AUREN
MUTU'A TSAKANIN
MUSULMI
(1)
Sheikh Sale Sani Zaria
Idan mutum ya bibiyi abubuwan da ake
fada da rubutawa a kan Auren Mutu’a a wannan zamani daga malaman Ahlus Sunna. A
dukkanin abubuwan da ake fada akwai abubuwa masu jan hankali matuka wanda ake
bukatar al'umar musulmi su fahimci hakikanin sa. Alhamdu lillahi dukda cewa su
malaman suna kokarin fada da wannan ibada amma anyi dace suka yarda da halaccin
Mutu’a da ayar AlKur’ani ta cikin Surar Nisa’i aya ta 24. A kan haka ne ma nake ganin cewa duk mai hankali zai yi mamakin yadda wasu
malamai suke kwatatnta auren mutu’a da
"dadiro" ko "kwanan gida". Idan har mutum ya yarda da cewa akwai
ayar AlKur’ani wadda ta halatta Mutu’a ko da kuwa
ya yarda da cewa an goge ta daga baya, to da wace irin mahanga kuma yake
kwatanta shi da dadiro da kwanan-gida? Ina ayar da ta taba halatta dadiro da
kwanan-gida a AlKur’ani har ya
cancanci irin wannan kwatanci? Dadiro fa alfasha ne! Yanzu yana jin cewa akwai
inda Allah Ya taba horo da aikata alfasha sannan daga baya ya hana? Kuma yana jin
cewa Sahabban da suka aikata mutu’a (koda kuwa a farkon halatta shi din ne) sun
aikata alfasha kenan? Yaya matsayin Sahabban da suka saura da fahimtar rashin
goge mutu’a ba wani bambanci tsakanin “fitatu” ko “masu gafaka” da wasunsu. Yana jin irin wadannan sun yarda kuma suna-
aikata alfasha kenan? Misalta haka da matakan haramta giya kuskure ne, saboda
Musulunci ba shi ya halatta giya a matakin farko ba, alhali mutu’a Musulunci ne ya kirkire shi tun asali. Ko ta halin
kaka dai lamarin ba yadda irin wadannan malamai suke dauka ba ne. Tun
lokacin Sahabbai akwai sabanin ra’ayi a kan
wanzuwar hukuncin auren mutu’a, sai dai na
su ba irin sabanin da ya biyo bayan yaduwar kirkirun hadisan karya ba ne. A
wancan lokacin sabanin kan ko Khalifa na da hakkin haramta hukuncin Allah da ManzonSa
bisa kowane irin dalili ne kuwa, ko ba
shi da wannan hakkin? A nan ina cewa ne hadisan da ake ambata a yau wadanda
suke dangana haramta mutu’a ga Manzo
[SAWA] kirkirarru ne kuma Sahabbai ba su san su ba. Insha’Allah zan tabbatar da haka a binciken da zai zo kan
wadannan hadisai a nan gaba cikin wannan kasida insha Allah.
Kamar yadda na fada, sabani ya gudana ne
tsakanin malaman Musulmi (ba kawai tsakanin ’yan Shi’a da
Ahlusunna kamar yadda wasu suke dauka dangane da goge shi da abin da ya goge shi
da lokacin da aka goge shi.
To a yanzu zan fara ne da gabatar da hujjojin masu
haramta Auren Mutu'a.
Zan fara ne da masu kafa hujja da wasu ayoyin da suke
riyawa cewa sun shafe ayar Auren Mutu'a
Fadar Goge Auren Mutu’a Da AlKur’ani
Wasu daga malaman Ahlussunna da fakihansu sun tafi a kan cewa AlKur’ani ne ya haramta mutu’a kafin komai. Daga ayoyin da suke kawowa a kan haka akwai fadar Allah cewa:“Kuma su ne wadanda suke kare al’aurarsu (daga aikata sabo); sai ga matayensu ko kuyangin da suka mallaka, to lallai su (a kan wannan) ba ababen zargi ba ne. To duk wanda ya nemi wanin wannan to wadannan su ne masu ketare iyaka ” (al- Mu’uminun: 5-7);
Bisa la’akari da cewa auren mutu’a ba aure ba ne, kuma matar da aka yi
Wasu daga malaman Ahlussunna da fakihansu sun tafi a kan cewa AlKur’ani ne ya haramta mutu’a kafin komai. Daga ayoyin da suke kawowa a kan haka akwai fadar Allah cewa:“Kuma su ne wadanda suke kare al’aurarsu (daga aikata sabo); sai ga matayensu ko kuyangin da suka mallaka, to lallai su (a kan wannan) ba ababen zargi ba ne. To duk wanda ya nemi wanin wannan to wadannan su ne masu ketare iyaka ” (al- Mu’uminun: 5-7);
Bisa la’akari da cewa auren mutu’a ba aure ba ne, kuma matar da aka yi
auren da ita ba matar aure ba
ce, ga shi kuma da ma ba
kuyanga ba ce.
Aya ta biyu da suke kafa hujja da ita ita ce ayar Saki dake cewa: “Ya kai
Aya ta biyu da suke kafa hujja da ita ita ce ayar Saki dake cewa: “Ya kai
wannan Annabi, idan za ku
saki mata ku sake su ga
iddarsu” (al-Talak:
1).
Sai kuma aya ta uku wadda ita ce
Sai kuma aya ta uku wadda ita ce
ayar gado tsakanin ma’aurata
dake cewa: “Kuna da
(gadon)
rabin abin da matanku suka
bari idan ba su da da… ” (al-
Nisa’i: 12).
A kan haka na ke cewa:
1- Duk an dace a kan cewa
Surar Mu’uminun (wadda
ayar
da suke da’awar an goge
mutu’a da ita) a
Makka aka
saukar da ita, alhali Nisa’i
(wadda ayar halaccin mutu’a
ta zo a cikin ta) a Madina ta
sauka, ta ina saukakkiyar
Makka ke iya goge saukakkiyar
Madina? Da wannan ba zai
yiwu wannan aya ta goge
mutu’a ba. Haka
wannan ya
raunana abin da masu
haramtawa ke doruwa a kai na
cewa halattawarta a farkon
Musulunci ne, wanda a
rayuwar Makka kenan. A duk
surorin nan biyu kuwa babu
wani dalili daga dukkan
bangarorin biyu da ya toge
ayar mutu’a da cewa a
Makka
ta sauka.
2- Mutu’an da muke
zance a
kansa AURE ne; don haka
matar da aka yi da ita MATAR
AURE ce; saboda tun da har
AlKur’ani ya zo da
shi da sigar
yarjejniya tsakanin mata da
miji, ya shiga cikin tsaikon
aure kenan. Da wannan za mu
iya kasa auren Musulunci zuwa
kashi biyu: auren dindindin da
auren mutu’a; a dabi’ance zai
zama suna da wuraren da
suka daidaita da inda suka
saba da juna.
3- Duk malaman da suka
halatta Mutu’a sun wajabta
idda ga matar da aka yi auren
da ita a duk lokacin da auren
ya kare. Iddarta kwana arba’in
da biyar ne da ittifakin
malaman Shi’a (zancen da
wasu ke dangana musu na
cewa ba sa wajabta idda a kan
auren mutu’a tsabagen
kage
ne da shaidar zur). Wannan ya
bayyana kuskuren tunanin cewa wani na iya
“auren mutu’a da wata (mace)
na awa biyu misali, kuma
tsawon rayuwar auren ya
kare; wani ya ya aura na
tsawon kwana biyu shi ma ya
kare; wani ya aura na kwana
biyar…” a ina masu fadar hakan suka ga wannan?
Mafi karancin muddar dake
tsakanin karewar auren
mutu’a da wani
sabo shi ne
kwana 45. Ya kamata a rika
neman sani kafin ayi magana!
4- Idan kuwa don ba saki a
cikinsa ne, to ai saki ba
manufar aure ba ne, shi
hanyar magance matsaloli ne
a lokacin da abubuwa suka
rincabe suka kai haddin rashin
wani magani idan ba sakin ba;
don haka ne ma Manzo
[SAWA] ya siffanta saki da
“halal din da Allah ke fushi da
shi.” Kara da cewa
masu
halatta mutu’a sun halatta
miji ya yafe abin da ya saura
na muddar auren saboda
kowane irin dalili ne kuwa,
wanda hakan ke matsayin
hanyar samar da mafita irin
na saki.
5-Fadar cewa an haramta
mutu’a ne da ayar
gado
tsakanin ma’aurata, bisa
la’akari da cewa
ba a wajabta
gado tsakanin ma’aurata a
auren mutu’a ba, wannan
ba
kakkarfan dalili ba ne; saboda
babu abin da ke lizimta wa
hatta dauwamammen aure
gadon ma’aurata; bisa
la’akari
da cewa akwai halayen da
shari’a ta yanke
igiyar gado
tsakanin ma’aurata, kamar
a
lokacin da kafirci ya gindaya
(saboda kafiri ba ya gadon
Musulmi); ko kisa ya shigo
(saboda wanda ya yi kisa ba ya
gadon wanda ya kashe). Da
wannan za mu iya fahimtar
cewa gado wani tanaji ne na
dabam daga aure, illa dai shi
aure (na dindindin) daya ne
daga sabubban gado; iyakarta
kenan.
6-Dukkanin wadancan ayoyi ba
su fito barobaro sun haramta
auren mutu’a kamar yadda
ayar da ta halatta shi ta fito
da halattawan ba; domin kuwa
ayar da ta halatta cewa ta yi:
“Abin da kuka yi mutu’a da
su a kan shi, to ku ba su
ladaddakinsu (wannan)
farilla ne ” (Nisa’i: 24). Ga shi
kuwa Allah Yana fadar yadda
Yake goge wata aya da wata
da cewa: “Idan muka
shafe
wata aya ko muka manta
da ita (wato muka kau da
kai daga gare ta) mukan zo
da wadda ta fita ko kamar
ta” (Baqara:
105). Idan za mu
yi amfani da yadda muka saba
fahimtar AlKur’ani a nan, ya
kamata mu fahimci cewa
ayoyin da ake da’awar goge
mutu’a da su ba su
fito da
haramta shi daidai da yadda
ayar dake halattawa ta fito da
bayanin halattawan filla filla
ba. Kuma ba su zo da wani
hukunci day a musanya
mutu’a ba (bisa la’akari da
cewa da ma can akwai tsarin
dauwamammen aure kafin a
halatta mutu’a). Wannan ya
saba da waccan ka’ida ta “goge
aya da wadda ta fi ta ko irin
ta.”
Wadannan dalilai shida kawai
sun isa su sa dole mu ki yarda
da goge mutu’a da wata aya
daga AlKur’ani.
AUREN MUTU'A TSAKANIN
MUSULMI (2)
Fadar Goge Auren Mutu’a
Da Hadisai.
Wannan ya kawo mu nazari a
kan da’awar goge
mutu’a da
ruwayoyi, wanda shi ne mafi
karfin madogaran masu
haramtawan. Ruwayoyin
haramta mutu’a sun kasu
kashi biyu kamar haka:
Kashi Na Daya: Su ne
ruwayoyin dake dangana
gogewan ga Manzo (SAWA).
Irin wadannan hadisai an
dangana ruwayarsu ga mutane
uku:
a) Imam Ali bin Abi Talib: a
hadisin Abubakr bin Abi
Shaiba, wanda isnadinsa ya
hadu da Sufyan bin Uyaina
daga Zuhri, ya kare da Ali
[AS] ta hanyar dansa
Muhammad (binl-Hanafiyya),
wanda kuma yake cewa (wai
Ali) ya ce: “Lallai Manzo
(SAWA) ya hana auren mutu’a
a lokacin (yakin) Khaibara
kuma ya hana cin naman
jakunan gida.” Wannan ya
maimaitu da lafuzza
makusanta a kusan duk
littafan hadisai na Ahlussunna.
Wannan hadisi ba ya iya zama
hujja a kan goge mutu’a
saboda dalilai ma su zuwa:
1. Yana da babbar matsala a
isnadinsa, saboda a ciki jerin
wadanda suka ruwaito shi
akwai Sufyan bin Uyaina,
wanda shi Sufyan sananne ne
datadlisi a hadisai (wato boye
aibobin da ke tattare da
hadisi ko sanadinsa). Wannan
shi ne abin da Zahabi ya
tabbatar a cikin littafinsa
Mizanul-l’itidal
(2/170), har
ma ya kara da cewa shi Sufyan
bin Uyaina “ya kware da
irin
wannan aiki na tadlisi, kuma
ba ya yin haka sai ta hanyar
jingina wa mutanen da aka
yarda da su.” Dacewan
malaman hadisi ne kuwa cewa
tadlisi na daga mafi girman
abubuwan dake raunana
hadisi; don haka irin hadisin
dake da wannan illa ba zai
taba goge hukuncin AlKur’ani
ba.
2. Yayi karo da abin da ya
shahara daga Imam Ali [AS]
na nacewarsa a kan halaccin
auren mutu’a; ta yadda
har
maganarsa mai cewa: “Ba don
cewa Umar ya hana auren
mutu’a ba da babu
wanda zai
yi zina sai tababbe” ya zama
ruwan-dare a tasakanin masu
nazari a kan lamarin mutu’a.
Don kore wa masu sukar Mutu'a
shakka nake cewa a duba
wannan zance na Imam Ali
[AS] a tafsirin Tabari (5/13);
da Tafsirul Kabir na
Fakhruddin al-Razi (10/50); da
tafsirin Durrul Manthur na
Suyuti (2/140); da tafsirin
Kurtubi (5/130) da wasu
littafan hadisi irin su Nailul-
Autar na Shaukani
(3/250-251) da Subulul-Salam
(sharhin Bulugul-Maram) na
San’ani (3/967).
b) Sai ruwayar da ta zo ta
hanyar Sabra bin Ma’abad al-
Juhaniy: Shi ne hadisin Abdul-
Malik bin Rabi’ bin Sabra da
ke cewa: “Manzon Allah
[SAWA) ya umarce mu da yin
mutu’a a shekarar
da aka
bude Makka yayin da muka
shiga birnin Makka, amma ba
mu fice daga cikinta ba har
sai da ya hana mu yin auren
na mutu’a.” Wannan hadisi ya
maiamaita da lafuzza
makusanta ta yadda har ya
wuce wanda ya gabace shi. Sai
dai shi ma kamar wanda ya
gabace shi ne, ba shi da
kwarin da zai iya goge ayar
AlKur’ani saboda
dalilai masu
zuwa:
1. Duk da yawan hanyoyinsa
sai dai duk sun kare ne da
Sabra daga babansa. Wannan
ya sa hadisin ya zama cikin
hadisan al-Aahad (wato hadisin
da ya fito ta hanyar mutum
daya) wanda malamai suka
dace a kan cewa ba ya goge
aya. Kara da cewa a daya daga
cikin ruwayoyin na Sabra an ce
huduba Manzo [SAWA] ya yi
ga jama’a a tsakanin
Ka’aba da
Makamu Ibrahim; amma duk
da haka babu wanda ya
ruwaito wannan huduba sai
Sabra shi kadai!
2. Sabra ya ruwaito shi ne
daga babansa Rabi’u, wanda
masana masu ruwayar hadisi
suka kusan dacewa a kan cewa
majhuli ne (wato ba a ma san
shi ba). Wannan ma aibi ne
dake raunana hadisi.
3. Ruwayoyin Sabra
din suna karo da juna wajen
fayyace lokacin da haramtawan
ya faru; wasu daga cikin su
sun ce ranar bude Makka,
wasu suka ce a hajjin ban-
kwana. Kara da cewa ya yi
karo da hadisin da a kan
dangana wa Ali, wanda zance
a kansa ya gabata; saboda a
can an dangana haramtawan
ne da lokacin yakin Khaibara.
Wannan duk da cewa wasu
masu sharhin hadisan, irin su
Ibin Hajar mai sharhin
Bukhari, sun yi kokarin sama
wa wannan mummanan
karyata juna dake cikin
hadisan dake haramta mutu’a
mafita na cewa ta yiwu an
maimaita hanin ne, sai dai
wannan zato ne da bai dogara
da wani dalili ba, taimakon da
zai iya yi shi ne ya samar
mana da shakka a kan haka;
wanda ya fi wannan rauni shi
ne fadar maimaita halattawan
da haramtawan fiye da sau
daya da wasu malamai (irin su
Imamu Shafi’i a
littafinsa
Kitabul-Ummu). Da wannnan,
ta yaya kuwa za a dogara goge
tabbataccen hukuncin AlKur’ani
da abin da ake shakka a kan
tabbatarsa?
c) Sai Ruwayar Salma bin
Akwa’u: Shi ne
hadisin
Musulim (a Littafin Aure,
babin mutu’a), wanda a
cikin
isnadinsa akwai Yunus bin
Muhammad da kuma Abdul-
Wahid bin Ziyad, wanda ya ce:
“Manzon Allah [SAWA] ya yi
mana rahusa da yin auren
mutu’a a shekarar
bude
Makka na kwana uku, sannan
sai ya hana yin auren.” Shi
ma wannan hadisi kamar
sauran ’yan’wansa ne, ba ya
iya zama hujjar haramta
mutu’a saboda
raunin hanyar
da ya fito (isnadinsa); domin
daga maruwaitansa akwai
Yunus bin Muhammad, wanda
manyan masana masu ruwaya
daga Ahlussuna guda uku suka
raunana shi, wadannan kuwa
su ne Ibn Mu’in da Nasa’i da
Ahmad bin Hanbali (kamar
yadda Zahabi ya bayyana a
cikin Mizanul- I’itidal
4/485).
Har ila yau a cikin maruwaitan
nasa akwai Abdul-Wahid bin
Ziyad, wanda shi ma bai sami
yabo a wajen malaman fannin
ba, saboda Zahabi ya ruwaito
zantukan wadannan malamai
suna zargin Abdul-Wahid da
cewa ya shahara wajen kago
insnadi na karya a ruwaya
(duba Mizanul- l’itidal 2/ 672
wajen ambatonsa); haka Abu
Dawud ya yi irin wannan
magana a kansa; Yahya bin
Mu’in ya kara da
cewa
“ruwayar Abdul-Wahid ba a
bakin komai take ba” (duba
duk wadannan bayanan a
wancan littafi na Zahabi).
A kan wannan ka kiyasta
kowane irin hadisi ka gani
yana haramta mutu’a koda a
littafan Shi’a ne kuwa.
Ruwayar da malamai masu kokarin haramta auren Mutu'a
ke
ishara da ita a al-Istibsar da
Tahzeebul-Ahakam na Sheikh
al-Tusi (daga malaman Shi’a
na karnin hijra na hudu), ko
dai irin wadannan malamai basu karanta su da kansu ba
ko
kuma ya zama sun
kawar da kansu daga cewa
wannan hadisi yana tsakiyar
sama da hadisai ashirin a
babobi daban daban na
mutu’a kuma ya
saba da duk
sauran. Sannan abin lura anan sune kamar haka: (a) a
cikin wadannan littafai biyu
kawai hadisin ya fito; (b)
Kuma duk littafan biyu mutum
daya ya wallafa su; (c) Sannan
mawallafin ya tabbatar da
rauninta bayan ya bayyana ta
a cikin Tahzeebul-Ahakam,
haka ya yi bayanin ma’anar
wannan hanin a cikin al-
Istibsar. Don haka babu abin
da ke taimaka wa haramta
mutu’a a duk
littafan Shi’a.
Kashi Na Biyu: Su ne
ruwayoyin da suke dangana
hana auren mutu’a da Khalifa
na biyu Umar bin Khattab
[RA]. Da alamun ambaton
wannan ne ya fusata wasu malamai masu fishi da fishin
wani har su nemi karyata
wannan dangane da tawile tawile marasa ma'ana.
Sai dai duk wanda ya bibiyi
wannan mas’ala da
abubuwan
da malaman Musulunci suka
tattauna a kanta zai zama ba
shi da hanyar karyata wannan
dangane ga Khalifa [RA].
Misali, daga hadisan da
Muslim ya fitar a wannan
babin akwai hadisin Ibn Juraih
daga Ibn Zubair, ya ce: Jabir
bin Abdullah (al-Ansari) ya ce:
“Mun kasance muna yin auren
mutu’a da
(sadakin) cikan
tafin hannu na dabino da
(nikakken) gari na ’yan
kwanaki a lokacin Manzon
Allah [SAWA] da lokacin
Abubakr [RA], har zuwa
lokacin da Umar [RA] ya hana
a kan lamarin Amr bin Haris.
A wata ruwayar irin wannan
da Muslim ya fitar, wadda
Ahmad bin Hambali ma ya
fitar da ita a cikin hadisan da
ya kawo kan mutu’a, an nuna
lokacin da Umar [RA] ya dauki
wannan mataki da cewa “a
karshen khalifancinsa
ne” (duba duk
wadannan a
Sahih Muslim 4/131 a Littafin
Aure, babin Mutu’a); haka
wannan ruwaya ta zo a cikin
Sunan na Baihaki (wajen
ambaton hadisan mutu’a a
Littafin Aure) da Tafsirin
Kurtubi (wajen fassarar Ayar
mutu’a) da wasunsu
da yawa.
Gaskiya ne cewa wasu
malamai sun ga ba makawa su
koma da haramtawar zuwa ga
lokacin Manzo [SAWA], da yin
tawilin zantukan Khalifa Umar
[RA] mai cewa “ina yin hani
a
kansu” da cewa yana
nufin
bayanin hanin da Shari’a ta yi
ne, ba shi da kansa ba. Haka
wadancan sun bayyana fadinsa
da ya gabaci wancan din,
wanda ya ke cewa: “Sun
kasance” da cewa yana
nufin a
wani lokaci da ya gabata kafin
a hana; da cewa Umar [RA] ya
fadi haka ne a bisa mumbarin
Manzo [SAWA] kuma a gaban
Sahabbai, da dai masu
sauraronsa ba su da labarin
hani a kanta da sun yi korafi a
kan haka. Sai dai duk
wadannan tawile-tawile zasu
rasa kowace irin kima idan aka
yi la’akari da
cewa:
1. Shi dai Khalifa da kansa bai
fadi hanin Shari’a kafin
zancensa ba; ya dai danagana
wa kansa ne hanin; da kuwa
akwai wani abu a Shari’a da ya
haramta mutu’a da ba za a
iya
fahimtar abin da zai hana
Umar [RA] ambatonsa a
lokacin haninsa ba. Rashin
dangana hanin ga Shari’a ya
nuna haninsa ne kamar yadda
ya bayyana haka a fili.
2. Ruwayoyin da ake dangana
haramta mutu’a ga AlKur’ani
da fadar Manzo [SAWA] duk
mun tabbatar da ranuninsu a
ka’idar ruwayar
hadisi ta
bangaren dukkan Musulmi.
3. A wani zancen na Umar
[RA] da ya zo a cikin ruwayar
da Baihaki ya fitar da ita a
cikin Sunan dinsa (7/206), an
hakaito Khalifa yana fusata
bayan Khaulatu bint Hakim ta
tsegunta masa auren mutu’a
da Rabi’u bin Umayya
ya yi da
wata mace, a kan haka ne
Khalifa ya fadi cewa: “Wallahi
da na gabaci wannan mutu’an
da na jefe shi a kansa.”
Wannan na nuna kafin
khalifancin Umar [RA] babu
hani a kan mutu’a.
4. Barazanar ukuba
da Khalifa ya yi ga duk wanda
ya kama da auren mutu’a ya
nuna yaduwarsa a tsakanin
Sahabbai (sabanin yadda
irin wadannan malamai suke
tsammani); abin da ke nuna
Sahabbai ba su da labarin
haramcin mutu’a kafin
Khalifa
ya hana; kuma barazana daga
mai mulki ba a wasa da ita,
shi yasa wasu Sahabbai suka
kame daga mutu’a.
5. Cewa Sahabbai irin su Ibin
Abbas [RA] da Jabir bin
Abdullah al-Ansari da wasunsu
sun yi karfin halin hamayya da
matsayin Khalifa, inda suka ci
gaba da fatawa a kan
wanzuwar halaccin mutu’a.
Abubuwan da wasu ke kokarin
fada na cewa Ibin Abbas ya
dawo daga halatta shi daga
baya; da cewa Jabir ba shi da
labarin haramcin ne ya sa ya
nace a kan halatta shi, duk
tawile tawile ne da ba su
jingina da wani dalili ba; don
haka ne ma malaman furu’a
suka yi sakwa-sakwa da
haramta mutu’a (ba su
tsananta a kansa ba).
6. Zancen da Imam Ali [AS]
ya yi ta nanatawa na cewa ba
don hanin Khalifa ba da babu
mai yin zina sai tababbe. Ka
kuwa riga ka ji cewa dangana
ruwayar haramta mutu’a gare
shi rarrauna ne da ya fito
daga wadanda aka zarga da
tadlis da majhuli.
Wadannan kawai sun isa nuna
cewa hanin na Khalifa ne,
wanda shi ke da akalar mulki
a hannunsa. Illa dai akwai
uzurori da wasu ke ba Khalifa
a kan haka, daga ciki akwai
cewa ya yi wannan hani ne
saboda wata maslaha da ta
shafi wannan yanayin, don
haka haninsa ba na dindindin
ba ne. Wannan ya sa wasu
daga malaman Ahlussunna
(duk da su ne ’yan tsiraru)
suka saura a kan halatta
mutu’a.
AUREN MUTU'A TSAKANIN
MUSULMI (3)
Fadar Halaccin Mutu’a.
Wadanda suke ganin hallacin
auren mutu’a sun dogara
ne
da:
1. Ayar AlKur’ani (Nisa’i:
24) wadda duk Musulmi suka
dace a kan cewa ita ta hallata
mutu’a, amma suka
saba a
kan goge ta; kenan halattawan
tabbatacce ne, haramtawan ne
ake da shakka a kansa; babu
inda shakka ke iya goge
yakini.
2. Ga kuma tarin hadisai
a kan halaccin auren, wadanda
aka ambace su a dinbin litattafan hadisan Ahlus sunna
kuma Malamai ba su yi jayayya da su
ko karyata su ba.
3. Cewa hadisan da ake
dogara da su a kan haramcin
mutu’a ba su
inganta ba ta
fuskar isnadi da ma’ana (don
sun saba wa AlKur’ani), don
haka ba su da karfin da za su
iya goge hukuncin da ya
tabbata a AlKur’ani.
4. Malaman Ahlul-baiti
(wadanda ’yan Shi’a ke dauka
a matsayin magadan ilimin
kakansu) duk sun dace a kan
halaccin mutu’a.
Halattawarsu
gare shi ne ma ya wanzar da
tattauna wa a kansa a tsawon
tarihin bincike da nazari. Da
ma kuwa Annanbi [SAWA] ya
fadi cewa ya bar mana su
(Ahlul-baiti) tare da AlKur’ani,
kuma ba za su taba rabuwa ba
har su same shi a bakin tafkin
Alkausara (Sahih Muslim
4/1873 hadisi na 2408).
5. Cewa akwai Sahabban da
suka tafi a kan rashin shafe
hukuncin mutu’a har suka
bar
duniya.
6. Kara da cewa kowane irin
dalili ya sa Shari’a ta halatta
mutu’a a jiya, to
wannan dalili
na nan a yau. Kuma bukatar
mutu’a a yanzu (da
hayoyin
fitinuwa suka wayaita) bai kasa
bukatarsa a farkon Musulunci
ba idan ma bai wuce ba.
7. Cikar Musulunci da
Musulmi suka yi imani da shi
kuma wanda AlKur’ani ya
tabbatar da shi (al-Ma’ida: 3)
yana nufin cikakkun tanaje
tanajen da Musulunci ya
samar ne, wadanda za su
magance wa Musulmi duk
matsalolinsu na rayuwa. Idan
aka ce Musulunci ne ya share
mutu’a to an
tuhume shi da
samar da gibi ga mabiyansa,
wanda bai musanya shi da
wani abu mai tasiri ba.
Saboda azumi yana rage kaifin
sha’awa ne ba
biyan bukatar
jima’i ba; saboda
mabukaci ko
ya yi azumi yana da bukata
idan ya yi bude-baki; kuma
azumi ba ko da yaushe ake
yinsa ba; sannan akwai masu
uzurin da aka sauke musu
azumin farilla ma balle na
rage sha’awa. Halin
matsi da
matsan da ba su da ikon aure
na dindindin kan shiga a
lokacin fizgar balaga ba shi da
magani sai mutu’a, in ba haka
ba kuwa sai zina ko dabarun
fitar da maniyyi da hannu
(wanda ke haifar da cutar
saurin gama jima’i ga da
namiji da barazanar kau da
sha’awar mace
gare shi gaba
daya) barnar wadannan
lamurra ga daidaiku da
al’umma kuwa
bayyane yake
ga kowa. Wannan ya kore
soki-burutsun tsirarun Ustazai na kore
mutu’a da rashin
kawo wa
matasa kakkarfar mafita.
Mutu’a A Furu’a.
A nan ne nake son yin gyra a
kan sigar da wannan
tattaunawa take tafiya. Wani
abu da masu tattaunawa suka
rafkana daga gare shi shi ne
cewa kallon mas’aloli irin
wannan ya kamata ya fi bayar
da karfi ne ta mahangar
furu’a. Saboda
daukar
matsayin halattawa ko
haramta abu irin mutu’a yana
bukatar wasu ilmummuka da
suka wuce harshen larabci da
karanta hadisai da tafsiri.
Akwai kusan fannonin ilimi
har guda tara (wasu sun kai su
har goma sha daya) da ya
kamata mutum ya kware (ba
kawai ya san wani abu a kansu
ba) kafin ya yi fatawa da halal
ko haram a furu’a.
Masifar da aka jarabci
al’ummar Musulmi
a ’yan
shekarun nan shi ne na wasu
’yan Ustazai da suka fito daga
wasu jami’o’in wasu kasashen
Larabawa, bisa dogaro da
kalkala da kadifiri na magana
da harshen larabci sai suka
shiga dora mutane a kan
abubuwan da suka saba wa
mazahabobinsu na furu’a.
Wannan kuskure ne babba.
Dole ne mutum ya koma ga
daya daga wadanda aka dace a
kan ikonsu na iya shiga cikin
wadancan ruwayoyi masu karo
da juna da samar da mafita,
don aiki da abin da suka yi
fatawa a kai. Dole Ahlussunna
su koma ga malamansu (bai
halatta su dauki fatawar
wasunsu don jin dadi kawai
ba), haka ma dan Shi’a wajibi
ne ya dogara da fatawar
marja’i a kan komai
har da
mutu’a. Wannan shi
ne abin
da duk bangarorin biyu suka
dace a kai.
Malaman furu’a sun kasu
kashi
biyu a kan auren mutu’a;
akwai wadanda ijtihadinsu ya
kai su ga halatta shi
(wadannan su ne daukacin
malaman Shi’a a jiya da
yau,
da wasu ’yan tsiraru
daga
malaman Ahlusunna); sai
kuma galibin malaman
Ahlussunna, wadanda
ijitihadinsu ya kai su ga
haramta shi. Amma duk da
haka, malaman suna da wasu
hukunce hukunce da suka dora
mabiyansu a kai; misali
mazhabar Malikiyya sun dace
a kan cewa:
1. Idan dan Malikiyya ya yi
mutu’a a raba
auren.
2. Matar da a ka yi mutu’a da
ita ta cancanci dukkan sadakin
da aka dace idan mijin ya taba
saduwa da ita, da rabin sadaki
idan bai taba saduwa da ita
ba.
3. Kar a yi musu haddi (ba
bulala ba balle jifan
zawarawa); sai dai wasu sun ce
a tsawatar da su da wata
ukuba da alkalin shari’a ya ga
ta dace.
4. Idan aka sami ciki dan
yana bin ubansa ne, kuma dan
halal ne. Wannan ne ya sa
wasu masu da'awar malanta kuma ake daukan su a
matsayin malamai suke fadar abin kunya na ban mamaki
yayin da suke cewa: “duk dan da
aka samu ta auren mutu’a ba
dan aure ba ne!” alhali hatta
a
cikin Iziyya ta Shazili (wanda
ake karanta shi daga matakin
farko na karatun fikihu a kasar
nan) an tabbatar da sabanin
haka a Babi na Takwas a kan
Aure da Saki (shafi na
201-202), da cikin
Thamaruddani sharhin Risala
ta Abu Zaid (shafi na 447).
5. Da yana gadon iyayensa
bisa fatawarsu ta cewa dan na
bin ubansa.
Su kuwa ’yan Shi’a da suke
halatta shi, suma sun bayyana
hukunce hukuncensa; wasu
daga cikin wadannan hukunce
hukunce sun hada da:
1- Sadaki sharadi ne a cikinsa;
yana iya zama duk abin da
ma’auratan suka
dace a kai.
2- Idan ba a ambaci mudda a
lokacin daura shi ya zama na
dindindin.
3- Ba a wajabta gado tsakanin
ma’aurata a
cikinsa ba, sai a
inda aka shardanta hakan a
lokacin daura shi.
4- Babu saki a tare da shi, sai
dai mijin yana iya yafe mata
muddar da ta saura a duk
lokacin da ya so.
5- Ciyarwa ba wajibi ne a
cikinsa sai a inda aka sa shi a
matsayin sharadi a lokacin
kulla auren.
6- Ba shi da iyakantaccen
adadi, mutum na iya yi da
iyaka adadin da ya so.
7- Ba a yi da budurwa sai da
izinin waliyyinta na Shari’a.
8- Makaruhi ne a yi mutu’a
da wadda ta shahara da da
zina da mai zaman kanta.
9- Ya halatta ayi azalu (fitar
da maniyyi a waje) yayin
saduwa ba da izininta ba.
Wadannan sharudda da ire-
irensu masu yawa suna iya
bayyana wa kowa cewa ba a
shardanta mutu’a don barna
ko sangarta mutane ko
raunana auren dindindin ba;
sai don kara kare al’umma da
rage zafi ga wadanda ba su da
ikon dauwamammen aure ko
wadanda suke bukatar karin
lokaci don shirin auren
dindindin da sauransu. Kar a
manta da cewa ba don maza
kawai aka shar’anta wannan
auren mutu’a ba; mata ma
za
su iya cin gajiyarsa kusan fiye
da maza. Yanzu zawarawa
nawa ne suka share shekaru
ba miji, ko saboda wahalhalu
da suka sha a tsohon aurensu
suke tsoron gaggauta sake
aure; yaya irin su Ja’afar za su
yi da sha’awar irin
wadannan?
Wannan zai nuna kuskuren
ustazai na kokarin nuna
mutu’a da mummunan
sura.
Da dai zasu takaita da ambaton
fatawowin malaman furu’a da
haka fi alheri gare su da
al’umma baki
daya. Kuma ya
kamata kafin zargin masu
halatta mutu’a irin
wadannan mutane su ba
kansu lokacin sanin ainihin
abin da suke fada a kan
auren, amma abubuwan da ya
bayyana sun nuna basu san
fatawoyin masu halatta mutu’a
ba.
Idan Shari’a ta halatta
mutu’a
ne don manufar saukaka wa
mutane, shawarar irin wadannan Usatazai na
takaita da auren dindindin ba
ta da mahalli kenan. Mun
dace da su a kan kira zuwa ga
bin Sunnar auren dindindin
amma ba tare da haramta
mutu’a ba. Kuma
kasancewar
Manzo [SAWA] ya yi auren
dindindin bai cutar da
halaccinsa ba, saboda Annabi
ba duk halal ya ke yi ba.
Kuma ai an halatta masa rike
mata fiye da hudu bayan
kuyangu; yanzu wadannan malamai zasu iya
auren mata fiye da hudu? Ko
suna da hanyar samun
kuyangu? Sai dai idan sun
halatta wa kansu tabi’ar auri-
saki, wanda zaluncinsa
bayyane yake ga kowa.
Kuma ina ba masu tattauna
mas’alolin addini
shawara da
koyon ladubban tattaunawa.
Yanzu ina amfanin zargin da
wasu ustazai sukeyi na cewa litattafan shia “cike
suke da karya da cakuda
gaskiya da karya.” Wannan irin
diban-karan-mahaukaciya da
suke yi na hukunta “littattafan
Shi’a” ya saba wa kowane irin
mizani –na hankali da
Shari’a.
Irin wannan babban zargi ya
kamata ya biyo bayan tarin
misalai ne na wuraren da
“littattafan Shi’a” suka yi
karya
da wuraren da suka “cakuda
gaskiya da karya”. Su sani
cewa ba a kan wasu ’yan
tsiraru suke magana ba; yanzu
’yan Shi’a a kasar nan
sun
wuce yadda duk suke
tsammani a adadi da tasiri da
karfi ta kowace fuska. Ba kore
samun kuskure –kai hatta ma
samun ganganta karya- nake
yi ga littafan Shi’a ba, amma
gamammen hukuncin nasu ne
yake da sa kuka da dariya a
lokaci daya.
Rufewa
Na yi kokarin yin bayani ne a
kan matsayin auren mutu’a a
tsakanin Musulmi. Ta bayyana
cewa dukkan Musulmi sun
dace a kan cewa asalinsa halal
ne; amma sun saba a kan
wanzuwar wannan halacci da
goge shi. Akwai masu ganin
wanzuwar wannan halacci
akwai kuma wadanda suka tafi
a kan cewa an goge shi; kowa
ya dogara ne da hakkin da
Musulunci ya ba shi na yin
ijtihadi, da yadda ya bar
kofarsa a bude ga Musulmi a
kowane zamani. Abin kuma
sha’awa shi ne
yadda
Musulunci ke da fadin kirjin
rungumar sakamakon
ijtihadodin ’ya’yansa –matukar
sun yi su bisa ka’idar yin
ijtihadi- ta yadda ya ba duk
wanda ya yi daidai a
ijtihadinsa lada biyu na
kokarinsa da samun daidai da
ya yi; ya kuma ba da lada
daya ga wanda ya yi kuskure
saboda kokarinsa (Hadisin
Bukhari ma ya tabbatar da
haka).
Don haka abin takaici ne ganin
yadda wasu ke kokarin takaita
wa Musulunci fadinsa; da
gda ba ta su ba, da kokarin
tilasta mutane a kan
takurarren tunaninsu.Ya zama
dole Musumi su kare kansu
daga irin wadancan, ta hanyar
lizimtar fatawoyin malamansu
na furu’a da
mujtahidan da
suka cika sharuddan ijtihadi.
Da hake ne kawai za su tsira
daga fadawa rudani da rashin
sanin kakkarfar majingina.
Allah Ya sa mu dace amin.
Wa sallal lahu ala Sayyidina Muhammad wa ala alihit
tahirin.
Masha Allah abu yayi kyau. Allah Ya saka da alheri da bude wannan shafin, mal. Murtala
ReplyDeleteAmin Malam Auwal, ai kune manya a wannan fage. Da fatar za ku rika bamu shawarwari, da ilimantarwa ta yanda zamu qara ingantawa, da kuma gyara a inda muka yikuskure.
Delete