantarwar Alkur’ani.
Amma sai gashi an canza shafan kafa zuwa wankewa. Domin a ‘kare hakan sai aka kawo tawile-tawile na wasali game da fassarar ayar don a nuna dacewar wanke kafafuwan ne ayar tazo dashi. 
A yayin da Ahlul baiti a.s da mabiya karantarwar su suka tsayu akan abinda Alkur’ani ya koyar na yin shafa akan kafafuwa kuma kamar yanda suka ga kakan su Manzon Allah (s) yake yi kuma ya koyar da al’uma. Sannan Manzon ya hori al’uma da rikon shiryarwarsu a bayan sa, a inda yake cewa;
اني تارك فيكم ما ان تمسكتم به(أو بهما) لن تضلوا بعدي ، احدهما اعظم من الاخر : كتاب الله حبل ممدود من السماء إلى الارض ، وعترتي أهل بيتي
)صحيح مسلم باب فضائل علي بن ابي طالب ومسند احمد 4 / 366 ، وسنن الدارمي  2 / 431 باختصار ،
وسنن البيهقي  2 / 148 و 7 / 30 منه باختلاف يسير في اللفظ(
“Lallai na bar muku nauyayan abubuwa guda biyu a baya na wadanda idan kuka rike su ba zaku bace ba, sune littafin Allah (Alkur’ani) igiya mikakkiya daga sama zuwa kasa da iyalan gida na (Ahlul baiti)”

Mahukuntan Banu Umayya su suka aukar da wannan canji na Alwala wanda ya faro tun lokacin khalifancin Usman bin Affan.
Sahabban Manzon Allah irin su shi wannan hadimin Manzo Anas Bin Malik, Abdullahi dan Abbas da makamantansu sun yi fama da gwagwarmaya wajen ganin cewa Musulmai basu canza wannan ibada ta alwala daga shafan kafa zuwa wankewa ba, amma ina! sakamakon hukumomin Banu Umayya sun tsaurara da tilasta jama’a, basu sami nasara ba.
Mahukuntan Umayyawa irin su Hajjaj As-sakafiy su suka rika tilasta Mutane wajen wanke kafafuwan su maimakon shafawa. A yayin da Su Ibn Abbas da  irin su Anas bin Malik din suka yi tawaye kuma suke yin fatawa wa mutane da su rika shafan kafafuwan su domin haka yake a cikin Alkur’ani kuma Haka Manzon Allah ya kasance yake yi. Kamar yanda yazo a cikin tafsirin Ibn Kasir da tafsirin Ibn Jarir Tabari a karkashin tafsirin ayan alwala, cewa;
قال موسى بن أنس ونحن عنده: يا أبا حمزة إِنّ الحجّاج خطبنا بالاَهواز ونحن معه، فذكر الطهور فقال: اغسلوا وجوهكم وأيديكم وامسحوا بروَوسكم وأرجلكم وأنّه ليس شيء من ابن آدم أقرب من خبثه من قدميه، فاغسلوا بطونهما وظهورهما وعراقيبهما، فقال أنس: صدق اللّه وكذب الحجاج، قال اللّه تعالى: (وامسحوا بروَوسكم وأرجلكم) . قال: وكان أنس إذا مسح قدميه بلّها

(A yayin da aka taho ana bada labari wa shi Anas cewa) Hajjaj yazo yana mana huduba yana ce mana idan zamu yi alwala mu wanke ciki da bayan kafafuwan mu domin babu wani gaba a jikin danadam da yafi kusa da daukan najasa kamar kafa. Sai Anas yace; Allah Ya yi gaskiya kuma Hajja yayi karya, saboda Allah cewa Yayi ku shafi kawukanku da kafafuwanku. Kuma sai ya bayyana cewa shi Anas idan yana alwala shafa kafafuywansa yake yi.

Shima Ibn Abbas akwai hadisai da dama da suke nuna yanda yayi ta irin wannan gwagwarmaya da wannan canjin na mahukuntan Banu Umayya, kamar yanda yazo a cikin Tafsirin Durrul Mansur a karkashin tafsiri Ayar alwala cewa;
قال ابن عباس: أبى الناس إلاّ الغسل، ولا أجد في كتاب اللّه إلاّ المسح
 Mutane sun ki (zancen shafa kafa a alwala sun nace) sai wankewa, ni kuma ban sami hakan a littafin Allah (Alkur’ani) ba face (umurni) da shafawa.

Wannan lamari har ya kai ga wasu sahabbai masu jin tsoron musgunawar hukuma sai sun 6uya suke koya wa mutane yin sallah da alwala da sauran alamuran addini kamar yanda yake a hukunci. 
Yazo a cikin Musnad da Mu’ujamul Kabir cewa;
عن أبي مالك الاَشعري أنّه قال لقومه: اجتمعوا أصلّـي بكم صلاة رسول اللّه - صلّى اللّه عليه وآله وسلّم - فلما اجتمعوا قال: هل فيكم أحد غيركم؟ قالوا: لا، إلاّ ابن أُخت لنا، قال: ابن أُخت القوم منهم، فدعا بجفنة فيها ماء، فتوضّأ ومضمض واستنشق، وغسل وجهه ثلاثاً، وذراعيه ثلاثاً، ومسح برأسه وظهر قدميه، ثم صلّـى بهم
 Sahabi Abi Malikil Ash’ari yana fada wa mutanen sa (kabilarsa) cewa ku taru domin in koya muku irin sallar Manzon Allah (s),a yayin da suka tattaru sai yace musu; shin akwai wani a cikin ku wanda ba kuba? Sai sukace a’a saidai dan yar’uwarmu, sai Abi Malik din yace ai dan yaruwan mutane yana cikin su. (yana wannan bincike ne domin tsoron kada wani yaga abinda zai aikata yaje ya sanar da hukuma cewa ga wani yana koyar da mutane salla sabanin yanda hukuma ta yarda ayi) sannan sai ya sanya aka kawo masa ruwa sai yayi alwala, a yayin alwalar tasa bayan ya kammala wanke fuska da hannayen sa, sai ya shafi kansa da kafafuwansa.
 (Musnad Ahmad bin Hanbal, juzu’i na 5 shafi na 342. Muajamul kabir, juzui 3 shafi 280)

Sannan sai wadannan mahukuntan na Banu Umayya suka sanya aka kirkiro hadisai wadanda yanzu aka cika litattafai da su wadanda suke nuna cewa wai Manzon Allah (s) yana wanke kafafuwansa ne a yayin da yake alwala. Saidai a gefe guda kuma akwai dimbin hadisai a cikin litattafan na Ahlus Sunna wadanda suke nuni da cewa Manzo (s) shafa kafafuwan sa yake yi. Saidai abinda ra’ayi ya hadu tsakanin musulmi shine duk lokacin da hadisai guda biyu suka taho masu karo da juna, to mataki na farko shine a gittasu ga Alkur’ani mai girma ne, duk hadisin da ya dace to shine ingantacce, wanda ya saba wa Alkur’ani sai ayi jifa dashi a garu. Anan babu wahalan binciken sahihanci ko rashin sahihanci sa ta bangaren maruwaita (jarhu wat ta’adil)

HADISAN SHAFA KAFA A ALWALA DAGA RUWAYOYIN AHLUS SUNNA.

A bayanin da ya gabata an bayyana dalilin faruwar canjin shafan kafa a alwala zuwa wankewa, wadda sarakunan banu umayya suka aukar, kuma aka kirkiro hadisai wadanda suke ‘kare wannan canji aka dangana su zuwa ga Manzon Allah (s) alhali Allah Ta’ala Ya yi bayani a cikin Alkur’ani karara yanda za’ayi alwala a inda Ya yi umurni a wanke fuska da hannaye, sannan shafi kai da kafafuwa.

A yayin da Ahlul baiti (a.s) da Mabiyansu suke shafa kafafuwansu a yayin alwala kamar yanda Allah Ta’ala yayi umurni kuma Annabin da aka aiko shi da wannnan ibada shima yake aikata haka.
Su kuma Ahlus sunna suke wanke kafafuwan su kamar yanda malaman sun a fikhu suka bada fatawa bisa dogaro da wadancan hadisai.

To saidai kamar yanda na ambata a baya, a cikin litattafansu na ruwayoyi akwai hadisai birjik wadanda suke nuna cewa Manzon Allah s. shafa kafafafuwansa yake yi a yayin alwala ba wankewa ba. sannan wasu ruwayoyin sun nuna yanda wasu sahabbai suke karantar da mutane cewa shafa kafa akeyi yayin alwala ba wankewa ba . Kuma anyi ittifaki cewa duk lokacin da ruwayoyi biyu suka taho masu karo da juna, to ana bijirar das u ne bisa alkur’ani., duk wanda yayi daidai da karantarwar alkur’ani to shine ingantacce, wanda ya saba masa kuwa sai ayi jifa da shi.
Ga kadan daga cikin irin wadannan ruwayyoyi:

1-
عن بسر بن سعيد قال : أتى عثمان المقاعد فدعا بوضوء فتمضمض واستنشق ثمّ غسل وجهه ثلاثا ويديه ثلاثا ثلاثا ومسح برأسه ورجليه ثلاثا ثلاثا ، ثمّ قال : رأيت رسول الله صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم هكذا توضّأ ، يا هؤلاء أكذلك؟ قالوا : نعم ، لنفر من أصحاب رسول الله صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم عنده.
An karbo hadisi wanda ya tuke daga Basr dan Sa’id yace; Usman (bin Affan) yazo mazaunin sa, sai ya bukaci yin alwala (a yayin alwalar tasa) sai yayi kurkurar baki kuma ya sheka ruwa (a hancin sa), sannan sai ya wanke fuskar sa sau uku da hannayen sa sau uku-uku sai Ya Shafi Kansa Da Kafafuwan Sa sau uku-uku. Sannan sai yace “ Na ga Manzon Allah (s)  haka yake alwala.” (sannan sai ya juyo ya fuskanci jama’an da suke tare dashi sai ya tambaye su yace musu) “ yaku wadannan (jama’a) haka yake?” Sai suka ce “haka ne” (yayi tambaya ne) ga wasu sashen sahabban Manzon Allah s.a.w.a wadanda suke tare dashi a wajen. (Musnad na Ahmad Bin Hambal, juzu’i na 1, shafi na 109, hadisi na 489)

2-
عن حمران قال : دعا عثمان بماء فتوضّأ ثمّ ضحك ، ثمّ قال : ألا تسألوني ممّ أضحك؟ قالوا : يا أمير المؤمنين ما أضحكك؟ قال : رأيت رسول الله صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم توضّأ كما توضّأت ، فتمضمض واستنشق وغسل وجهه ثلاثا ويديه ثلاثا ومسح برأسه وظهر قدميه.
An karbo hadisi da ya tuke daga Humran yace; Usman ya bukaci ruwa, sai yayi Alwala sannan sai yayi dariya. Sannan sai yace “ ba za ku tambaye ni don me nake dariya ba?” sai suka ce ; “ya shugaban muminai me ya sa ka dariya?” sai yace “Na ga manzon Allah yayi Alwala kamar yanda nayi Alwala. Sai yayi kurkuran baki kuma ya sheka ruwa kuma ya wanke fuskar sa sau uku kuma ya wanke hannayen sa sau uku-uku, sai yayi shafa a kansa da bayan kafafuwan sa.
(Kanzul ummal juzu’i na 9, shafi na 436, hadisi na 26,863).

3-
عن أبي مطر قال : بينما نحن جلوس مع علي في المسجد ، جاء رجل إلى علي وقال : أرني وضوء رسول الله صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم فدعا قنبر ، فقال : ائتني بكوز من ماء فغسل يديه ووجهه ثلاثا ، فأدخل بعض أصابعه في فيه واستنشق ثلاثا ، وغسل ذراعيه ثلاثا ومسح رأسه واحدة ورجليه إلى الكعبين ولحيته تهطل على صدره ثمّ حسا حسوة بعد الوضوء ثمّ قال : أين السائل عن وضوء رسول الله صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم ، كذا كان وضوء رسول الله صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم.

 An karbo hadisin daya tuke daga Abi Matar, yace wata rana muna zaune tare Aliyu (r.a) a cikin Masallaci, sai wani mutum yazo wajen Ali sai yace; ka nuna min alwalar Manzon Allah s.a.w.a. sai (Ali a.s) ya kira Kambar sai yace ka taho mini da butan ruwa. Sai ya wanke (tafukan) hannayen da fuskar sa sau uku-uku, sai ya shigar da sashen yatsun sa a cikin bakin sa, kuma ya sheka ruwa (a hancin sa) sau uku-uku. Sannan ya wanke damasun sa sau uku-uku, kuma ya shafi kansa sau daya da kafafuwan sa zuwa dugadugi, a yayin dagemun sa take saukowa akan kirjin sa, sannan sai ya kurbi (ruwan) kurbi guda bayan yayi alwalan. Sannan sai yace “ina mai tambaya game da Alwalar Manzon Allah s.a.w.a , to haka Alwalar Manzon Allah (sawa) take. 
(Kanzul Ummal, juzu’i na 9 shafi 448, hadisi na26,908.)

4-
عن عباد بن تميم ، عن أبيه ، قال : رأيت رسول الله صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم توضّأ ومسح بالماء على لحيته ورجليه
 An karbo hadisi daga Ubad dan Tamim, daga Baban sa yace; Na ga Manzon Allah (s) yana Alwala sai ya shafi gemun sa da kafafuwan sa.
(Kanzul Ummal, juzu’i na 9 shafi 429, hadisi na26,822.)


5-
عن علي بن أبي طالب عليه‌السلام ؛ قال : كنت أرى أنّ باطن القدمين أحق بالمسح من ظاهرهما حتى رأيت رسول الله صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم يمسح ظاهرهما

An ruwaito Hadisi daga (Imam) Ailiyu Bin Abi Talib (a.s) yace Na kasance ina ganin cewar cikin (tafin) kafa shi yafi dacewa da wajen shafawa maimakon bayan sa, har sai da na ga Manzon Allah s.a.w.a yana shafa bayan su.
(Musnad na Ahmad Bin Hanbal, juzu’i na 1, Hadisi na 739 da na 919)

6-
عن رفاعة بن رافع انّه سمع رسول الله صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم يقول : « إنّه لا يجوز صلاة أحدكم حتى يسبغ الوضوء كما أمره الله عزّ وجلّ ، ثمّ يغسل وجهه ويديه إلى المرفقين ، ويمسح رأسه ورجليه إلى الكعبين
An karbo Hadisi daga Rafa’a Bin Rafi’u cewa shi ya ji Manzon Allah (s) yana cewa “lallai Sallar dayan ku baya halatta har sai ya cika Alwalakamar yanda Allah Mai girma da daukaka yayi umurni, sannan (sai ya gwada musu yanda ake alwalar) ya wanke fuskar sa da hannayen sa zuwa gwiwan hanu, kuma ya shafi kayin sa da kafafuwan sa zuwa dugadugi.
(Sunanu Ibn Maja, Juzu’i na 1,Hadisi na 460. Sunanin Nisa’I, juzu’I na2, shafi na 226)



7-
عن عباد بن تميم المازني ، عن أبيه انّه قال : رأيت رسول الله صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم يتوضّأ ويمسح الماء على رجليه
Daga Ubada Bin Tamim Al-azaniy, daga Baban sa yace; Naga Manzon Allah (s)yana Alwala sai yana shafa ruwa akan kafafun sa.
(Sunani Ibn Majah, juzu’i na 1, Hadisi na 460)

8-
عن أوس بن أبي أوس الثقفي أنّه رأى النبي صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم أتى كظامة قوم بالطائف ، فتوضّأ ومسح على قدميه
Daga Aws Bin Abi Aws as-Saqafiy, cewa yaga Annabi (s) yazo kududdufin wasu jama’a a Ta’if, sai yayi Alwala (a yayin da ya wanke fuska da hannayen sa) sai yayi shafa akan kafafuwan sa.
(Tafsirul Tabari, Juzu’i na 6 shafi na 86/ Mu’ujamul Kabir, juzu’i na 1 shafi 221, mai lambar hadisi na 603)

9-
عن رفاعة بن رافع قال : كنت جالسا عند رسول الله صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم إذ جاءه رجل فدخل المسجد ، فصلّى فلمّا قضى الصلاة جاء فسلم على رسول الله صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم فقال رسول الله صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم ارجع فصلّ فإنّك لم تصل
فقال رسول الله صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم : إنّه لا تتم صلاة أحدكم حتّى يسبغ الوضوء كما أمره الله ، فيغسل وجهه ويديه إلى المرفقين ، ويمسح برأسه ورجليه إلى الكعبين
Daga Rafa’a ‘dan Rafi’u yace; na kasance ina zaune a wajen Manzon Allah (s) sai wani mutum yazo ya shiga Masallaci sai yayi salla………. (har zuwa inda yake cewa) sai Manzon Allah yace lallai Sallar dayanku bata cika har sai ya cika Alwala kamar yanda Allah Yayi umurni, ya wanke fuskar sa da hannayen sa zuwa gwiwoyi, kuma ya shafi kan sa da kafafuwan sa zuwa dugadugi……….
(wannan Hadisi za a same shi cikin Mustadarak na Hakim an-Nisaburiy, juzu’i na 1 shafi na 241)

10-
عن ابن عباس انّه قال : ذكر المسح على القدمين عند عمر وسعد وعبد الله بن عمر فقال عمر بن الخطاب : سعد أفقه منك ، فقال عمر : يا سعد انّا لا ننكر انّ رسول الله صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم مسح ـ أي على القدمين

Daga ibn Abbas yace; Anyi zancen Shafa Akan Kafafuwa a wajen Umar da Sa’ad da Adullahi ‘dan Umar. Sai Umar ‘Dan Khaddabi yace; Sa’ad ya fika ilmi’ sai Umar yace ya Sa’ad “ Bamu musun cewa Manzon Allah yayi shafa (ai akan kafafuwan sa a yayin Alwala)
(Tafsir Durrul Mansur, Jalaluddin Suyuti, juzu’i na 3 shafi na 29)

11-
عن عروة بن الزبير انّ جبرئيل عليه‌السلام لمّا نزل على النبي صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم في أوّل البعثة فتح بالإعجاز عينا من ماء فتوضأ ومحمد صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم ينظر إليه فغسل وجهه ويديه إلى المرفقين ومسح برأسه ورجليه إلى الكعبين ، ففعل النبي محمد صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم كما
رأى جبرئيل يفعل. (
Daga Urwah ‘Dan Zubair (yace); Lallai (Mala’ika) Jabra’il a.s yayin daya sauko zuwa ga Annabi (s) a farkon tayarwa (bashi Annabci), ya bude idaniyar ruwa da mu’ujiza, sai yayi Alwala, a yayin da Muhammadu s.a.w.a yana duba zuwa gare shi (yana kallon yanda yake Alwalar). Sai ya wanke fuskar sa da hannuwan sazuwa gwiwoyi sai ya shafi kan sa da kafafuwan sa zuwa dugadugi. Sai Annabi Muhammadu (s) ya aikata (yayi Alawalarsa) kamar yanda yaga Jabra’il yake aikatawa.
(Khasa’isul Kubra, na Imam Suyudiy, Juzu’i na 1 shafi na 94)
12-
روى عبد الرحمن بن جبير بن نفير ، عن أبيه انّ أبا جبير قدم على النبي صلى‌الله‌عليه‌وآله‌وسلم مع ابنته التي تزوجها رسول الله ، فدعا رسول الله بوضوء فغسل يديه فأنقاهما ، ثمّ مضمض فاه واستنشق بماء ، ثمّ غسل وجهه ويديه إلى المرفقين ثلاثا ، ثمّ مسح رأسه ورجليه. (

Abdulrahman ‘Dan Jubair ‘Dan Nufair ya rawaito daga Baban sa cewa, Jubair ya gabata ga Manzon Allah (s) tare ‘yar sa wacce Manzon Allah (s) ya aure ta , sai Manzon Allah ya bukaci yin alwala, (a yayin Alwalar) saiya wanke hannayen sa ya tsaftace su sannan yayi kurkura bakin sa, sai yayi shakan (hanci) da ruwa. Sannan ya wanke fuskar sa da hannayen sa zuwa gwiwoyi sau uku-uku, sannan ya shafi kan sa da kafofin sa.
(Kanzul Ummal, juzu’i na 5, Shafi na 106)

13-
حدّثنــا عبد اللّه، حدثني أبي حدثنا وكيع، حدثنا الاَعمش، عن أبي إسحاق، عن عبد خير، عن علي بن أبي طالب عليه السّلامقال: كنت أرى أنّ باطن القدمين أحقّ بالمسح من ظاهرهما حتى رأيت رسول اللّه - صلّى اللّه عليه وآله وسلّميمسح ظاهرهما 
Daga Abi Is’hak, daga Abdi Khair, daga Ali (r.a) yace “Da addini da ra’ayi ne da cikni (tafin) kafa shi yafi dacewa wajen shafawa daga bayan sa (a yayin Alwala), saidai naga Manzon Allah s.a.w.a yana shafa bayan su ne(saman tafin kafafuwa.”
(Musannaf na Ibn Abi Shaiba, juzu’i na 1 Shafi na 30)

14-
حدثنا عبد اللّه، حدثنا إسحاق، حدثنا سفيان قال: رأيت
علياً عليه السّلام توضّأ فمسح ظهورهما 
Daga Sufyan yace; Naga Aliyu (r.a) ya yi Alwala saiya shafi bayan su (kafafuwan sa)
(Musnad na Ahmad Bin Hanbal, Hadisi na 1018)
15-
عن حمران، انّه قال: رأيت عثمان دعا بماء غسل فغسل كفيه ثلاثاً، ومضمض و استنشق، وغسل وجهه ثلاثاً، وذراعيه ثلاثاً، ومسح برأسه وظهر قدميه 
Daga Humran yace; Naga Usman (Bin Affan) ya bukaci ruwa, sai ya wanke tafukan (hannuwan) sa sau uku uku, sai yayi kurkuran baki ya sheka ruwa ya wanke fuskar sa sau uku uku, sai ya shafi kan sa da bayan kafafuwan sa.
(kanzul Ummal, juzu’i na 5 Shafi na106)

16-
عن عكرمة، عن ابن عباس قال: الوضوء غسلتان ومسحتان
 Daga Ikrima daga Ibn Abbas yace; Alwala dai wanki biyu ne da shafa biyu (wanke fuska da hannuwa , shafan kai da kafafuwa)
(Tafsirul Tabari, juzu’i na 6 shafi na 82)

17-
حدثني يعقوب، قـال: حدثنا ابن عليـة، قـال عبد اللّه العتكي، عن عكرمة، قال: ليس على الرجلين غسل، إِنّما نزل فيهما
Daga Abdullahi al-Utkiy, daga Ikrima yace; Ba wanki ake wa kafafuwa (a Alwala) ba, abinda ya sauko (daga umurnin Allah) a game da su (hukuncin kafafuwa) shine shafawa.
(Tafsirul Tabari, juzu’i na 6 shafi na 82)

18-
عن جابر، عن أبي جعفر الباقر عليه السّلامقال: امسح على رأسك وقدميك 
Daga Jabir (Bin Abdullahi al-Ansariy), daga Abi Ja’far al-Baqir (as) yace; kayi shafa akan ka da kafafuwan ka.
(Tafsirul Tabari, juzu’i na 6 shafi na 82)

19-
حدثني يعقوب، قال: حدثنا ابن علية بن داود، عن الشعبي انّه قال: إنّما هو المسح على الرجلين ألا ترى أنّه ما كان عليه الغسل جعل عليه المسح، وما كان عليه المسح أهمل يريد ما كان عليه الغسل في الوضوء جعل عليه المسح في التيمم وما كان عليه المسح في الوضوء أهمل في التيمم
Daga Ibn Ulayya Bin Daud, daga Aamir ash-Sha’biy yace; Lallai abin sani kawai shafa (aka yi umurni da ayi) a kan kafafuwa. Shin baka gani ga6an da ake wankewa (a Alwala) an sanya a yi shafa a kan sa, sannan ga6an shafawa a barsu a cikin Taimama?
(Tafsirul Tabari, juzu’i na 6 shafi na 82)

20-
حدثنا ابن المثنى، قال: حدثنا عبد الوهاب، قال: حدثنا داود، عن عامر الشعبي انّه قال: أمر أن يمسح في التيمم ما أُمر أن يغسل في الوضوء، وأُبطل ما أُمر أن يمسح في الوضوء الرأس والرجلان .
Daga Aamir ash-Sha’biy yace; anyi umurni da a shafa a cikin Taimama inda akayi umrni da a wanke a Alwala, sai aka soke (shafan) abinda akayi umurni a shafa a cikin alwala, sune Kai da Kafafuwa.
(Tafsirul Tabari, juzu’i na 6 shafi 

21-
حدثنا أبو بشير الواسطي إسحاق بن شاهين قال: حدثنا خالد بن عبد اللّه، عن يونس، قال: حدثني من صحب عكرمة إلى واسط، قال: فما رأيته غسل رجليه انّما يمسح عليهما حتى خرج منها 
 An karbo Yunus yace; Wanda yayi rakiya wa Ikrima zuwa Wasit ya fada min cewa “ban taba ganin sa (Ikrima) yana wanke kafafuwan sa ba (a yayin yin alwalar sa), abin sani kawai yakan yi shafa ne a kansu har ya fita daga cikin ta (garin Wasit).
(Tafsirul Tabari, juzu’i na 6 shafi na 82)

Wa sallallaahu alaa Muhammad wa alaa aalihit taahiriin.


Murtala Isah Dass
(22 RABI’UL AWWAL, 1439 / 11 DECEMBER, 2017)
Domin neman Karin bayani/ Gyara ko Kalu-bale, a tuntubeni ta daya daga cikin wadannan lambobi;
08133289306, 08058636125 & 07083030309.
Haka ma za a iya saduwa da ni ta Whatsapp a wannan lambar;
08058636125
Ko a sadu da ni ta daya daga cikin wadannan Adireshin Email:
Sannan ana iya samun wannan kasida da wasu makamantan sa a wannan website na internet:

Comments

Popular posts from this blog

MENENE TAMBAYOYIN DA ‘YANMATA SUKE YI??? NA 1

MENENE TAMBAYOYIN DA ‘YANMATA SUKE YI??? ماذا تسأ ل الفتيات؟ NA   - 1 DAGA “CIBIYAR NUUN” MASU WALLAFA DA TARJAMA FASSARA: MURTALA ISAH DASS MUKADDIMA A kwai tambayoyi (masu yawa) da suke kekkewayawa a cikin rai (kwakwalwar) ko wace budurwa, wadanda take bukatar amsar su, wani lokaci takan koma wajen uwarta ko 'yar'uwarta ko kawarta ko kuma wajen malamarta ta makaranta. Saidai wani lokaci bata gamsuwa da amsar da suke bata. Saboda haka sai kaga son sanin wadannan abubuwan na tunkudata zuwa ga tambayoyi masu dinbin yawa (alhali ta rasa mai bata gamsassun amsoshi) Yawancin uwaye kunya na lullubesu (suna jin kunya) game da amsa wasu sashen tambayoyi masu tsarkakiya. (Sannan wani bangare kuma ita kanta budurwar ce take jin kunyar yin tambayar alhali abin na damunta tana so ta sami bayani a kan su) Wannan littafi da ke gaba gareki ya ke 'yar'uwata abar girmamawa, tattararrun tambayoyi ne daga cikin tambayoyi wadanda ake jin kunyar ...

SHIN GASKIYA NE ‘YAN SHI’A SUNA TUHUMAR UMMUL MUMININA A’ISHA DA AIKATA ZINA?

SHIN GASKIYA NE ‘YAN SHI’A SUNA TUHUMAR UMMUL MUMININA A’ISHA DA AIKATA ZINA? Daya daga cikin abinda makiya shia suka dau tsawon zamani suke yadawa na karya akan ‘yan shia domin kyamatar da al’uma da wannan mazhaba ta ‘ya’yan gidan Manzon tsira s.a.w.a shine cewa wai suna da kudurin dora wa Matar Manzo A’isha ‘yar khalifa Abubakar tuhumar aikata zina (wal’iyazu billah). Da alama wadanda suka tsara wannan qaryar basu san cewa wata rana duniya za ta iya kasancewa tamka gari guda ba ta tayanda babu abinda zai buya ga wani. Yanzu dai ga ‘yan shia ko ina ana tare da su, ga malaman su cikin sauki za’a iya tuntuban su sannan ga dubban litattafan su a kasuwa kowa na iya saye ya karanta, uwa uba kuma ga yanar gizo wanda cikin lokaci kankani mutum zai binciki irin littafin da kake bukata ya karanta. Wani abin mamaki shine sai ga ‘yan shia basu ma yarda da wannan tuhumar akan ita Ummul muminina A’isha ba balle kuma tabbatar da tukuhumar a kan ta. Za mu duba bayanan malaman shia game da wannan a...

AUREN MUTU'A TSAKANIN MUSULMI

AUREN MUTU'A TSAKANIN MUSULMI (1) Sheikh Sale Sani Zaria Idan mutum ya bibiyi abubuwan da ake fada da rubutawa a kan Auren Mutu’a a wannan zamani daga malaman Ahlus Sunna. A dukkanin abubuwan da ake fada akwai abubuwa masu jan hankali matuka wanda ake bukatar al'umar musulmi su fahimci hakikanin sa. Alhamdu lillahi dukda cewa su malaman suna kokarin fada da wannan ibada amma anyi dace suka yarda da halaccin Mutu ’ a da ayar AlKur ’ ani ta cikin Surar Nisa ’ i aya ta 24. A kan haka ne ma nake ganin cewa duk mai hankali zai yi mamakin yadda wasu malamai suke kwatatnta auren mutu ’ a da "dadiro" ko "kwanan gida". Idan har mutum ya yarda da cewa akwai ayar AlKur ’ ani wadda ta halatta Mutu’a ko da kuwa ya yarda da cewa an goge ta daga baya, to da wace irin mahanga kuma yake kwatanta shi da dadiro da kwanan-gida? Ina ayar da ta taba halatta dadiro da kwanan-gida a AlKur ’ ani har ya cancanci irin wannan kwatanci? Dadiro fa alfasha ne! Yanzu yana jin cewa ...