Skip to main content

TAKLIDI A SHI'A



TAKLIDI A SHI’A

Taklidi shine yin aikin ibada da mu’amala bisa dogaro da fatawar Mujtahidi.

Mujtahidi shine mutumin da ya yi karatun addinin musulunci mai zurfi har ya kai matakin iya fidda hukunci daga mabubbugan shari’a wanda suka hada da Alkur’ani, sunna, hankali da ijma’i (dacewan malamai).




Dalilin hankali akan wajabcin yin Taklidi:

Dalilin da ya wajabta komawa zuwa ga malami a fannin aikin addini kuwa shine, ba kowani mutum bane yake da ikon yin ilimi mai zurfi har ya iya fidda hukunce hukunce a addini wadanda suka shafi ibada da mu’amala. Wadanda suka san hakan kawai sune malamai da suka yi zurfin karatu “fakihai”. Sune wadanda suke iya fahimtar zahirin kur’ani da sunnar Manzon Allah s.a.w.a da Ahlul baiti a.s.

Komawan Mukallafi zuwa ga fakihi tamkar komawan mara lafiya ne zuwa ga likita, sakamakon shi mara lafiya bai karanci yanayin cututtuka da magungunan su ba, saboda haka dole ya tafi wajen korarren likita wanda yabi matakan karatu ya karanci yanayin cututtuka da magungunan su.




Dalilin Nassi:

Allah Madaukaki ya aiko Manzonni da sakon sa domin su kira mutane zuwa ga bauta masa da kuma tsarin rayuwar da yake so su gudanar a wannan duniya. Saboda haka sai ya sanya wadannan Manzonni sune zasu fada wa al’uma yanda sakon yake su nuna musu yanda ake ibada kamar yanda Allah Yake bukata. Sakamakon haka sai ya zama wajibi akan al’uma su bi umurnin wadannan Manzonni. Iadan suka yi ibada sabanin yanda wadannan Manzonnin suka yi umurni to ibadar sub a karbabbe bane, kuma sun saba wa Allah.

Karshen wadannan Manzanni shine Annabi Muhammad s.a.w.a. saboda haka kenan mu al’umar sa dole ya zamo mun bauta wa Allah ne bisa ga koyarwar sa.

Kafin barinsa duniya sai ya zamanto bai barmu a cikin dimuwa ba, sai ya nuna mana wadanda zamu yi koyi da karban umurnin su a bayan sa, sune Khalifofi guda goma sha biyu, wanda na farko shine Imam Ali a.s, na karshen su shine Imam Mahdi a.s.

Sai ya zamo wajibi akan musulmi da su yi koyi da bin umurnin wadannan Khalifofi na Manzon Allah a bayan sa. Matukar basu aikata ibadar su da mu’amalar su bisa umurnin sub a, to aikin sub a karbabbe ba ne a wajen Allah, kuma hakan saba wa Allah ne.

Kahalifofi guda goma sha daya sun shude sai na karshen su shine Imam Mahdi a.s. to shi Imam Mahdi shine Imamin da zai yi tsawon zamani har zuwa gab da tashin kiyama, kenan mu jama’ar wannan zamani muna cikin jama’ar Imam Mahdi ne.

Allah ta’ala ya kaddara masa buya ga barin ganin gani da mu’amala kai tsaye tare dashi, har sai lokacin da Allah ya kaddari bayyanar sa a karshen zamani domin cika duniya da adalci bayan azzalumai sun cika ta da zalunci.




Imam Mahdi ya yi buya sau biyu ne, ana kiran buya na farko da “karamar buya (gaibatus sugra)”. A wannan wannan buya na farko ya ayyana wa mabiya wakilan sa mutum hudu daya bayan daya wadanda za’a karbi fatawa a wajen su, sune Usman bin Sa’id al-Asadiy, Muhammad bin Usman bin Sa’idil Amriy al-Asady, al-Husaini ibn Ruh Naubakhty al-Bagdady da Aliyu bin Muhammad as-Samariy.

Bayan wannan sai ya yi buya ta biyu wanda ake kira “babban buya (Gaibatul kubra)” wanda shine har yanzu yake ciki kafin bayyanar sa. To kafin ya shiga wanna buya sai ya yi wasici game da wadanda al’uma zasu rika su karbi addini a wajen su a lokacin buyan nasa. A wannan lokaci ne ya bayyana cewa “..... Amma wanda ya kasance daga cikin fakihai (malamai masu zurfin ilimin addini) mai kamun kansa, mai kiyaye addinin sa, mai saba wa son ran sa kuma mai bin umurni Ubangijin sa, to ya doru (wajaba) ga amawa (wadanda basu da wannan matsayi) da suyi riko da shi (wajen ayyukan su na addini).

Irin wadannan fahihai ana kiran ko wannen su “Marji’i” ko “Marji’it Taklid” (wato wanda ake komowa zuwa gare shi), sannan a wannan zamani ana musu lakabi da sunan “Ayatullahi”.

Wadannan Mujtahidai da suka cika sharuddan yi musu taklidi to wajibi ne ga mukallafi ya yayi riko da fatawar su a ayyukan sa na ibada kamar salla da abinda ya ratatayu das hi na tsarki, azumi, zakka, hajji da sauran su. Haka ma dukkan abinda ya shafi mu’amala kamar kasuwanci da makamantan su. Kuma hakan ya kunshi abubuwan da suka zama wajibi, mustahabbi da mubahi. Hakama tun daga halal, haram da makaruhi.

Idan Mukallafi ya gudanar da wani abu na ibada ko mu’amala ba tare da taklidi da Mujtahidin da ya cika sharadi ba, to aikin sa batacce ne.

Bai halatta ga Mukallafi ya ya riki wani mutum komai matsayin da yake das hi a wajen sa yana aiki da fatawar sa ba matukar ba ya da wannan zurfin karatu da ya kai ijtihadi kuma ya cika sharudda ba, yin hakan jefa kai ne cikin halaka na rashin karbuwan aikin sa a wajen Allah madaukaki da rashin hujja a gaban sa a ranar tashin kiyama. Yin hakan tamkar mutum mara lafiya ne ya kai kan sag a wanda Hakan jefa kan sa cikin halaka ne ta wajen rashin samun waraka ko kara tsananin ciwo harma yakai ga rasa ran ma gabadayan sa.

Sannan banbancin kasa ko nisa tsakanin mukallafi da Marji’in sa baya da tasiri.

Comments

Popular posts from this blog

MENENE TAMBAYOYIN DA ‘YANMATA SUKE YI??? NA 1

MENENE TAMBAYOYIN DA ‘YANMATA SUKE YI??? ماذا تسأ ل الفتيات؟ NA   - 1 DAGA “CIBIYAR NUUN” MASU WALLAFA DA TARJAMA FASSARA: MURTALA ISAH DASS MUKADDIMA A kwai tambayoyi (masu yawa) da suke kekkewayawa a cikin rai (kwakwalwar) ko wace budurwa, wadanda take bukatar amsar su, wani lokaci takan koma wajen uwarta ko 'yar'uwarta ko kawarta ko kuma wajen malamarta ta makaranta. Saidai wani lokaci bata gamsuwa da amsar da suke bata. Saboda haka sai kaga son sanin wadannan abubuwan na tunkudata zuwa ga tambayoyi masu dinbin yawa (alhali ta rasa mai bata gamsassun amsoshi) Yawancin uwaye kunya na lullubesu (suna jin kunya) game da amsa wasu sashen tambayoyi masu tsarkakiya. (Sannan wani bangare kuma ita kanta budurwar ce take jin kunyar yin tambayar alhali abin na damunta tana so ta sami bayani a kan su) Wannan littafi da ke gaba gareki ya ke 'yar'uwata abar girmamawa, tattararrun tambayoyi ne daga cikin tambayoyi wadanda ake jin kunyar ...

SHIN GASKIYA NE ‘YAN SHI’A SUNA TUHUMAR UMMUL MUMININA A’ISHA DA AIKATA ZINA?

SHIN GASKIYA NE ‘YAN SHI’A SUNA TUHUMAR UMMUL MUMININA A’ISHA DA AIKATA ZINA? Daya daga cikin abinda makiya shia suka dau tsawon zamani suke yadawa na karya akan ‘yan shia domin kyamatar da al’uma da wannan mazhaba ta ‘ya’yan gidan Manzon tsira s.a.w.a shine cewa wai suna da kudurin dora wa Matar Manzo A’isha ‘yar khalifa Abubakar tuhumar aikata zina (wal’iyazu billah). Da alama wadanda suka tsara wannan qaryar basu san cewa wata rana duniya za ta iya kasancewa tamka gari guda ba ta tayanda babu abinda zai buya ga wani. Yanzu dai ga ‘yan shia ko ina ana tare da su, ga malaman su cikin sauki za’a iya tuntuban su sannan ga dubban litattafan su a kasuwa kowa na iya saye ya karanta, uwa uba kuma ga yanar gizo wanda cikin lokaci kankani mutum zai binciki irin littafin da kake bukata ya karanta. Wani abin mamaki shine sai ga ‘yan shia basu ma yarda da wannan tuhumar akan ita Ummul muminina A’isha ba balle kuma tabbatar da tukuhumar a kan ta. Za mu duba bayanan malaman shia game da wannan a...

AUREN MUTU'A TSAKANIN MUSULMI

AUREN MUTU'A TSAKANIN MUSULMI (1) Sheikh Sale Sani Zaria Idan mutum ya bibiyi abubuwan da ake fada da rubutawa a kan Auren Mutu’a a wannan zamani daga malaman Ahlus Sunna. A dukkanin abubuwan da ake fada akwai abubuwa masu jan hankali matuka wanda ake bukatar al'umar musulmi su fahimci hakikanin sa. Alhamdu lillahi dukda cewa su malaman suna kokarin fada da wannan ibada amma anyi dace suka yarda da halaccin Mutu ’ a da ayar AlKur ’ ani ta cikin Surar Nisa ’ i aya ta 24. A kan haka ne ma nake ganin cewa duk mai hankali zai yi mamakin yadda wasu malamai suke kwatatnta auren mutu ’ a da "dadiro" ko "kwanan gida". Idan har mutum ya yarda da cewa akwai ayar AlKur ’ ani wadda ta halatta Mutu’a ko da kuwa ya yarda da cewa an goge ta daga baya, to da wace irin mahanga kuma yake kwatanta shi da dadiro da kwanan-gida? Ina ayar da ta taba halatta dadiro da kwanan-gida a AlKur ’ ani har ya cancanci irin wannan kwatanci? Dadiro fa alfasha ne! Yanzu yana jin cewa ...