Skip to main content

ME YA SA 'YAN SHI'A SUKE SUJADA AKAN TURBA?


“Turba” kalma ce ta larabci wanda yake nufin “K’asa”. ‘yan shia suna salla a kan kasa ne saboda abinda yazo a fikhu na wajabcin yin sujada a kan kasan, da rashin ingancin yin sujada a kan wani abunda ba kasan ba saidai in shima dangin kasan ne kamar dutse da makamancin sa, ko kuma abinda ya fito daga kasan na tsirrai, saidai bai hallata ba a yi akan sa sune abinda yake abinci ne ko tufafi. yin sujada akan koma bayan wadannan abubuwan da aka sharadanta yana sanya rashin ingancin salla wanda yake shine ibada mai daraja ta daya a muhimmanci.
Da wannan ne yasa ‘yan shia domin saukakawa suke kwaba laka su busar da shi suna yin sujadan a kan sa. Wannan shi ya haifar da za ka taras ‘yan shia suna daukan wannan turba a tare das u domin idan salla ya same su sais u sanya domin yin sujada a kan sa musamman idan wajen sallar ko masallacin a shimfide yake da shinfidu na zamani, haka ma shi ya sanya in ka shiga masallatan ‘yan shia zaka tarar da wadannan dunkulallun kasa wanda ake kira turba domin a rika sanya goshi ana sujada akan sa sakamakon masallatai shinfide suke da shinfidu na zamani

HADISAN AHLUSSUNNA WADANDA SUKA NUNA WAJABCIN YIN SUJADA AKAN K’ASA
Duk da cewa malaman Ahlus sunna sun halatta yin sujada akan komai to amma akwai hadisai suma a cikin litattafan ruwayoyin su wadanda suka nuna cewa sujada baya inganta sai aka kasa.

Yazo a cikin Sahihiul Bukhari, Manzon Allah s.a.w.a yace ‘’An sanya kasa gare ni ya zamo abin sujada da tsarkakewa.(Sahihul Bukhariy juzu’i na 1 shafi na 91, sunanu Baihakiy juzu’i na 2 shafi na 433 da sauran litattafan ruwayoyi)

Yazo cikin Musnad na Ahmad bin Hanbal daga Ummulmu’uminina Maimuna tace manzon Alla s.a.w.a ya kasance yana sujada akan yankin tabarmar da aka saka da ganye dabino. (musnad Ahmad bin Hanbal juzu’i na6 shafi 331)

Yazo cikin Musannaf na Ibn Abu Shaiba, daga Ummul muminina A’isha tace ban taba ganin Mazon Allah ya dora goshin sa akan wani abu ba (koma bayan kasa) (musannaf juzu’i na 1 shafi na397)

An rawaito hadisi daga daga Wa’il bin Hujur yana cewa “lallai Annabi s.a.w.a idan zaiyi sujada yakan sanya goshin sa da hancin sa akan kasa ne.(Musnad Ahmad bin Hanbal juzu’i na 1 shafi na 315)

Sahabban Manzon Allah suma sun kasance basa yin sujada akan wani abu face ka kasa koda kuwa a cikin yanayi mai wahala ne.

An samo hadisi daga Jabir bin Abdullahil Ansariy yana cewa na kasance ina salla tare da Annabi s.a.w.a sallar azahar (a lokacin tsanin zafi), sai na kwashi damki na kasa, sai na sanya shi a hannu na ina juyawa zuwa wani hannu saboda tsananin zafi har sai da yayi sanyi sannan sai na saka shi a goshi na ina sujada a kan sa.

Bayan hakaito wannan hadisi baihakiy yayi ta’aliki yace da ace ya halatta ayi sujada akan tufafi wanda yake tare dashi a jikin sa, da yafi sauki yayi akan tufan maimakon (ya sha wahala wajen) sanyaya kasa.

An karbo hadisi daga Ibn Abbas cewa Manzon Allah yana sujada akan dutse (Sunanu Baihakiy; juzu’i na 2 shafi na102)

A cikin littafin Musannaf an ruwaito daga sahabin Ibn Mas’ud yana cewa, shi Ibn Mas’ud din baya sujada akan wani abu in ba kan kasa ba koda kuwa a cikin jirgin ruwa ne sai ya riki wani yanki daga kasa ya hau da shi domin yayi sujada a kan sa. (musannaf juzu’i na 1 shafi na 367)

Akwai ruwayoyi masu yawa wanda suke nuna wajabci da muhimmancin yin sujada akan kasa. Mai neman zurfafa bincike yana iya duba littafin Silsilatul Masa’ilil Fiqihiyya, mas’ala ta shida na Shaikh Allama Ja’afarus Subhaniy.
2 Fiqihiyyat bainash shi’a wassunna, na Ustaz Atif Salam)

Comments

Popular posts from this blog

MENENE TAMBAYOYIN DA ‘YANMATA SUKE YI??? NA 1

MENENE TAMBAYOYIN DA ‘YANMATA SUKE YI??? ماذا تسأ ل الفتيات؟ NA   - 1 DAGA “CIBIYAR NUUN” MASU WALLAFA DA TARJAMA FASSARA: MURTALA ISAH DASS MUKADDIMA A kwai tambayoyi (masu yawa) da suke kekkewayawa a cikin rai (kwakwalwar) ko wace budurwa, wadanda take bukatar amsar su, wani lokaci takan koma wajen uwarta ko 'yar'uwarta ko kawarta ko kuma wajen malamarta ta makaranta. Saidai wani lokaci bata gamsuwa da amsar da suke bata. Saboda haka sai kaga son sanin wadannan abubuwan na tunkudata zuwa ga tambayoyi masu dinbin yawa (alhali ta rasa mai bata gamsassun amsoshi) Yawancin uwaye kunya na lullubesu (suna jin kunya) game da amsa wasu sashen tambayoyi masu tsarkakiya. (Sannan wani bangare kuma ita kanta budurwar ce take jin kunyar yin tambayar alhali abin na damunta tana so ta sami bayani a kan su) Wannan littafi da ke gaba gareki ya ke 'yar'uwata abar girmamawa, tattararrun tambayoyi ne daga cikin tambayoyi wadanda ake jin kunyar ...

SHIN GASKIYA NE ‘YAN SHI’A SUNA TUHUMAR UMMUL MUMININA A’ISHA DA AIKATA ZINA?

SHIN GASKIYA NE ‘YAN SHI’A SUNA TUHUMAR UMMUL MUMININA A’ISHA DA AIKATA ZINA? Daya daga cikin abinda makiya shia suka dau tsawon zamani suke yadawa na karya akan ‘yan shia domin kyamatar da al’uma da wannan mazhaba ta ‘ya’yan gidan Manzon tsira s.a.w.a shine cewa wai suna da kudurin dora wa Matar Manzo A’isha ‘yar khalifa Abubakar tuhumar aikata zina (wal’iyazu billah). Da alama wadanda suka tsara wannan qaryar basu san cewa wata rana duniya za ta iya kasancewa tamka gari guda ba ta tayanda babu abinda zai buya ga wani. Yanzu dai ga ‘yan shia ko ina ana tare da su, ga malaman su cikin sauki za’a iya tuntuban su sannan ga dubban litattafan su a kasuwa kowa na iya saye ya karanta, uwa uba kuma ga yanar gizo wanda cikin lokaci kankani mutum zai binciki irin littafin da kake bukata ya karanta. Wani abin mamaki shine sai ga ‘yan shia basu ma yarda da wannan tuhumar akan ita Ummul muminina A’isha ba balle kuma tabbatar da tukuhumar a kan ta. Za mu duba bayanan malaman shia game da wannan a...

AUREN MUTU'A TSAKANIN MUSULMI

AUREN MUTU'A TSAKANIN MUSULMI (1) Sheikh Sale Sani Zaria Idan mutum ya bibiyi abubuwan da ake fada da rubutawa a kan Auren Mutu’a a wannan zamani daga malaman Ahlus Sunna. A dukkanin abubuwan da ake fada akwai abubuwa masu jan hankali matuka wanda ake bukatar al'umar musulmi su fahimci hakikanin sa. Alhamdu lillahi dukda cewa su malaman suna kokarin fada da wannan ibada amma anyi dace suka yarda da halaccin Mutu ’ a da ayar AlKur ’ ani ta cikin Surar Nisa ’ i aya ta 24. A kan haka ne ma nake ganin cewa duk mai hankali zai yi mamakin yadda wasu malamai suke kwatatnta auren mutu ’ a da "dadiro" ko "kwanan gida". Idan har mutum ya yarda da cewa akwai ayar AlKur ’ ani wadda ta halatta Mutu’a ko da kuwa ya yarda da cewa an goge ta daga baya, to da wace irin mahanga kuma yake kwatanta shi da dadiro da kwanan-gida? Ina ayar da ta taba halatta dadiro da kwanan-gida a AlKur ’ ani har ya cancanci irin wannan kwatanci? Dadiro fa alfasha ne! Yanzu yana jin cewa ...