Skip to main content

ME YASA YANSHIA SUKE SHAFAN KAFA A ALWALA BA WANKEWA BA?



ME YASA YANSHIA SUKE SHAFAN KAFA A ALWALA BA WANKEWA BA?

Addinin Musulunci addinin ne na mika wuya ga Allah Madaukakin sarki. Shi Allah Ya halicci dandam da Aljani ne domin su bauta masa, bai yarda da bautan wanin saba in ba shi kadai ba. Wannan bauta kuma bai yarda mutum ya yi shi yanda yaga dama ba, sai ya aiko Manzannin sa ya saukar musu da littafi mai dauke da yanda yake so su gudanar da bautan. Saboda haka aiki zai zamo karbabbe ne a waje Allah kawai idan ya dace da yanda yayi umurni ayi.
Manzo na qarshe da Allah ya aiko shine Annabi Muhammadu (sawa) tare da littafi Alqurani mai girma, ta yanda ya umurci wannan aluma da aikin ibadu naui dabam-dabam ciki kuwa har da Sallah, kuma ya zamo shine mafi girman a cikin su. Kuma shi Manzon ya koyar da wadannan ibadu a aikace a fili kuma filla-filla.

To saidai wannan addini na Musulunci ya gamu da ibtilai a inda bayan rasuwar Manzo s.a.w.a aka sami sabani dangane da alamura masu yawa, sakamakon jarrabar addinin da akayi da wasu gurbatattun masu daawar musulunci a baka amma baikai zuci ba wadanda sukayi ta kawo cikas. Hatta abuwan da basu dace da ace an sami sabani akan suba kamar wannan ibada na salla wanda a daukacin rayuwar Maaiki s.a.w.a tun bayan aiko shi da sakon Annabta yake yi tare da jamaa sau biyar a kowani yini, amma sai gashi an sami alumar musulmi sun yi sabani akan sa sakamakon kokarin irin wadannan gurbatattu na ganin sun jirkita addinin koma su kawo karshen sa.
Baban abin tsoro shine tun baaje ko ina ba sai ga tarihi na nuna cewa Sahabin Annabi kuma hadimin sa Anas bin Malik kamar yanda Bukhari ya fitar a Sahihin sa, bayan rasuwar Maaiki s.a.w.a da yayi tafiya zuwa Sham, yaje masallaci akayi salla dashi, da ya komo masaukin sa sai akaga yana kuka, sai aka tambayeshi me kuma ya sa ka kuka? Sai yace babu wani abu na addini wanda jamaa basu jirkita shi ba daga yanda Manzon Allah (sawa) ya aikata ko ya koyar, sai wannan salla da mukeyi, to amma sai naga ita sallar ma an jirkita ta.(Sahihul Bukhari JuzuI na 1, shafi na 134)
Kamar yanda Imam Ahmad bin Hanbal shima ya rawaito irin wannan hadisi inda yake cewa da aka tambayi Anas bin Malik cewa me yasanyaka kuka? Sai ya amsa da cewa; bansan wani abu na addini da akeyi a lokacin Manzon Allah wanda yau baa jirkitashi ba, face fadar lailaha Illallahu da kuke yi, . (Musnad Ahmad bin Hanbali, juzuI na 3 shafi na 270)
Wannan abin tsoro ne dake nuna zurfin irin hatsarin da wannan addini ya shiga ciki tun bai wuce karnin farko ba, tun sahabban annabi basu gama barin duniya ba amma an canza alamuran addinin. Sannan wannan canji bai tsaya ga wasu ayyuka masu wuyan shaani kawai ba, aa har ma ayyukan da Manzon Allah yake yi tare da jamaa ko wane rana akalla sau biyar wato sallolin farilla na kowace rana.
Shima mukaddimar da ake gabartarwa kafin shi wannan salla wato Alwala kenan bai tsira daga wannan jirkita ba. Manzon allah s.a.w.a ya kasance yana yin alwala a gaban iyalan sa, hakama sahabban sa na kimanin shekaru ashirin da uku amma wai ace an sami sabani game da yanda akeyin sa.
A matakin farko ayan alkurani ya karantar da yanda ake alwala a yayin da yake cewa ya ku wadanda sukayi imani idan kun tashi zuwa ga salla ku wanke fuskokin ku da hannayen ku zuwa gwiwoyi, kuma ku shafi kayukan ku da sawayen ku zuwa dugadugi. (Maida, aya ta 6). Kuma abinda akayi ittifaqi shine babu yanda zaayi Manzo ya sabawa karantarwar Alkurani.
Amma sai gashi an canza shafan kafa zuwa wankewa. Domin a qare hakan sai aka kawo tawile tawile game da fassarar ayar don a nuna dacewar wanke kafofin ne ayar tazo dashi.
A yayin da Ahlul baiti a.s da mabiya karantarwar su suka suka tsayu akan abinda Alqurani ya koyar na yin shafa akan kafafuwa kuma kamar yanda suka ga kakan su Manzon Allah s.a.w.a yake yi kuma ya koyar da aluma.
Mahukuntan banu Umayya su suka aukar da wannan canji na alwala wanda kuma canjin ya faro tun lokacin khalifanci Usman bin Affan.
Sahabban Manzon Allah irin su shi wannan hadimin Manzo Anas Bin Malik, Abdullahi Bin Abbas da makamantansu sun yi fama da gwagwarmaya wajen ganin cewa Musulmai basu canza wannan ibada na alwala daga shafan kafa zuwa wankewa ba, amma ina! sakamakon hukumomin Banu Umayya sun tsaurara da tilasta jamaa, basu sami nasara ba.
Mahukuntan Umayyawa irin su Hajjaj AS-sakafiy su suka rika tilasta Mutane wajen wanke kafafuwan su maimakon shafawa. A yayin da Su Ibn Abbas da Su Anas bin Malik suka yi tawaye kuma suke yin fatawa wa mutane dasu rika shafan kafafuwan su domin Haka yake a cikin Kurani kuma Haka Manzon Allah ya kasance yake yi. Kamar yanda yazo a cikin tafsirin Ibn Kasir da tafsirin Ibn Jarir Tabari a karkashin tafsirin ayan alwala, cewa; (a yayin da aka taho ana bada labara was hi Anas cewa) Hajjaj yazo yana mana huduba yana ce mana idan zamu yi alwala mu wanke ciki da bayan kafafuwan mu domin babu wani gaba a jikin danadam da yafi kusa da daukan najasa kamar kafa. Sai Anas yace; Allah Yayi gaskiya kuma Hajja yayi karya, saboda Allah cewa Yayi ku shafi kawukanku da kafafuwanku. Kuma sai ya bayyana cewa shi Anas idan yana alwala shafa kafafuywansa yake yi.

Shima Ibn Abbas akwai hadisai da dama da suke nuna yanda yayi ta irin wannan gwagwarmaya da wannan canjin na mahukuntan Banu Umayya, kamar yanda yazo a cikin Tafsirin Durrul Mansur a karkashin tafsiri Ayar alwala cewa; Mutane sun nace game da lamarin wankin kafa a alwala, ni kuma ban sami hakan a Alkurani ba face umurni da shafawa.

Wannan abu har ya kai ga wasu sahabbai masu jin tsoron musgunawan hukuma sai sun buya suke koya wa mutane yin salla da alwala da sauran alamuran addini kamar yanda yake a hukunci.
Yazo a cikin Musnad da Muuyjamul Kabir cewa Sahabi Abi Malikil Ashariy yana fada wa mutanen sa (kabilarsa) cewa ku taru domin in koya muku irin sallar Manzon Allah s.a.w.a , yayin da suka tattaru sai yace musu; shin akwai wani a cikin ku wanda ba kuba? Sai sukace aa saidai dan yaruwarmu, sai Abiy malik din yace ai dan yaruwan mutane yana cikin su. (a lura da nwannan nuqda da kyau, yana wannan bincike ne domin tsoron kada wani yaga abinda zai aikata yaje ya sanar da hukuma cewa ga wani yana koyar da mutane salla sabanin yanda hukuma ta yarda ayi) sannan sai ya sanya aka kawo masa ruwa sai yayi alwala, a yayin alwalar tasa bayan ya kammala wanke fuska da hannayen sa, sai ya shafi kansa da kafafuwansa. (Musnad Ahmad bin Hanbal, juzuI na 5 shafi na 342. Muajamul kabir, juzui 3 shafi 280)

Sannan sai wadannan mahukunta na Banu Umayya suka sanya aka kirkiro hadisai wadanda yanzu aka cika litattafai da su wadanda suke nuna cewa wai Manzon Allah yana wanke kafafuwansa ne a yayin da yake alwala. Saidai a kefe guda kuma akwai dimbin hadisan a cikin litattafan na Ahlus Sunna wadanda suke nuni da cewa Manzo (sawa) shafa kafansa yake yi. Saidai abinda akayi ittifaqi dashi a tsakanin musulmi shine duk lokacin da hadisai guda biyu suka taho masu karo da juna to mataki na farko shine a gittasu ga Alkurani mai girma, duk hadisin daya dace to shine ingantacce, wanda ya saba da Alkurani sai ayi jifa dashi a garu. Anan babu wahalan binciken sahihanci ko rashin sahihancisa ta bangaren maruwaita (jarhu wat taadil)
A fitowa na gaba da yardar Allah zamu kawo wadannan Hadisai kamar guda ashirin daga litattafan Ahlus sunna wadanda suke nuni da cewa Manzon Allah s.a.w.a shafa kafansa yake yi a yayin alwala kamar yanda Alkurani ya koyar, ba wankewa ba.


NADISAN SHAFA KAFA A ALWALA DAGA RUWAYOYIN AHLUS SUNNA.

A bayanin day a gabata an na bayyana dalilin faruwar canjin shafan kafa a alwala zuwa wankewa, wadda mahukuntan banu umayya suka aukar, kuma aka kirkiro hadisai wadanda suke ‘kare wannan canji aka dangana su zuwa ga Manzon Allah s.a.w.a. alhali Allah Ta’ala yaayi bayani a cikin Alkur’ani karara yanda za’ayi alwala a inda yayi umurni a wanke fuska da hannaye, a shafi kai da kafafuwa.

A yayin da Ahlul baiti da Mabiyansu suke shafa kafafuwansu a yayin alwala kamar yanda Allah Ta’ala yayi umurni kuma Annabin da aka aiko shi da wannnan ibada shima yake aikata haka.

Su kuma Ahlus sunna suke wanke kafafuiwan su kamar yanda malaman sun a fikhu suka bada fatawa bisa dogaro da wadancan hadisai.

To saidai kamar yanda na ambata a baya, a cikin litattafansu na ruwayoyi akwai hyadisai birjik wadanda suke nuna cewa Manzon Allah shafa kafafafuwansa yake yi a yayin alwala ba wankewa ba. sannan wasu ruwayoyin sun nuna yanda wasu8 sahabbai suke karantar da mutane cewa shafa kafa akeyi yayin alwala ba wankewa ba . Kuma anyi ittifaki cewa duk lokacion da ruwayoyi biyu suka taho masu karo da juna, to ana bijirar das u ne bisa alkur’ani., duk wanda yayi daidai da karantarwar alkur’ani to shine ingantacce, wanda ya saba masa kuwa sai ayi jifa da shi.

Ga kadan daga cikin irin wadannan ruwayyoyi:




1- An karbo hadisi wanda ya tuke daga Basru ‘dan Sa’id yace; Usman (bin Affan) yazo mazaunin sa, sai ya bukaci yin alwala (a yayin alwalar tasa) sai yayi kurkurar baki kuma ya sheka ruwa (a hancin sa), sannan sai ya wanke fuskar sa sau uku da hannayen sa sau uku-uku sai Ya Shafi Kansa Da Kafafuwan Sa sau uku-uku. Sannan sai yace “ Naga Manzon Allah haka yake alwala.” (sannan sai ya juyo ya fuskanci jama’an da suke tare dashi sai ya tambaye su yace musu) “ yaku wadannan (jama’a) haka yake?” Sai suka ce “haka ne” (yayi tambaya ne) ga wasu sashen sahabban Manzon Allah s.a.w.a wadanda suke tare dashi a wajen. (Musnad na Ahmad Bin Hambal, juzu”I na 1, shsfi na 109, hadisi na 489)




2- An karbo hadisi daya tuke daga Humran yace; Usman ya bukaci ruwa, sai yayi Alwala sannan sai yayi dariya. Sannan sai yace “ baza ku tambaye ni don me nake dariya ba?” sai sukace ; “ya shugaban muminai me ya sa ka dariya?” sai yace “Naga manzon Allah yayi Alwala kamar yanda nayi Alwala. Sai yayi kurkuran baki kuma ya sheka ruwa kuma ya wanke fuskar sa sau uku kuma ya wanke hannayen sa sau uku-uku, sai yayi shafa a kansa da bayan dugadugin sa. (Kanzul ummal juzu’I na 9, shsfi na 436, hadisi na 26,863).




4- An karbo hadisin daya tuke daga abi Matar, yace wata rana muna zaune tare Aliyu (r.a) a cikin Masallaci, sai wani mutum yazo wajen Ali sai yace; ka nuna min alwalan manzon Allah s.a.w.a. sai (Ali a.s) ya kira Kambar sai yace ka taho mini da butan ruwa. Sai ya wanke (tafukan) hannayen da fuskar sa sau uku-uku, sai ya shigar da sashen yatsun sa a cikin bakin sa, kuma ya sheka ruwa (a hancin sa) sau uku-uku. Sannan ya wanke damasun sa sau uku-uku, kuma ya shafi kansa sau daya da kafafuwan sa zuwa dugadugi, a yayin dagemun sa take saukowa akan kirjin sa, sannan sai ya kurbi (ruwan) kurbi guda bayan yayi alwalan. Sannan sai yace “ina mai tambaya game da Alwalar Manzon Allah s.a.w.a , to haka Alwalar Manzon Allah (sawa) take.

(Kanzul Ummal, juzu’I na 9 shafi 448, hadisi na26,908.)




5- an karbo hadisi daga Ubad ‘dan Tamim, daga Baban sa yace; Naga Manzon Allah s.a.w.a yana Alwala saiya shafi Gemun sa da kafafuwan sa.




6- An ruwaito Hadisi daga (Imam) Ailiyu Bin Abi Talib (A.S) yace Na kasance ina ganin cewar cikin (tafin) kafa shi yafi dacewa da wajen shafawa maimakon bayan sa, harsai da naga Manzon Allah s.a.w.a yana shafa bayan su.

(Musnad na Ahmad Bin Hanbal, juzu’I na 1, Hadisi na 739 da na 919)




7- An karbo Hadisi daga Rafaa’a Bin Rafi’u cewa shi yaji Manzon Allah s.a.w.a. yana cewa “lallai Sallar dayan ku baya halatta har sai ya cika Alwalakamar yanda Allah Mai girma da daukaka yayi umurni, sannan (saiya gwada musu yanda ake alwalar) ya wanke fuskar sad a hannayen sa zuwa gwiwan hanu, kuma ya shafi kayin sa da kafafuwan sa zuwa dugadugi.

(Sunanu Ibn Maja, Juzu’I na 1,Hadisi na 460. Sunanin Nisa’I, juzu’I na2, shafi na 226)




8- Daga Ubada Bin Tamimil Mazaniy, daga Baban say ace; Naga Manzon Allah s.a.w.a yana Alwala sai yana shafa ruwa akan kafafun sa.

(Sunani Ibn Majah, Juzu’I nz 1, Hadisi na 460)




9- Daga Aws Bin Abiy Aws as-Saqafiy, cewa yaga Annabi s.a.w.a yazo ………a Ta’if sai yayi Alwala (a yayin da ya wanke fuska da hannayen sa) sai yayi shafa akan kafafuwan sa.

(Tafsirit Tabariy, Juzu’I na 6 shafi na 86/ Mu’ujamul Kabir, Juzu’I na 1 shafi 221, mai lambar hadisi na 603)




10- Daga Rafa’a ‘dan Rafi’u yace; na kasance ina zaune a wajen Manzon Allah s.a.w.a. sai wani mutum yazo ya shiga Masallaci sai yayi salla………. (har zuwa inda yake cewa) sai Manzon Allah yace lallai Sallar dayanku bata cika har sai ya cika Alwala kamar yanda Allah Yayi umurni, ya wanke fuskar sad a hannayen sa zuwa gwiwoyi, kuma ya shafi kayin sa da kafafuwan sa zuwa dugadugi……….

(wannan Hadisi za’a same shi cikin Mustadark na Hakim an-Nisaburiy, Juzu’I na 1 shafi na 241)




11- Daga ibn Abbas yace; anyi zancen SHAFA AKAN KAFAFUWA a wajen Umar da Sa’ad da Adullahi ‘dan Umar. Sai Umar ‘Dan Khaddabi yace; Sa’ad ya fika ilmi’ sai Umar yace ya Sa’ad “Ni bamu kin(musun) cewa Manzon Allah yayi shafa ,ai akan kafafuwan sa (a yayin Alwala)

(Tafsir Durrul Mansur, Jalaluddin Suyutiy, Juzu’I na 3 shafi na 29)




12- Daga Urwata ‘Dan Zubair (yace); Lallai (Mala’ika) Jibra’il a.s yayin daya sauko zuwa ga Annabi s.a.w.a. a farkon tayarwa (bashi Annabci), ya bude idaniyar ruwa da mu’ujiza, sai yayi Alwala, a yayin da Muhammadu s.a.w.a yana duba zuwa gare shi (yana kallon yanda yake Alwalar). Sai ya wanke fuskar sad a hannuwan sazuwa gwiwoyi sai ya shafi kan sa da kafafuwan sa zuwa dugadugi. Sai Annabi Muhammadu s. ya aikata(yayi Alawalan) kamar yanda yaga Jibra’il yake aikatawa.

(Khasa’isul Kubra, na Imam Suyudiy, Juzu’I na 1 shafi na 94)




13- Abdurrahman ‘Dan Jubair ‘Dan Nufair ya rawaito daga Baban sa cewa, Jubair ya gabata ga Manzon Allah s.a.w.a tare ‘yar sa wacce Manzon Allah s. ya aureta , sai Manzon Allah ya bukaci yin alwala, (a yayin Alwalar) saiya wanke hannayen sa ya tsaftace su sannan yayi kurkura bakin sa, sai yayi shakan (hanci)da ruwa. Sannan ya wanke fuskar sa da hannayen sa zuwa gwiwoyi sau uku-uku, sannan ya shafi kan sa da kafofin sa.

(Kanzul Ummal, juzu’I na 5, Shafi na 106)




14- Daga Abi Is’haq, daga Abdi Khair, daga Aliy (r.a) yace “Da addin da ra’yi ne da cikni (tafin) kafa shi yafi dacewa wajen shafawa daga bayan sa ( a yayin Alwala),saidaii naga Manzon Allah s.a.w.a yana shafa bayan su ne(saman tafin kafafuwa.

(Musannaf na Ibn Abiy Shaiba, Juzu’I nz 1 Shafi na 30)




15- Daga Sufyan yace; Naga Aliyu (r.a) yayi Alwala saiya shafi bayan su(kafafuwan sa)

(Musnad na Ahmad Bin Hanbal, Hadisi na 1018)

16- Daga Humran yace; Naga Usman (Bin Affan) ya bukaci ruwa, sai ya wanke tafukan(hannayen) sa sau uku uku, sai yayi kurkuran baki ya sheka ruwa ya wanke fuskar sa sau uku uku, sai ya shafi kan sa da bayan kafafuwan sa.

(kanzul Ummal, Juzu’I na 5 Shafi na106)




17- Daga Ikrima daga Ibn Abbas yace; Alwala dai wanki biyu ne da shafa biyu (wanke fuska da hannuwa , shafan kai da kafafuwa)

(Tafsirit Tabariy Juzzu’I na 6 shsfi na 82)




18- Daga Abdullahi al-Utkiy, daga Ikrima yace; Bawanki ake wa kafafuwa (a Alwala) ba, abinda ya sauko (daga umurnin Allah) a game dasu shine shafawa.

(Tafsirit Tabariy Juzzu’I na 6 shsfi na 82)




19- Daga Jabir (Bin Abdullahi al-Ansariy), daga Abiy Ja’far al-Baqir yace; kayi shafa akan kafan ka da kafafuwan ka.

(Tafsirit Tabariy Juzzu’I na 6 shsfi na 82)




20- Daga Ibn Ulayya Bin Daud, daga Aamir ash-Sha’biy yace; Lallai abin sani kawai SHAFA (AKAYI UMURNI DA AYI) AKAN KAFAFUWA. Shin baka gani ga’ban da ake wankewa (a Alwala) an sanya ayi shafa a kan sa, sannan ga’ban shafawa ka barsu a cikin Taimama?

(Tafsirit Tabariy Juzzu’I na 6 shsfi na 82)




21- Daga Aamir ash-Sha’biy yace; anyi umurni da a shafa a cikin Taimama inda akayi umrni da a wanke a Alwala, sai aka soke (shafan) abinda akayi umurni a shafa a cikin alwala, sune Kai da Kafafuwa.

(Tafsirit Tabariy Juzzu’I na 6 shafi




22- An karbo Yunus yace; Wanda yayi rakiya wa Ikirima zuwa Wasit ya fada min cewa “ban taba ganin sa (Ikrima) yana wanke kafafuwan sa ba (a yayin yin alwalar sa), abinda sani kawai yakan yi shafa ne a kansu har ya fita daga cikin ta (garin Wasit).
(Tafsirit Tabariy Juzzu’i na 6 shafi na 82)

Comments

Popular posts from this blog

MENENE TAMBAYOYIN DA ‘YANMATA SUKE YI??? NA 1

MENENE TAMBAYOYIN DA ‘YANMATA SUKE YI??? ماذا تسأ ل الفتيات؟ NA   - 1 DAGA “CIBIYAR NUUN” MASU WALLAFA DA TARJAMA FASSARA: MURTALA ISAH DASS MUKADDIMA A kwai tambayoyi (masu yawa) da suke kekkewayawa a cikin rai (kwakwalwar) ko wace budurwa, wadanda take bukatar amsar su, wani lokaci takan koma wajen uwarta ko 'yar'uwarta ko kawarta ko kuma wajen malamarta ta makaranta. Saidai wani lokaci bata gamsuwa da amsar da suke bata. Saboda haka sai kaga son sanin wadannan abubuwan na tunkudata zuwa ga tambayoyi masu dinbin yawa (alhali ta rasa mai bata gamsassun amsoshi) Yawancin uwaye kunya na lullubesu (suna jin kunya) game da amsa wasu sashen tambayoyi masu tsarkakiya. (Sannan wani bangare kuma ita kanta budurwar ce take jin kunyar yin tambayar alhali abin na damunta tana so ta sami bayani a kan su) Wannan littafi da ke gaba gareki ya ke 'yar'uwata abar girmamawa, tattararrun tambayoyi ne daga cikin tambayoyi wadanda ake jin kunyar ...

SHIN GASKIYA NE ‘YAN SHI’A SUNA TUHUMAR UMMUL MUMININA A’ISHA DA AIKATA ZINA?

SHIN GASKIYA NE ‘YAN SHI’A SUNA TUHUMAR UMMUL MUMININA A’ISHA DA AIKATA ZINA? Daya daga cikin abinda makiya shia suka dau tsawon zamani suke yadawa na karya akan ‘yan shia domin kyamatar da al’uma da wannan mazhaba ta ‘ya’yan gidan Manzon tsira s.a.w.a shine cewa wai suna da kudurin dora wa Matar Manzo A’isha ‘yar khalifa Abubakar tuhumar aikata zina (wal’iyazu billah). Da alama wadanda suka tsara wannan qaryar basu san cewa wata rana duniya za ta iya kasancewa tamka gari guda ba ta tayanda babu abinda zai buya ga wani. Yanzu dai ga ‘yan shia ko ina ana tare da su, ga malaman su cikin sauki za’a iya tuntuban su sannan ga dubban litattafan su a kasuwa kowa na iya saye ya karanta, uwa uba kuma ga yanar gizo wanda cikin lokaci kankani mutum zai binciki irin littafin da kake bukata ya karanta. Wani abin mamaki shine sai ga ‘yan shia basu ma yarda da wannan tuhumar akan ita Ummul muminina A’isha ba balle kuma tabbatar da tukuhumar a kan ta. Za mu duba bayanan malaman shia game da wannan a...

AUREN MUTU'A TSAKANIN MUSULMI

AUREN MUTU'A TSAKANIN MUSULMI (1) Sheikh Sale Sani Zaria Idan mutum ya bibiyi abubuwan da ake fada da rubutawa a kan Auren Mutu’a a wannan zamani daga malaman Ahlus Sunna. A dukkanin abubuwan da ake fada akwai abubuwa masu jan hankali matuka wanda ake bukatar al'umar musulmi su fahimci hakikanin sa. Alhamdu lillahi dukda cewa su malaman suna kokarin fada da wannan ibada amma anyi dace suka yarda da halaccin Mutu ’ a da ayar AlKur ’ ani ta cikin Surar Nisa ’ i aya ta 24. A kan haka ne ma nake ganin cewa duk mai hankali zai yi mamakin yadda wasu malamai suke kwatatnta auren mutu ’ a da "dadiro" ko "kwanan gida". Idan har mutum ya yarda da cewa akwai ayar AlKur ’ ani wadda ta halatta Mutu’a ko da kuwa ya yarda da cewa an goge ta daga baya, to da wace irin mahanga kuma yake kwatanta shi da dadiro da kwanan-gida? Ina ayar da ta taba halatta dadiro da kwanan-gida a AlKur ’ ani har ya cancanci irin wannan kwatanci? Dadiro fa alfasha ne! Yanzu yana jin cewa ...