Skip to main content

SHUBUHAN RIDDAN SAHABBAI DA AKE DANGANA WA 'YAN SHI'A

SHIN DA GASKE NE ‘YAN SHI’A SUNA CEWA DUKKAN SAHABBAI SUNYI RIDDA BAYAN WAFATIN ANNABI (SAWA) SAI ‘YAN KADAN?

Daya daga cikin shubuhohin da makiya shi’a shi’a suke bijirarwa don ‘yamatar da al’uma akidar itace cewa wai a akidar shi’a suna da kudurin cewa dukkan sahabbai sunyi ridda da ma’anar sun fice daga da’irar musulunci sun zamo kafirai face ‘yan kalilan wadanda basu fi a kirga ba. kuma masu wadannan tuhumar suna kafa hujja da wasu ruwayoyin shi’a wadanda suke bayyana hakan. Kuma masu wannan tuhumar kuwa mafiya rinjaye sune wahabiyawa masu bin manhajin koyarwar ibn Taimiyya masu kafirta duk wani wanda ya saba wa fahimtarsu.
Daya daga cikin matsalolin wahabiyawa shine hukunta wa wasu bangaren jama’a musulmi masu bin wata koyarwar da ta saba da fahimtar su a addini abinda su din basu yi i’itiqadi da shi ba. Sannan sukan shiga cikin litattafan da masu sabani dasu suka rubuta, kuma sukan shige ta ne da mummunan manufa domin gano maganganun da za su sami damar fidda su daga da’irar musulunci ta hanyar kafirta su ko mushrikantar da su, sakamakon abinda aka cusa musu a cikin kwakwalensu na cewa fahimtar su kawai itace musulunci, komai ibadar mutum matukar ya saba wa fahimtar su to musuluncin sa bata da kima, Kalmar shahadar sa bata amfanar dashi da komai.
Wannan irin matsayi kuwa lamari ne wanda kowa ya san hakan, sannan zancen da nake so in yi baya ni a kai na yin qazafi da danqara wa wasu mutane abinda ba su yi imani da shi ba ta wajen karanta wasu maganganu wadanda basu fahimci haqiqanin ma’anonin su ba shima wani al’amari ne da ya shahara a ayyukan malaman wahabiyawa na da da na yanzu. Maimakon su idan sun karanta su koma su tambayi ahalin abun game da abinda suke nufi, wanda mai yiwuwa ba yanda yake a zahiri haka ma’anar take ba wanda hakan shine adalci, a’a kawai saisu fassara yanda suka ga dama kuma su yi hukunci.
Misali guda da zan bayar shini labarin nan da babban Shehin dariqa Dahiru Usman Bauchi ya sha bayarwa game da muhawarar da ta faru a tsakanin sa da babban malamin su kuma wanda ya kawo wahabiyanci a Nigeria (Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi). A yayin da ya kalubalanci ‘yan dariqar Tijjaniyya game da kalma ta kafirci wanda yayi da’awar na rubuce a cikin littafin su wanda ke cewa “sufi gayatuhu huwallahu” Sai ya fassara da cewa “Sufi asalin sa shine Allah” kamar yanda yake da’awa. Alhali abinda ya dace in bai fahimci me ake nufi ba koda hakan ne sai ya tambayi ma’abutan sa su bayyana masa kafin ya hukunta su a bisha shaidar bakinsu kamar yanda na ambata. To anan Shehun Tijjaniyyar ya mbayyana masa cewa ba abinda ake nufi kenan ba. manufa itace “Sufi al’amarinsa gaba daya na Allah ne” ma’ana abinda Allah Ya yi umurni da hani shi yake dabbakawa baya ketarewa wajen aikata son sabanin abinda Allah ke so ko baya so.
Allah Madaukaki yana cewa “Kuma kada ka bi (fada ko jajircewa akan) abinda baka da ilimi dashi. Lallai ne ji da gani da zuciya, dukkan wadancan ya kasance abinda ake tamya ne” (Kur’ani: Isra’i, aya ta 36)
Kuma Yana cewa “ … ku tambayi ma’abuta sanin in kun kasance baku da sani” (Kur’ani: Nahl, aya ta 43)
To lallai wahabiya da sauran masu kiyayya da ‘yan shi’a sun rike  wannan a matsayin makamin yakar shi’anci da cusa kiyayyar mazhabar shia a zukatan mabiyan su da sauran bangarorin musulmai wadanda ba ‘yan shi’a ba, har ma da harzuka al’uma don su auka wa ‘yan shian. Suna kana karfafa wannan tuhuhumar ce da ruwayoyin da suka taho cikin litattafan hadisan shi’a wadanda suke nuna cewa bayan wafatin Manzon Allah s.a.w.a sahabbai sun yi ridda face jama’a yan kadan, kamar yanda nayi nuni a baya.
Na’am “ridda” kalma ce ta larabci wadda yake akwai ma’anar sa a lugga sannan akwaishi a is’dilahin addinin musulunci. Kalmomi suna da a isdilahohin na ma’abuta wasu bangarori na ilimi da suka kebanta da su. Kamar haka ma mazhabobin aqidu suna da isdilahohin su da suke amfani das u sabanin yanda aka sansu a al’ada. Mazhabar Ahlul bayt a.s ma wanda aka fi sani da shia suna da isdilahohin wasu kalmomi ta yanda suka saba wa isdilahohin gama-gari a musulunce a wurare kebantattu. Daya daga cikin irin wadannan kalmomi itace Kalmar “ridda”. A isdilahi na gama garin musulunci Kalmar “ridda” tana nufin ficewa daga musulunci dungurungum. Lallai shi’a ma suna amfani da wannan ma’anar, to amma bayan wannan ma’ana, suna amfani da wannan kalma da wata manufa wanda yake nufin ficewa daga biyyayyar jagorancin Ahlul baiti a.s, wanda kuma wannan riddar bata fitar da wanda ya yita daga musulunci dungurungum, saidai ace ta fitar das hi daga da’irar biyyayya wa umurnin Allah da Manzonsa wajen jibantar Ahlul baiti a matsayin jagororin addini.
Kasancewar ‘yan shi’a suna da I’itikadin cewa Manzon Allah s.a.w.a tare da umurnin Allah madaukaki ya nada Imam Ali a.s a matsayin jagoran al’uma a bayan sa w3anda ya faro tun farkon aiko shi da sako a makka har zuwa karkarewar bayyanawa ta karshe a hajjinsa na ban kwana, kuma a gaban dubban daruruwan sahabbai, kuma sahabban suka mika mubaya’a gare shi (Imam Ali), amma daga baya sai wasun su suka nada kan su ta hanyar zabe, sannan sai mafi yawan su suka mara musu baya, alhali ga wancan mubaya’a da suka yi wa Imamu Ali a.s a gaban Manzon Allah (sawa) a ghadir khum. Sakamakon haka sai Kalmar ridda ya zamo isdilahi na musamman wanda yake nufin warware wulayar Imamu Ali wanda suka yi. Amma ba ana nufin sun fita daga musulunci bane dungurungum.
Wani yana iya cewa wannan wata dabarace kawai wacce shia suka saba yi a matsayin takiyya domin boye asalin manufar su. To sai muce sam ba haka abin yake ba, kuma akwai dinbin bayanai da Imaman mu tsarkaka suka yi a cikin litattafan mu na ruwayoyi a matsayin hujjojin dake bayyana hakan karara. 
Ga kadan daga cikin hadisai da suka zo a cikin littafin “Ilalush shra’i’” na Sheikhus Saduq, Juzu’i na 1, babi na 122shafi na 149 – 150
a matsayin misali;

.... Na fada wa Abi Abdillah (Imam Ja’afar As-Sadiq) a.s, Shin me ya sanya Aliyu a.s ya kame (daga yakar) jama’ar (da suka saba masa game da khalifanci)? Sai yace, saboda tsoron kada su zamo Kafirai.

Daga Zurara yace, na fada wa Abi Abdillah a.s; Me ya hana shugaban muminai (Imam Ali) a.s bai kira mutane zuwa ga kansa ba? Sai yace,yana jin tsoron kada su yi ridda ne. (Anan yana nufin matukar ya qirasu suka yi tawaye to zai zamo sun yi riddan da yake haifar da fita daga musulunci kenan)

…… Daga  Abi Ja’afar (Imam Muhammad al Baqir) a.s yace; Lallai Aliyu a.s bai kame ba wajen kiran mutane zuwa ga kansa face zasu zamo batattu,(kasancewar) kada su bar musulunci shi ya fi soyuwa gare shi a maimakon ya kirasu su yi tawaye sakamakon haka sai su zamo kafirai.

Idan mai karatu yayi dubi da idon basira kuma ba tare da wani dogon tunani ba zai iya tsinkaya a sarari cewa wadancan hadisai da suke maganar riddar sahabbai idan sun inganta, to ba suna nuna riddar ficewa daga musulunci bane saidai riddar ficewa daga wilayar Ahlul baiti a.s ne.


Allah Ta’ala yana cewa “ Yaku wadanda suka yi imani idan fasiki ya zo muku da wani labari, to ku nemi bayani, domin kada ku cutar da wadansu mutane a cikin jahilci, sai ya zamo kun wayi gari akan abinda kuka aikata kuna masu nadama” (Kur’ani: Hujurat, aya ta 6)



.

Comments

Popular posts from this blog

MENENE TAMBAYOYIN DA ‘YANMATA SUKE YI??? NA 1

MENENE TAMBAYOYIN DA ‘YANMATA SUKE YI??? ماذا تسأ ل الفتيات؟ NA   - 1 DAGA “CIBIYAR NUUN” MASU WALLAFA DA TARJAMA FASSARA: MURTALA ISAH DASS MUKADDIMA A kwai tambayoyi (masu yawa) da suke kekkewayawa a cikin rai (kwakwalwar) ko wace budurwa, wadanda take bukatar amsar su, wani lokaci takan koma wajen uwarta ko 'yar'uwarta ko kawarta ko kuma wajen malamarta ta makaranta. Saidai wani lokaci bata gamsuwa da amsar da suke bata. Saboda haka sai kaga son sanin wadannan abubuwan na tunkudata zuwa ga tambayoyi masu dinbin yawa (alhali ta rasa mai bata gamsassun amsoshi) Yawancin uwaye kunya na lullubesu (suna jin kunya) game da amsa wasu sashen tambayoyi masu tsarkakiya. (Sannan wani bangare kuma ita kanta budurwar ce take jin kunyar yin tambayar alhali abin na damunta tana so ta sami bayani a kan su) Wannan littafi da ke gaba gareki ya ke 'yar'uwata abar girmamawa, tattararrun tambayoyi ne daga cikin tambayoyi wadanda ake jin kunyar ...

SHIN GASKIYA NE ‘YAN SHI’A SUNA TUHUMAR UMMUL MUMININA A’ISHA DA AIKATA ZINA?

SHIN GASKIYA NE ‘YAN SHI’A SUNA TUHUMAR UMMUL MUMININA A’ISHA DA AIKATA ZINA? Daya daga cikin abinda makiya shia suka dau tsawon zamani suke yadawa na karya akan ‘yan shia domin kyamatar da al’uma da wannan mazhaba ta ‘ya’yan gidan Manzon tsira s.a.w.a shine cewa wai suna da kudurin dora wa Matar Manzo A’isha ‘yar khalifa Abubakar tuhumar aikata zina (wal’iyazu billah). Da alama wadanda suka tsara wannan qaryar basu san cewa wata rana duniya za ta iya kasancewa tamka gari guda ba ta tayanda babu abinda zai buya ga wani. Yanzu dai ga ‘yan shia ko ina ana tare da su, ga malaman su cikin sauki za’a iya tuntuban su sannan ga dubban litattafan su a kasuwa kowa na iya saye ya karanta, uwa uba kuma ga yanar gizo wanda cikin lokaci kankani mutum zai binciki irin littafin da kake bukata ya karanta. Wani abin mamaki shine sai ga ‘yan shia basu ma yarda da wannan tuhumar akan ita Ummul muminina A’isha ba balle kuma tabbatar da tukuhumar a kan ta. Za mu duba bayanan malaman shia game da wannan a...

AUREN MUTU'A TSAKANIN MUSULMI

AUREN MUTU'A TSAKANIN MUSULMI (1) Sheikh Sale Sani Zaria Idan mutum ya bibiyi abubuwan da ake fada da rubutawa a kan Auren Mutu’a a wannan zamani daga malaman Ahlus Sunna. A dukkanin abubuwan da ake fada akwai abubuwa masu jan hankali matuka wanda ake bukatar al'umar musulmi su fahimci hakikanin sa. Alhamdu lillahi dukda cewa su malaman suna kokarin fada da wannan ibada amma anyi dace suka yarda da halaccin Mutu ’ a da ayar AlKur ’ ani ta cikin Surar Nisa ’ i aya ta 24. A kan haka ne ma nake ganin cewa duk mai hankali zai yi mamakin yadda wasu malamai suke kwatatnta auren mutu ’ a da "dadiro" ko "kwanan gida". Idan har mutum ya yarda da cewa akwai ayar AlKur ’ ani wadda ta halatta Mutu’a ko da kuwa ya yarda da cewa an goge ta daga baya, to da wace irin mahanga kuma yake kwatanta shi da dadiro da kwanan-gida? Ina ayar da ta taba halatta dadiro da kwanan-gida a AlKur ’ ani har ya cancanci irin wannan kwatanci? Dadiro fa alfasha ne! Yanzu yana jin cewa ...