MENENE TAMBAYOYIN DA ‘YANMATA SUKE YI???
ماذا تسأ ل الفتيات؟
NA -1
DAGA
“CIBIYAR
NUUN”
MASU
WALLAFA DA TARJAMA
FASSARA:
MURTALA
ISAH DASS
MUKADDIMA
Akwai tambayoyi (masu yawa) da suke kekkewayawa a
cikin rai (kwakwalwar) ko wace budurwa, wadanda take bukatar amsar su, wani
lokaci takan koma wajen uwarta ko 'yar'uwarta ko kawarta ko kuma wajen malamarta
ta makaranta. Saidai wani lokaci bata gamsuwa da amsar da suke bata. Saboda
haka sai kaga son sanin wadannan abubuwan na tunkudata zuwa ga tambayoyi masu
dinbin yawa (alhali ta rasa mai bata gamsassun amsoshi)
Yawancin
uwaye kunya na lullubesu (suna jin kunya) game da amsa wasu sashen tambayoyi
masu tsarkakiya. (Sannan wani bangare kuma ita kanta budurwar ce take jin
kunyar yin tambayar alhali abin na damunta tana so ta sami bayani a kan su)
Wannan
littafi da ke gaba gareki ya ke 'yar'uwata abar girmamawa, tattararrun
tambayoyi ne daga cikin tambayoyi wadanda ake jin kunyar tambayarsu ko kuma in
an tambaya ake jin kunyar bada amsarsu.
Hakika
"Cibiyar Nuun" mai wallafe-wallafe da fassara, tare da taimakon wasu
sashen mata da suka dora
wa kansu aikin (taimakon Addinin) musulunci ta hanyar tafiya makarantun (koyar
da addinin) musulunci, da ma wasu
makarantun na daban wanda ba na musulunci ba. Sai suka samo (tattaro) wadannan
tambayoyi kai tsaye daga 'yanmata kuma dalibai wadanda shekarunsu ya kama daga
sha biyu har zuwa karshen matakin makarantar sakandare. Sai wannan cibiya (ta
"Nuun") ta kakkasa wadannan tambayoyiyi zuwa maudhu'o'i. Sannan ta
bar wasu tambyoyi masu maimaituwa wadanda suka taho ta yanayi mabanbanta, domin
samun gamammen amfanuwa. Kuma hakan
sakamakone na cewa wadansu 'yanmata sunyi kebantattun tambayoyi ne wadanda suka
saba da tambaya mai kama da su.
Sannan sai muka yi kokarin amsa su ta bangaren kwararru game da sanin
zamantakewar hadakar jama'a. Sannan a daya bangaren kuma sai daya daga cikin
manyan shehunan malaman mu na Hauzar ilimi ya kawo bayanin hukuncin shari'a
a bisa ko wace tambaya.
Daga karshe muna mika godiya ga dukkan wadanda ke da kaso na taimakawa
wajen fiddo da wannan littafi zuwa samuwar sa. Muna masu rokon Allah Mai tsarki
da daukaka da Ya karba musu wannan aiki da suka yi domin Sa. Kuma da fatar
wannan kokari ya amfanar da 'yanmatan mu da uwayen mu da malaman mu mata, domin
warware matsaloli masu yawa wadanda suke kunshe a kwakwalen su (wadanda suka
kasa samun amsoshin da zai warkar da su).
Sannan muna fata al'uma zasu kasance tare da mu wajen saduwa da mu ta
yanda idan akwai wasu tambayoyi wadanda (ke kwakwalen su amma) basu samesu ba a
cikin wannan littafi. Muna sanar da su cewa mun shirya tsaf domin amsa su a cikin
sabon bugu mai fitowa ko a littafi mai biye wa wannan, in Allah Madaukaki Ya
so.
Daga: “Cibiyar Nuun” domin wallafa da tarjama.
KASHI NA
FARKO
DORUWAR AYYUKAN SHARI'A (TAKLIFI) A WAJEN BUDURWA.
Tambaya ta 1-
Yaushe ne ya
wajaba a kan budurwa ta aikata wajiban shari'a?
Amsa:
Yana wajaba ne ga budurwa ta aikata wajibanta
na shari'a a yayin da ta isa wacce taklifi ya hau kanta a shara'ance. Kuma
wannan taklifi yana tabbata ne a kan ta a yayin da sharuda guda uku suka tabbatu
a kanta
Na farko; Balaga. Kuma shi
(balaga) yakan tabbata ne aka budurwa da cikan shekaru tara na watannin
kamariyya (kirgen watannin musulunci)
Na biyu: Hankali. Babu taklifi a kan mahaukaciya. Sannan hankali a nan
yana nufin ikon banbance abu maikyau da mummuna (kenan ko da yarinya ta kai
shekara tara amma tana da wauta ta yanda bata iya banbance abu maikyau da
mummuna to taklifi ba zai hau kan ta ba)
Na uku: Ikon aikata aiki. Bai wajaba ga budurwa ta aikata abinta take da
gajiyawa wajen aikatawa ba (kamar in ba zata iya daukar azumi ba)
Tambaya ta 2-
Shin ba za'a iya daukan dora taklifin
wajabcin aikata shari'a akan budurwa a wadannan shekaru (tara) al'amari ne
wanda ya fi karfin ikonta a bisa tsayuwa akan wadannan wajibai na ibada ba?
Amsa:
Lallai shari'ar
musulunci mai daraja tare da doruwar aikata hukun-hukunce (taklifi) a cikinta
ya tattaru ne tare da ikon budurwa a shekarunta na balaga. Koda yake budurwa
tana iya gazawa wani lokaci wajen iya gudanar da wasu sashen ayyukan ibada na
wajibi kamar azumi a bisa misali. A nan sai hukuncin wajabcin azumin ya sauka a
kan ta a watan ramadhana din, sai ta rama shi kafin wani watan ramadhana mai
zuwa (a lokacin ta kara girma da samun ikon iya yin azumin). Idan kuwa (duk da
hakan) ta gajiya (ta kasa aikatawa) to wajabcin yin azumin ya sauka a kan ta
gaba daya. Anan sai ta wadatu da biyan fansa, wanda shine ciyar da miskini guda
daya ko wace rana kilogram uku. Idan tayi hakan to babu wajabcin ramuwa a wasu
shekaru masu zuwa koda tana da ikon yin hakan.
Ya ke
'yar'uwa ta abin girmamawa, ya kamata ki
san cewa Allah Madaukakin sarki bai kallafa wani abu a kanki ba face kina da
ikon aikata shi. Sallah da azumi da
khumusi da hajji da sadaka da rikon amana da barin (haramta) yi da wani da
annamimanci da sata da makamantan su dukkansu abubuwa ne na al'ada ga ko wani
mukallifi (zai iya aikata wadanda ake bukatar ya aikata da barin wadanda aka
hana shi aikatawa). Idan kuwa gazawa ta
bijiro to babu wannan taklifi a kan sa.
Allah
Madaukakin sarki Ya fada "Allah baya kallafa wa wata rai bace
iyawarta" (Bakara, aya ta 286)
"Ba Mu
kallafa wa wata rai face iyawarta" (An'am,
aya ta 152)
Tambaya ta 3-
Me ya sa lokacin balaga ya kan
tabbata ga budurwa gabannin saurayi? Shin haka yana da alaka da doruwar ayyukan
shari'a?
Amsa:
Allah Mai
tsarki da daukaka Ya halicci na miji da mace,
kuma sai ya sanya kebantattun abubuwa da bambance-bambance a cikin
halittarsu ta jiki da rai. Ko wani dayansu na cike na dayansa. Bai sanya su
masu kama da juna ba, saboda kamanceceniyarsu zai kore (hana) cikar (gina) hadakar zamantakewa. Lokacin balaga a wajen
budurwa yakan rigayi lokacin balagar saurayi. Wannan yana faruwa ne sakamakon
abinda mace ta kebanta da shi wanda ba a samu a wajen saurayi. Saboda haka a
lokacin da ta kai shekarun balaga sai ta sami daukaka da dora mata hakkokin
shari'a (taklifi). To sai a wannan lokaci sai aikata ayyukanta na shari'a su
wajaba a kanta. Wannan kuma ba yana jayo mata tawaya bane, saidai ma balagar a
gareta daukaka ce da girmamawa.
'Yar'uwa ta abin
girmamawa, kada ki kwatanta lokacin
taklifin ki da na wani. Ke dai ki yi tunanin yanda zaki tabbatar da kamalarki
da samun kyakkyawar rayuwar lahira. Ki fadaka da cewa za a tashe ki (daga
kabari bayan mutuwar ki) ke kadai
ne, kuma hisabin ki ma ke kadai za'a
miki (game da abubuwan da kika aikata). Saboda haka ke dai ki yi kokarin
tsarkake ayyukan ki ga Allah Madaukaki. Ki yi aiki domim kubutar da kanki.
Allah Madaukaki Yana fada a cikin Suratul Zalzala "A ranar nan ne mutane
za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu"
Tambaya ta 4-
Wadansu suna daukar cewa dora nauyin
shari'a ga budurwa a wadannan shekaru yana nuna tamkar zaunci ne gare ta, wani
lokaci ma suna ganin cewa hakan tawaya ce gareta. Shin za ku iya bayyana mana
hakikanin yanayi ko matsayin wannan taklifi?
Amsa:
Allah
Madaukaki Ya halicci mutum sai Ya sanya masa ayyukan shari'a wanda wadannan
ka'idodi na shari'a suna kaiwan sa ne zuwa ga daukakar sa (kamalar sa) da samun
arzikin sa na lahira. Kuma wadannan shari'o'i suna kunshi wajibai da muharramai
(abubuwan da ya wajaba a aikata da kuma wadanda suke haramun ne aikata su).
Kuma dukkan ayyuka na wajibi akwai amfanuwar mukallifin a cikinsu, kuma dukkan
abinda aka haramta akwan barna ne gare shi. To a yayin da mutum ya zama balagagge,
mai hankal,i mai ikon aikatawa, sai ya zamo an kallafa masa wadannan ayyuka na
shari'a, amma ba wani abu bane mai nauyi wanda aka dora masa.
'Yar'uwata
abar girmamawa, ya kamata ki san cewa lallai Allah Mai girma da daukaka bai
wajabta wani abu a kan ki ba face akwai maslaha gareki, haka nan bai haramta
wani abu akan ki ba face akwai barna (matsala)
a cikinsa. To idan kika aikata wajibai kuma ki ka bar aikata
muharramai, a nan kin kasance mai
tabbatar da da amfani ga kanki ne, kuma kin nisantar da kan ka ga barna ne. To
kin ga haka kuwa alheri ne da daukaka (kika jawo wa kan ki). Hakan sam-sam ba
zalunci da tawaya ba ne. Ki kara fahimtar cewa shi taklifi (doruwan zartas da
shari'a akan mutum) daukaka ne da girmamawa. Saboda haka isar ki lokacin balaga
kafin na saurayi (namiji) wannan na nuni ne ga cewa ke kin shiga duniyar wadanda Allah Ya daukaka
su a gabannin sa. (Kenan hakan fifiko ne a kansa wanda ya kamata ki yi alfahari
da shi, amma ba daukar hakan a matsayin zalunci da tawaya ba)
Tambaya ta 5-
Don me Allah Madaukaki Ya sanya
bukata a cikin ran mu? Kuma don me wasu sashen wadannan bukata suna tahowa ne a
shekarun balaga?
Amsa:
Allah
madaukakin sarki Ya halicci mutum ne daga (bangarori biyu na) ruhi da jiki.
Sannan sai ya cusa wasu tarin lamura na neman biyan bukata. Wasu (bukatar)
sukan tunkuda mutun wajen cin abinci, ko shan abin sha, ko bukatuwar numfashi
da sauran bukatu. Kuma da wdannan al'amura ne kiyaye jiki yake samuwa. To amma
wasu bangaren bukatar sukan auku ne a lokacin da aka kai matakin balaga (a
yayin da mace za ta iya jin bukata ga namiji, haka shima na miji zai ji bukatar
mace). Manufar wannan bukata na lokacin balaga kuwa ci gaba ne na samar da
nau'in dan-adam, idan babu wannan bukata ba za'a sami aukuwar aure ba, idan
kuwa ba'a yin aure ba za'a sami haihuwa ba, kenan zai zamo babu ci gaban
samuwar mutum a bayan kasa, haka kuma zai haifar da yankewa zuriyar mutum.
Saboda haka sai ya zamo samuwar wannan bukata wajibi ne domin cigabantar da
samuwar mutane.
'Yar'uwata
abar girmamawa, ina miki horo da cewa ki bi hanyar gaskiya, ki yi mu'amala da
bukatar ki ta hanyar tsayuwa bisa iyakokin da shari'ar (addinin)musulunci ya
iyakance. Kada ki bi son rai da shedan. Domin bin son rai da batarwar shedan
yana bata budurwa, kamar yanda bacin budurwa
kaso ne na abinda ke bata hadakar zamantakewar al'uma. Kuma ranar tashin kiyama
yana zamowa azaba ne mai tsanani.
Tambaya ta 6-
Ban san menene alhakin da ya hau kaina
na shari'a ba a matakin balaga ta, kuma ina jin kunyar in yi tambaya a kan
haka. To mene ne ya hau kai na in yi?
Amsa:
Ya wajaba
akan ko wani mutumin da ya isa matakin taklifi ya nemi sanin wajibobin da ke
kan sa domin ya aikata su. Sannan haka ma ya nemi sanin abubuwan da suka
haramta a kansa domin ya bar su kuma ya nisance su. To a nan akwai hanyoyi masu
yawa wanda mukallifi zai bi wajen sanin abubuwan da suka doru a kansa na shari'a.
Daga cikin su akwai;
Ø Tambayar uwa
Ø Tambayar
kwararru wajen sha'anin tarbiyyar addini a makarantu
Ø Kwararru akan
halittar mata, da masu irshadi ga mata.
Ø Kuma zai iya
yiwuwa a tambayi malami masanin addini ko da ta hanyar tarho ne. Da makamantan
su.
Kuma ya
kamata dukkan jama'a su san cewa wasu sashen al'amuran addini ya kamata ga
mutum mumini ya yi tambaya game da alhakin da ya doru a kan sa game da su, ko
da kuwa tambayar za ta jawo jin kunya. Domin sanin hukunce-hukuncen shara'a
shine abu mafi muhimmanci daga komai a cikin rayuwar mu.
Wa
sallallaahu alaa Muhammad wa alaa aalihit taahiriin.
Kashi na biyu zai amsa tambayoyin da ya shafi
alaka tsakanin na miji da mace, ko alaka tsakanin saurayi da budurwa.
A biyo ni da izinin Allah.
Murtala Isah Dass
(8
RABI’US THANI, 1439 / 27 DECEMBER, 2017)
Domin neman Karin bayani/ Gyara ko
Kalu-bale, a tuntubeni ta daya daga cikin wadannan lambobi;
08133289306, 08058636125
& 07083030309.
Haka ma za a iya saduwa da ni ta
Whatsapp a wannan lambar; 08058636125
Ko a sadu da ni ta daya daga cikin
wadannan Adireshin Email:
Sannan ana iya samun wannan kasida da
wasu makamantan sa a wannan website na internet:
Comments
Post a Comment