Skip to main content

SHIN GASKIYA NE ‘YAN SHI’A SUNA TUHUMAR UMMUL MUMININA A’ISHA DA AIKATA ZINA?





SHIN GASKIYA NE ‘YAN SHI’A SUNA TUHUMAR UMMUL MUMININA A’ISHA DA AIKATA ZINA?

Daya daga cikin abinda makiya shia suka dau tsawon zamani suke yadawa na karya akan ‘yan shia domin kyamatar da al’uma da wannan mazhaba ta ‘ya’yan gidan Manzon tsira s.a.w.a shine cewa wai suna da kudurin dora wa Matar Manzo A’isha ‘yar khalifa Abubakar tuhumar aikata zina (wal’iyazu billah).

Da alama wadanda suka tsara wannan qaryar basu san cewa wata rana duniya za ta iya kasancewa tamka gari guda ba ta tayanda babu abinda zai buya ga wani. Yanzu dai ga ‘yan shia ko ina ana tare da su, ga malaman su cikin sauki za’a iya tuntuban su sannan ga dubban litattafan su a kasuwa kowa na iya saye ya karanta, uwa uba kuma ga yanar gizo wanda cikin lokaci kankani mutum zai binciki irin littafin da kake bukata ya karanta.

Wani abin mamaki shine sai ga ‘yan shia basu ma yarda da wannan tuhumar akan ita Ummul muminina A’isha ba balle kuma tabbatar da tukuhumar a kan ta.

Za mu duba bayanan malaman shia game da wannan al’amari, ba ma wanda ya shafi ita A’isha kadai ba amma aqidan shia yana nuna rashin yiwuwar aikata alfasha akan dukkan matan Annabawa Alaihimus Salam.



Babban malamin shian nan Shaikh Ad-Dusiy wanda ya rasu a shekara ta 460 bayab hijira, a cikin littafin sa na tafsirin Alkur’ani mai girma, mai suna “Tibyan fi tafsiril Kur’an” a yayain da yake fassarar aya ta 10 cikin suratut Tahrim, a inda Allah Ta’ala yake bada labarin matan Annabawan da suka ha’inci mazajen su, sune matar Annabi Nuhu a.s da matar Annabi Ludu a.s “Allah Ya buga wani misali ga wadanda suka kafirta, matar Nuhu da matar Ludu, sun kasance a karkashin bayin mu salihai, sai suka ha’ince su. Sai basu wadatar dasu komai ba daga (shiga azabar) Allah, kuma aka ce, ku shiga wuta tare da masu shiga.”

A yayin da yake fassara Kalmar “sai suka ha’ince su” sai ya rawaito hadisin Ibn Abbas r.a inda ya ce “matar Annabi Nuhu da Annabi Ludu munafukai ne, a wata ruwayar kafirai ne. Matar Nuhu ta kasance tana fada wa mutane cewa shi mahaukaci ne. matar Ludu kuwa ta kasance tana bada labarin bakin sa (domin su auka musu su yi luwadi da su). To yin hakan kuwa ha’intar Annabawan ne, amma babu wata matar Annabi da ta taba yin zina ko taki, saboda abinda yake cikin hakan na nisantar da mutane daga Manzon da kyamar sa.”

Bayan naqalto wannan hadisi na Ibn Abbas sai shi kuma Shaikhud Dusi din ya ce “duk wanda ya jingina aikata Zina ga daya daga cikin matan Annabi s.a.w.a, to hakika ya yi kuskure, kuskure mai girma, wannan Magana ne wanda ba zai karbu ba.”

Haka nan ya zo a cikin littafi mai suna “Tanzihul Anbiya” na babban malamin shi’a “Alamul Huda Abil Qasim” wanda aka fi sanin sa “Sharif Al-Murtadha” . bayan ya naqalto wasu ra’ayoyi na wasu sashen malaman tafsiri wadanda suke nuna ma’anar ha’inci a wancan ayar itace ha’inci da ya shafi aikata alfasha (wal’iyazu billah), Sai yake cewa “ai su Annabawa tsira da amincin Allah su tabbata a gare su ya wajaba su zama an tsarkake su daga wannan hali, ma’ana ya zamo an kiyaye mutuncin su ta yanda wani zai iya keta mutuncin su, ta yanda matan su za su iya abkawa cikin aikata alfasha, saboda hakan zai zamanto tsiraici ne da walakantarwa gare su, haka kuma zai zamo tawaya ce ga kimar su. Hakika Allah madaukaki ya nisantar das u akan abinda baikai haka muni ba ma, to yaya game da wannan al’amari (mai girma na walakanci)? Kuma hakika Allah Madaukaki ya nisantar da su daga wannan ne domin girmamawa da daukakakawa gare su, kuma da kore duk wani aibi da zai haifar da rashin karbuwa gare su. Hakika yanda ya bayyana a cikin hadisin da Ibn Abbas ya rawaito na nuni akan cewa ha’incin da ake nufi sam ba zina bane ….”



Allama Majlisi a cikin littafin hadisin sa “Biharul Anwar” bayan ya naqalto maganganu da wasu sashen masu tafsiri, ko kuma abinda ya zo cikin wasu litattafan tafsiri na shia wadanda suke ishsra da cewa ha’incin matan wadancan Annabawa ya hada da alfashan zina, sai yake cewa “a cikin wannan akwai abin firgitarwa, bakon al’amari ne mai ban mamaki wanda muke nisantar da samuwar asalin wannan maganar daga misalin mutum (mai daraja) irin Shaihin mu Aliyu bin Ibrahim (sakamakon an rawaito irin wannan maganmar a cikin wannan tafsiri wanda yake nuna cewa ha’incin da wadannan matan annabawan suka yi ya hada hard a aikata alfasha). Sai yaci gaba da cewa “Domin shi wannan tafsiri wanda ake kira tafsirul Qummi, ba dukkan abinda ke ciki bane daga gare shi (Shaikh Aliyu bin Ibrahim Al-qummi) Allah Ya tsarkake ruhin sa, face a ciki akwai kare-kare masu yawa daga wasun sa, musamman irin wannan Magana (na jingina zina zuwa ga matan Annabawa ko zuwa ga wani sashe na matan Annabi s.a.w.a) wanda gaba daya musulmi sun tafi akan sabanin sa, daga kebantattu ko gungun su, dukkanin su (musulmi) suna ikirari da tsarkin suturan matan Annabi s.a.w.a.

Hakannan Shaikh Ad-Dabrasy a cikin littafin sa na tafsiri “Majma’ul Bayan” a karkashin tafsirin wannan ayar ta 10 dake cikin Suratut Tahrim shima ya hakaito wancan hadisi na Ibn Abbas ne a matsayin fassarar wannan ayar …. Saboda haka babu matar wani annabi da ta taba aikata zina.

Malamin Ahlus sunnan Allama Alusi ma’abucin litattafin tafsirin mai suna “Ruhul Ma’ani” Ya qaryata wadanda suke jifan ‘yan shia da cewa suna da i’itiqadin cewa A’isha ta aikata zina, da cewa zance ne mara inganci, a inda yake cewa “abinda ya watsu ko ake jingina wa shia, magana ne wanda ya wofanta daga sahihanci, sun kasance suna ikirari da tsarkin suturar matan Annabi s.a.w.a sabanin abinda aka ambata. Na’am wasun su sun yi ikirari da sabon wani sashin su (A’isha) game da bijire wa shugaban muminai Ali a.s (da ma yakar sa)



Wadannan sune kadan daga cikin zantuttukan malaman shia, ba kawai wannan ya takaita ga Manzon tsira s.a.w.a kadai ba, a’a wannan ma zance suke yi game da sauran Annabawa alaihimus salam. Wannan wani abu ne wanda kai tsaye zai shafi mutuncin Annabawan ya kuma zame tawaya a gare su. To ina kuma ga Manzo mafi girma da karimci kuma shugaban su da halittu gaba daya? Yaya za a yi ace Allah Madaukaki ba zai tsarkake diyaucin matan sa ya kiyayae mutuncin su ba daga wannan alfasha na zina?

Wadannan Annabawa fa Allah Ta’ala ya aiko su ne domin su zamo abin koyi ga sauran halitta, shi ya sa ma ya sanya su ma’asumai kai tsaye domin dukkan abinda suka aikata ya zamo yankakkiyar hujja. To yaya za ayi wadanda ake bukatar su zamo abin koyi ga al’uma su zamo masu tawaya wajen barin tsare mutuncin su cikin lamarin matan su? Wannan wani abu ne wanda ya saba wa hankali a matakin farko kafin shara’a a mataki na biyu, balle kuma matan Manzon karshen zamani wanda aka turo shi ga al’uma gaba daya daga lokacin bayyanar sa abin koyi ne ga al’uma har zuwa ranar tashin kiyama.

Saboda haka wannan tuhuma da aka jingina ga mabiya tafarkin shi’a abu ne mara tushe, an yi shi ne domin kange al’uma daga kusantar mabiya wannan tafarki domin hana fahimtar su.


RUWAYAR TUHUMAR UMMUL MUMININA A’ISHA DA AIKATA ZINA KIRKIRAR MAKIYA NE DON CIN MUTUNTUNCIN MANZO ALLAH.

Bayan bayanin da na gabatar game tunkude tuhumar Ummul muminina A’isha da ake jingina wa ‘yan shi’a. A yayin da na naqalto maganganun manyan malaman shi’a wanda ke nuna cewa gaba daya ma aqidar shi’a ta ginu ne bisa cewa bazai yiwu matar wani Annabi daga cikin Annabawan Allah Alaihimus salam ta aikata zina ba, domin tsare mutuncin Annabawan da kuma karesu daga tawaya. To wannan karo zamu dubi yanda ‘yan shi’a suke ganin wannan ruwaya da ta taho cikin Sahihul Bukhari da wasu bangarorin sa a wasu litattafan ruwayoyi na Ahlus sunna wanda kuma aka jingina labarin ga ita A’isha. Lakaba wa ‘yan shia tuhumar Matan Manzon Allah A’isha da aikata zina Magana ne mara tushe saboda ‘yan shia basu ma yarda cewa wacce ake tuhuma da aikata zina daga cikin matan Manzo s.a.w.a kuma Allah Ya saukar da ayoyin wanke ta da kuma tsawatar da wadanda suka yi wannan aika-aika da ma wadanda suka yarda da hakan cewa ita ce A’isha ba, kamar yanda na bayyana a baya.

Ruwaya ta zo a cikin Sahihul Bukhari a cikin “Kitabul Magazi, babin Hadisul ifki. Wannan ruwayar ta taho da abubuwan mamaki wanda kacokam sun yi hannun riga da karantarwar Alkur’ani wadda ke bayyana mana wanene Manzon Allah (sawa) a matsayinsa na ma’asumi shugaban ma’asumai, 'dan Adam mafi kamala kuma mafi kyawawan halaye a cikin halitta. Idan akayi dubi da idon basira za’a tarar wannan labari yana suka ga Manzon Allah shi kansa da kuma wasu sahabbai na gari, a tanan za’a iya sunsunar cewa wannan aiki ne irin na banu Umayya da suka saba yi na ganin sun kaskantar da darajar Annabin tsira (sawa) sun nuna tamkar sauran mutane gama gari yake ta yanda zai iya abkawa cikin rudu da rashin tabbas a cikin lamuran sa.

Daga cikin abinda wannan labari yake nunawa shine cewa shi kansa Manzon Allah (sawa) yana zargi da shakka game da lamarin, a yanda yake ganin hakan abu mai iya abkuwa, saboda har takai ga yana tambayar ta cewa idan ta san bata aikata wannan abinda ake tuhumarta dashi ba to da sannu Allah Zai barrantar da ita, in ko ta aikata to ta yi istigfari kuma ta tuba zuwa ga Allah, domin idan bawa ya yi i’itirafi game da zunubinsa sannan ya tuba to Allah zai karbi tubansa. A wani ruwayar ma yana cewa ai ke ‘yar adam ce wacce za ki iya yin kuskure.

A wannan labari an nuna cewa Manzon Allah ya rika nuna wasu halayya na gujewa da nuna yatsan zargi ga A’isha tun lokacin da aka bashi labarin wannan tuhuma, kuma ta fahimci hakan sosai hart a kai ga bayan saukan ayar da ta tsarkake ta daga wannan zargi ya kuma bayan ya mata albishir sai tace ta gode wa Allah da ya tsarkake ta amma ba zata gode wa kowa ba har shi Manzon (sakamakon yana cikin wanda suka amince da cewar zata iya aikata wannan abu na alfasha). Har abin yakai matsayin lokacin da ayar ta sauka sai babarta tace mata ki tashi ki je wajensa (Manzon Allah s.a.w.a), sai tace mata wallahi ni ba zan je wajen sa ba (saboda bacin ran da take dashi game da shi na nuna cewa za ta iya aikata abinda ake zarginta a wannan kazafi da aka yi mata)

Bayan haka wanna labari yayi ta nuna yatsa akan Imamu Ali a.s da irin su Hassan bin Sabit a matsayin wadanda suma suka yarda da wannan qazafi akan Aisha har Hassan din yana cikin wadanda suka rika yayatawa.

Anan zamu iya fahimtar cewa wannan labari ba komai bane illa zuki ta malli wanda aka shirya domin kaskantar da darajar Manzo da wadanda ake hamayya da su tare da shi. Domin kuwa yaya za ayi ace Manzon yana cikin wadanda za su iya ganin yiwuwar faruwan hakan alhali yasan cewa Allah Ya katange matan Annabawa daga wani ya keta hurumin su? Sannan Idan muka yi la’akari da yanda ayan Alkur’ani mai girma ya tsawatar wa sahabban da suka amince da wannan lamari a suratun Nur dun daga aya aya na 12 zuwa na 16 “Don me a lokacin da kuka ji shi (wannan labari) muminai maza da muminai mata ba su yi zaton alheri game da kansu ba kuma su ce wannan kiren karya ne bayyananne?. Don me basu zo da shaidu hudu akan sa ba? to idan basu kawo shaidun ba, to wadannan a wurin Allah sune makaryata. Kuma ba domin falalar Allah akan ku da rahamarsa a cikin duniya da lahira ba, da azaba mai girma girma ta shafeku a cikin abinda kuka nutsa da zancesa. A yayin da kuke karbarsa da harsunanku, kuma kuna fada da bakunanku abinda baku da wani ilimi a game das hi, kuma kuna zatonsa (wannan al’amari na tuhumar matan Manzon Allah da aikata alfasha al’amari) mai sauki ne, alhali kuwa a wajen Allah abu ne mai girma.”

Kenan mumini ma abinda ke zama wajibi a kansa shine rashin halarto da yarda da wannan kazafi a cikin kwakwalwarsa, don hakan babban laifi ne, to ina kuma ga shia Mnazon kansa?

Mu’assasin akidar wahabiyanci “Ibn Taimiyya” wanda mabiyansa suke masa lakabi da “Shaikhul Islam” ya bayyana a cikin littafin “Minhajus Sunnah fi nakdhi kalamish shi’a”, juzu’i na 4 shafi na 110. Yana cewa “ya zo cikin sahihai biyu (Bukhari da Muslim) cewa kafin Allah Madaukaki Ya saukar da ayan da ya kubutar da A’isha, to manzon Allah s.a.w.a bai san kubutarta game da tuhumar aikata zina ba, ya kasance yana mai zargi game da al’amarinta.

Albani ya bayyana a cikin littafinsa “Silsilstul hadisis sahiha” a juzu’i na 6 kashi na farko, a karkashin hadisi 2507. Yana cewa “…. Saboda haka matsayin Annabi s.a.w.a a cikin wannan kissa shine matsayin mai dako da jiran saukan wahayi wanda zai yanke shakka game da wannan labari da aka bashi, kamar yanda hakan yake bayyana a hadisin inda shi Annabin yake ce (wa A’isha) ke ai kina cikin ‘yan’adam ne (saboda haka zaki iya yin kuskure). Kuma tabbas wannan zance haka ya zo a cikin Bukhari wai Annabi ya gaya wa A’isha cewa “labari ya iso gare ni cewa kin aikata kaza da kaza kuma ke ba kowa bace face ‘yar’adam (wanda hakan na iya faruwa da ke)”

Ya zo a cin littafin “fatawal lajanatid da’imati lilbuhusil ilmiyyati wal’ifta’i” wanda Ahmad ad-dawush ya harhada na fatawoyin malaman sunnah musamman na wahabiyawa. A juzu’i na 4 fatawar tambaya ta 9811; shin Manzo ya san kubutar A’isha (cewa bata aikata abinda ake tuhumarta na zina ba) kafin saukan wahayi? Amsa; Annabi s.a.w.a bai san kubutar A’isha daga aikata wannan laifi ba kafin saukan wahayi a gareshi, da kuwa yasan kubutarta da bai rikice da rashin samun tabbas cikin lamarinta ba (a lokacin da aka bashi labari).

Wadannan maganganu ba komai suke nunawa ba face kaskantar da matsayin Annabi s.a.w.a, a yayin da ‘yan shi’a kuwa suke ganin abune wanda bazai taba yiwuwa ba ace Manzon Allah yana shakka ko zargin wata matarsa da aikata alfasha. Manzon Allah s.a.w.a yana da yakinin cewa bazai taba yiwuwa ace daya daga cikin matansa ta aikata alfasha ba, saboda haka ko misalin kwayan zarra a bazai taba yiwuwa ya halarto da shakka ko zargi ba.

Comments

Popular posts from this blog

MENENE TAMBAYOYIN DA ‘YANMATA SUKE YI??? NA 1

MENENE TAMBAYOYIN DA ‘YANMATA SUKE YI??? ماذا تسأ ل الفتيات؟ NA   - 1 DAGA “CIBIYAR NUUN” MASU WALLAFA DA TARJAMA FASSARA: MURTALA ISAH DASS MUKADDIMA A kwai tambayoyi (masu yawa) da suke kekkewayawa a cikin rai (kwakwalwar) ko wace budurwa, wadanda take bukatar amsar su, wani lokaci takan koma wajen uwarta ko 'yar'uwarta ko kawarta ko kuma wajen malamarta ta makaranta. Saidai wani lokaci bata gamsuwa da amsar da suke bata. Saboda haka sai kaga son sanin wadannan abubuwan na tunkudata zuwa ga tambayoyi masu dinbin yawa (alhali ta rasa mai bata gamsassun amsoshi) Yawancin uwaye kunya na lullubesu (suna jin kunya) game da amsa wasu sashen tambayoyi masu tsarkakiya. (Sannan wani bangare kuma ita kanta budurwar ce take jin kunyar yin tambayar alhali abin na damunta tana so ta sami bayani a kan su) Wannan littafi da ke gaba gareki ya ke 'yar'uwata abar girmamawa, tattararrun tambayoyi ne daga cikin tambayoyi wadanda ake jin kunyar ...

AUREN MUTU'A TSAKANIN MUSULMI

AUREN MUTU'A TSAKANIN MUSULMI (1) Sheikh Sale Sani Zaria Idan mutum ya bibiyi abubuwan da ake fada da rubutawa a kan Auren Mutu’a a wannan zamani daga malaman Ahlus Sunna. A dukkanin abubuwan da ake fada akwai abubuwa masu jan hankali matuka wanda ake bukatar al'umar musulmi su fahimci hakikanin sa. Alhamdu lillahi dukda cewa su malaman suna kokarin fada da wannan ibada amma anyi dace suka yarda da halaccin Mutu ’ a da ayar AlKur ’ ani ta cikin Surar Nisa ’ i aya ta 24. A kan haka ne ma nake ganin cewa duk mai hankali zai yi mamakin yadda wasu malamai suke kwatatnta auren mutu ’ a da "dadiro" ko "kwanan gida". Idan har mutum ya yarda da cewa akwai ayar AlKur ’ ani wadda ta halatta Mutu’a ko da kuwa ya yarda da cewa an goge ta daga baya, to da wace irin mahanga kuma yake kwatanta shi da dadiro da kwanan-gida? Ina ayar da ta taba halatta dadiro da kwanan-gida a AlKur ’ ani har ya cancanci irin wannan kwatanci? Dadiro fa alfasha ne! Yanzu yana jin cewa ...