Skip to main content

Posts

Showing posts from April, 2017

SHIN GASKIYA NE ‘YAN SHI’A SUNA TUHUMAR UMMUL MUMININA A’ISHA DA AIKATA ZINA?

SHIN GASKIYA NE ‘YAN SHI’A SUNA TUHUMAR UMMUL MUMININA A’ISHA DA AIKATA ZINA? Daya daga cikin abinda makiya shia suka dau tsawon zamani suke yadawa na karya akan ‘yan shia domin kyamatar da al’uma da wannan mazhaba ta ‘ya’yan gidan Manzon tsira s.a.w.a shine cewa wai suna da kudurin dora wa Matar Manzo A’isha ‘yar khalifa Abubakar tuhumar aikata zina (wal’iyazu billah). Da alama wadanda suka tsara wannan qaryar basu san cewa wata rana duniya za ta iya kasancewa tamka gari guda ba ta tayanda babu abinda zai buya ga wani. Yanzu dai ga ‘yan shia ko ina ana tare da su, ga malaman su cikin sauki za’a iya tuntuban su sannan ga dubban litattafan su a kasuwa kowa na iya saye ya karanta, uwa uba kuma ga yanar gizo wanda cikin lokaci kankani mutum zai binciki irin littafin da kake bukata ya karanta. Wani abin mamaki shine sai ga ‘yan shia basu ma yarda da wannan tuhumar akan ita Ummul muminina A’isha ba balle kuma tabbatar da tukuhumar a kan ta. Za mu duba bayanan malaman shia game da wannan a...

SHUBUHAN RIDDAN SAHABBAI DA AKE DANGANA WA 'YAN SHI'A

SHIN DA GASKE NE ‘YAN SHI’A SUNA CEWA DUKKAN SAHABBAI SUNYI RIDDA BAYAN WAFATIN ANNABI (SAWA) SAI ‘YAN KADAN? Daya daga cikin shubuhohin da makiya shi’a shi’a suke bijirarwa don ‘yamatar da al’uma akidar itace cewa wai a akidar shi’a suna da kudurin cewa dukkan sahabbai sunyi ridda da ma’anar sun fice daga da’irar musulunci sun zamo kafirai face ‘yan kalilan wadanda basu fi a kirga ba. kuma masu wadannan tuhumar suna kafa hujja da wasu ruwayoyin shi’a wadanda suke bayyana hakan. Kuma masu wannan tuhumar kuwa mafiya rinjaye sune wahabiyawa masu bin manhajin koyarwar ibn Taimiyya masu kafirta duk wani wanda ya saba wa fahimtarsu. Daya daga cikin matsalolin wahabiyawa shine hukunta wa wasu bangaren jama’a musulmi masu bin wata koyarwar da ta saba da fahimtar su a addini abinda su din basu yi i’itiqadi da shi ba. Sannan sukan shiga cikin litattafan da masu sabani dasu suka rubuta, kuma sukan shige ta ne da mummunan manufa domin gano maganganun da za su sami damar fidda su daga da’irar m...

ME YASA YANSHIA SUKE SHAFAN KAFA A ALWALA BA WANKEWA BA?

ME YASA YANSHIA SUKE SHAFAN KAFA A ALWALA BA WANKEWA BA? Addinin Musulunci addinin ne na mika wuya ga Allah Madaukakin sarki. Shi Allah Ya halicci dandam da Aljani ne domin su bauta masa, bai yarda da bautan wanin saba in ba shi kadai ba. Wannan bauta kuma bai yarda mutum ya yi shi yanda yaga dama ba, sai ya aiko Manzannin sa ya saukar musu da littafi mai dauke da yanda yake so su gudanar da bautan. Saboda haka aiki zai zamo karbabbe ne a waje Allah kawai idan ya dace da yanda yayi umurni ayi. Manzo na qarshe da Allah ya aiko shine Annabi Muhammadu (sawa) tare da littafi Alqurani mai girma, ta yanda ya umurci wannan aluma da aikin ibadu naui dabam-dabam ciki kuwa har da Sallah, kuma ya zamo shine mafi girman a cikin su. Kuma shi Manzon ya koyar da wadannan ibadu a aikace a fili kuma filla-filla. To saidai wannan addini na Musulunci ya gamu da ibtilai a inda bayan rasuwar Manzo s.a.w.a aka sami sabani dangane da alamura masu yawa, sakamakon jarrabar addinin da akayi da wasu gurba...

TAKLIDI A SHI'A

TAKLIDI A SHI’A Taklidi shine yin aikin ibada da mu’amala bisa dogaro da fatawar Mujtahidi. Mujtahidi shine mutumin da ya yi karatun addinin musulunci mai zurfi har ya kai matakin iya fidda hukunci daga mabubbugan shari’a wanda suka hada da Alkur’ani, sunna, hankali da ijma’i (dacewan malamai). Dalilin hankali akan wajabcin yin Taklidi: Dalilin da ya wajabta komawa zuwa ga malami a fannin aikin addini kuwa shine, ba kowani mutum bane yake da ikon yin ilimi mai zurfi har ya iya fidda hukunce hukunce a addini wadanda suka shafi ibada da mu’amala. Wadanda suka san hakan kawai sune malamai da suka yi zurfin karatu “fakihai”. Sune wadanda suke iya fahimtar zahirin kur’ani da sunnar Manzon Allah s.a.w.a da Ahlul baiti a.s. Komawan Mukallafi zuwa ga fakihi tamkar komawan mara lafiya ne zuwa ga likita, sakamakon shi mara lafiya bai karanci yanayin cututtuka da magungunan su ba, saboda haka dole ya tafi wajen korarren likita wanda yabi matakan karatu ya karanci yanayin cututtuka da magungunan s...

ME YA SA 'YAN SHI'A SUKE SUJADA AKAN TURBA?

“Turba” kalma ce ta larabci wanda yake nufin “K’asa”. ‘yan shia suna salla a kan kasa ne saboda abinda yazo a fikhu na wajabcin yin sujada a kan kasan, da rashin ingancin yin sujada a kan wani abunda ba kasan ba saidai in shima dangin kasan ne kamar dutse da makamancin sa, ko kuma abinda ya fito daga kasan na tsirrai, saidai bai hallata ba a yi akan sa sune abinda yake abinci ne ko tufafi. yin sujada akan koma bayan wadannan abubuwan da aka sharadanta yana sanya rashin ingancin salla wanda yake shine ibada mai daraja ta daya a muhimmanci. Da wannan ne yasa ‘yan shia domin saukakawa suke kwaba laka su busar da shi suna yin sujadan a kan sa. Wannan shi ya haifar da za ka taras ‘yan shia suna daukan wannan turba a tare das u domin idan salla ya same su sais u sanya domin yin sujada a kan sa musamman idan wajen sallar ko masallacin a shimfide yake da shinfidu na zamani, haka ma shi ya sanya in ka shiga masallatan ‘yan shia zaka tarar da wadannan dunkulallun kasa wanda ake kira turba d...

AUREN MUTU'A TSAKANIN MUSULMI

AUREN MUTU'A TSAKANIN MUSULMI (1) Sheikh Sale Sani Zaria Idan mutum ya bibiyi abubuwan da ake fada da rubutawa a kan Auren Mutu’a a wannan zamani daga malaman Ahlus Sunna. A dukkanin abubuwan da ake fada akwai abubuwa masu jan hankali matuka wanda ake bukatar al'umar musulmi su fahimci hakikanin sa. Alhamdu lillahi dukda cewa su malaman suna kokarin fada da wannan ibada amma anyi dace suka yarda da halaccin Mutu ’ a da ayar AlKur ’ ani ta cikin Surar Nisa ’ i aya ta 24. A kan haka ne ma nake ganin cewa duk mai hankali zai yi mamakin yadda wasu malamai suke kwatatnta auren mutu ’ a da "dadiro" ko "kwanan gida". Idan har mutum ya yarda da cewa akwai ayar AlKur ’ ani wadda ta halatta Mutu’a ko da kuwa ya yarda da cewa an goge ta daga baya, to da wace irin mahanga kuma yake kwatanta shi da dadiro da kwanan-gida? Ina ayar da ta taba halatta dadiro da kwanan-gida a AlKur ’ ani har ya cancanci irin wannan kwatanci? Dadiro fa alfasha ne! Yanzu yana jin cewa ...