MENENE TAMBAYOYIN DA ‘YANMATA SUKE YI??? ماذا تسأ ل الفتيات؟ NA - 1 DAGA “CIBIYAR NUUN” MASU WALLAFA DA TARJAMA FASSARA: MURTALA ISAH DASS MUKADDIMA A kwai tambayoyi (masu yawa) da suke kekkewayawa a cikin rai (kwakwalwar) ko wace budurwa, wadanda take bukatar amsar su, wani lokaci takan koma wajen uwarta ko 'yar'uwarta ko kawarta ko kuma wajen malamarta ta makaranta. Saidai wani lokaci bata gamsuwa da amsar da suke bata. Saboda haka sai kaga son sanin wadannan abubuwan na tunkudata zuwa ga tambayoyi masu dinbin yawa (alhali ta rasa mai bata gamsassun amsoshi) Yawancin uwaye kunya na lullubesu (suna jin kunya) game da amsa wasu sashen tambayoyi masu tsarkakiya. (Sannan wani bangare kuma ita kanta budurwar ce take jin kunyar yin tambayar alhali abin na damunta tana so ta sami bayani a kan su) Wannan littafi da ke gaba gareki ya ke 'yar'uwata abar girmamawa, tattararrun tambayoyi ne daga cikin tambayoyi wadanda ake jin kunyar ...
AN BUDE WANNAN SHAFI NE DON BAYYANA HUJJOJIN DA SH'ANCI YA GINU AKAI NA AQIDA DA FIQHU DA SAURAN AL'AMURA, SANNAN DA TUNKUDE SHUBUHOHI DA QARAIRAYIN DA AKE JINGINA WA AQIDAR DAGA BANGARE MAKIYANSA.